Daga USMAN KAROFI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya bayyana alhinin sa kan rasuwar tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yana mai cewa marigayin mutum ne mai kishin ƙasa da sadaukarwa ga jin daɗin al’umma.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Shekarau yace labarin rasuwar Buhari ya girgiza shi amma ya miƙa wuya ga ƙaddarar Allah.
Buhari, wanda ya rasu yana da shekaru 82 a wani asibiti da ke birnin Landan a ranar Lahadi 13 ga Yuli 2025, bayan fama da doguwar jinya, an yi jana’izarsa a Daura, jihar Katsina ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Shekarau ya bayyana cewa dangantakar sa da Buhari ta fara ne tun lokacin da ya shiga siyasa a shekarar 2002, yana mai cewa Buhari ya kasance mai jajircewa da kishin al’umma a kowane lokaci.
A cewarsa, Buhari ya kasance mutum mai gaskiya, riƙon amana, da rayuwa mai sauƙi, wanda hakan ya ba da gudunmawa mai muhimmanci wajen gina siyasar Najeriya. “A duk lokacin da muka tattauna, buƙatun ‘yan ƙasa su ne kan gaba a zuciyarsa, ba wani abu na ƙashin kansa ba,” in ji Shekarau. Ya ƙara da cewa Buhari bai taɓa barin kowane matsayi ko girma ya hana shi nuna adalci da kishin ƙasa ba.
Sanata Shekarau ya kammala da addu’a ga marigayin shugaban ƙasa, yana roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa, ya kuma ba shi Aljannah Firdausi.
Ya ce Najeriya gaba ɗaya ta yi babban rashi na gwarzon da ya rayu cikin ɗa’a da ladabi, kuma ya bar tarihi mai kyau a rayuwar jama’a.
