Duk takalmin da aka kawo zan iya yin irinsa har ma a kasa gane bambanci – Kadeeja Ahmad

Spread the love

“Na yi ƙwarewar da zan iya gane ingancin takalma kowanne iri ne”

Daga AISHA ASAS

A yau shafin Mata A Yau ya ɗauko wa masu karatu matashiyar da ta zama allon kwaikwayo ga kowacce mace da ta san ciwon kanta, babba ko ƙarama, domin ta ce wa matasan mata idan ba ku yi, to, ku ba ni wuri, kuma ta tabbatar wa mata cewa, ba sana’ar da mace ba zata iya yi ba ko ta fi ƙarfinta, domin ta ɗauko ɗaya daga cikin sana’o’in da suka yi tambari da sunan jinsin maza, wato sana’ar ƙera takalma, inda ta koya, ta iya, ta kuma ƙware har a yanzu ta ke cin gajiyar abin fiye da tsamani, domin a yanzu ta kai da sunan takalman nata na ‘KAD Shoes’ sun yi suna, mutane sun san da zaman su. A tattaunarwar ta da Manhaja, za ku ji yadda matashiyar ta taso da son kasuwanci kuma ba tare da ta bari ya taɓa harkar neman iliminta ba. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Kadeeja Ahmad:

MAHNAJA: Wacce ce baƙuwar tamu?

KADEEJA: Sunana Kaddeja Ahmad. Haifafiyyar Jihar Katsina, sai dai na tashi anan Birnin Tarayya, wato Abuja. Na kammala karatuna a ɓangaren aikin jarida. Ina da shekaru 26 da haihuwa.

Yanzu me aka sa a gaba, aiki ne ko sana’a?

Sana’a dai zan ce, domin tun kan ma na kammala karatu nake sana’a, shekara ta 2015, don haka ita na sa a gaba har zuwa yanzu.

Ko za mu iya sanin sana’ar taki?

To, na yi sana’oi da dama abaya, sai dai a yanzu dai sana’ar takalma ce sana’ata.

Ita wannan san’a da ki ka ce kina yi ta takalma. Za mu so jin shin kina siyo takalma ne kina siyarwa ko ya abin yake?

Mu muke ƙera takalman da kanmu, muna siyo kayan aikin ne, mu sarrafa su zuwa duk wani nau’in takalma da ake buƙata. Wani lokacin mukan yi takalman iri daban-daban, za a zo a siya irin wanda kaga ya yi ma, wani lokacin kuwa kai za ka kawo irin wanda kaga an yi, ma’ana takalman da aka riga aka haɗa, sai mu yi ma irinsa, ko ta hanyar kawo takalman ko ta hanyar turo hoto, kuma Allah cikin ikonSa, idan muka yi, zai fito tamkar wanda ka kawo, kuma zuwa yanzu babu irin takalman da ba ma iya irinsa.

Shin kin koyi wannan sana’a ta yin takalma ne ko gadarta ki ka yi?

Na koya ne har na iya, kuma Ina yi har na zama gwana, amma a yanzu da na yi ƙarfi sosai, Ina da yara, ma’ana waɗanda ke aiki a ƙarƙashina, kuma su ma sun iya sosai, don haka duk aikin da muke yi su suke yin sa, sai dai Ina sa ido sosai, duk inda naga abin gyarawa zan faɗi yadda za a gyara, kamar ta ɓangaren su kansu kayan aikin, an sa wani abu da bai dace da takalman ba. Na yi ƙwarewar da ko manyan takalma irin na ƙasar waje na gani, zan iya gane da me aka yi su, kuma zan iya ganewa idan an yi shi ne marar inganci ko mai inganci.

Ita wannan harka ta yin takalma ya ake koyonta, shin ita ma kamar irin yadda ake zuwa koyon ɗinki ce da makamantan su?

Amsar zai iya zama eh, kuma zai iya zama a’a, inda ya zama ɗaya shine, dukkansu abu ne da za ka yi sha’awa ka nemi masu yin sa, ko waɗanda suka ƙware su koya ma, wani ɓangare kuwa kowanne daga cikinsu duniyarsu daban ce, domin ko daga duba ga yanayin bambancin da ke tare da ababen biyu, ɗinki da kuma takalma. A ɓangare na, na koyi wannan sana’a ne a wurin wasu ‘yan’uwana da su ma sana’ar da suke yi kenan, a cikisu na ɗauko ɗaya, ya zo yana koya min har na iya.

Bari na ɗan koma baya kaɗan. Kince kin fara wannan sana’a ta yin takalma a shekara ta 2015, a lokacin da ki ke shekara ta biyu a jami’a. Wani lokaci akan samu matsala ta hana yara tauna taura biyu a lokaci ɗaya, musamman ma ga mata, wasu iyayen za su iya hana wa a ƙoƙarin ganin ‘ya’yansu ba su yi wasa da karatunsu ta hanyar ba wa sana’a wani muhimmancin da zai rinjaye na karatu. Ko kin fuskanci wannan matsala?

Wannan haka ne, akan samu iyaye da ke da wannan tunanin, sai dai a ɓangarena ban fuskanci wannan matsala ba. A lokacin da na zan fara, da na sanar da mahaifiyata ta ba ni goyon baya sosai, duk da cewa, idan ki ka lura a lokacin da na fara ba kasafai ki ke samun mata a irin wannan sana’a ba, yawancin duk inda ake harka ta ƙera takalma a Arewacin Nijeriya za ki tarar maza ne ke yi, kuma ni a ɓangarena na zaɓi saka wa takalman da na yi suna da na zaɓa, saɓanin mafi yawa daga waɗanda ke yin takalma suna amfani da sunan ƙasashen waje, ko kamfanonin takalma. Duk da tambarin da sana’ar ta yi da sunan maza bai sa mahaifiyata ta ƙi ƙarfafa min gwiwa ba, asalima ita ce ta zaɓa min wanda zai koya min daga cikin ‘yan’uwan namu. A taƙaice dai iyayena sun ba ni goyon baya fiye da tunanin mai karatu, kuma ban samu wata matsala a ɓangaren karatu ba, saboda kowanne daga ciki na ba shi nashi lokacin da bai shiga cikin na wani.

Kasancewar sana’ar ta fi suna a wurin maza. Shin kin samu matsala daga masu siya ta hanyar rena abinda ki ke yi a matsayinki ta mace?

(Dariya) Gaskiya ban fuskanci irin wannan matsala ba, asali ma, a lokacin da na fara mutane da dama sun yaba min kan ɗaukar wannan sana’a a matsayina ta mace, sun ji daɗi na matsayina ta ‘yar Arewa, Ina wannan sana’a, wanda hakan ya taimaka wurin samun masu siyan takalman. Saidai hakan ba yana nufin ban fuskanci ‘yan matsaloli ba.

Matsala ta farko ita ce, lokacin da na yi zancen Ina son duk wani takalma da zan yi ya fito da sunan da zai nuna ni na yi shi, sai aka ce min ba damar yin hakan ta ɓangaren kasuwancinsa kenan, sai dai a dinga sa sunayen kamfanonin na ƙasar waje da suka yi suna a harkar ko suka yi ainahin takalman da muka kwaikwaya. Ni kuma na ce, a’a, Ina so a sa nawa sunan, to anan mutane da yawa sun ɗan sanyaya min gwiwa, sai dai hakan bai sa na haƙura ba, na shiga nema har na samu waɗanda suke buga sunan, ni ma sai aka sa min sunana da nake amfani da shi. Matsala ta biyu kuma da zan ce na fuskata ko ma nake fuskata ita ce, wahalar samun wasu daga cikin kayan aiki, kamar idan an bamu yin takalma babba wanda ƙwararun kamfanoni ke yi masu tsada, to wurin samun kayan yin su gaskiya muna shan wahala kafin mu samu, wani lokacin ma sai dai mu samu na kusa da su, waɗanda za su fita kamar su. To, wannan matsala wani lokacin kan sa mai siya yaga an masa ba daidai ba, saboda zai iya ganin kamar ba a yi masa yadda yake son takalman su kansance ba.

Da kamar nawa ki ka fara wannan sana’a ta takalma?

Da 50,000 na fara, kuma babana ne ya bani su.

To ya yanayin cigaban da aka samu daga amfani da dubu hamsin ɗin zuwa yanzu?

Gaskiya na samu cigaba sosai fiye ma da yadda ake tunani, don ba za ma ayi maganar 50,000, irin cigaban da na samu ma yanzu haka Ina shirin buɗe babban kamfani na yin takalma, kinga kuwa ko kusa 50,000 bata zo kusa ba.

Wasu mata na fuskantar danniya ta ɓangaren sana’a, wato za ki ga wasu na ƙorafin mazajensu sun hanasu yin sana’a. shin a naki gani hakan na da illa ga rayuwar macen da ta samu kanta a irin wannan?

Gaskiya wannan ba daidai ba ne, saboda rayuwar mace na buƙatar abin yi da zai kawo mata wani abu da zata kira mallakinta. A ganina hana mace sana’a ba mafita ba ce ga duk wani abu da su mazan ke tunani ko hange, saboda mace mai sana’a na da amfani ta ɓangarori da dama har ma ga shi karan kansa mijin nata, domin idan ta iya ɗaukar ɗawainiyar kanta ma kawai ai ta taimaka masa.

Mun gode.

Ni ma na gode sosai. 

By ukarofi