Gwamna Raɗɗa ya ziyarci Bakori domin yin ta’aziyya ga iyalan tsohon shugaban ƙaramar hukumar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai magana da yawun gwamnan Jihar Katsina Muhammad Kaula ya faɗi haka.

Da yake miƙa sakon ta’aziya ga iyalin mamacin,gwamnan ya tunatar da kowa cewa mutuwa na kan kowa.

Gwamnan ya ce wasu na iya yin murna ko baƙin ciki da rasuwar wasu, amma a ƙarshe dukkan mu zamu koma ga mahaliccin mu.

Malam Dikko Raɗɗa ya kuma jaddada muhimmancin yin rayuwa da aminci.

“Abu ne mai kyau mu rinƙa tafiyar da harkokin bisa gaskiya da adalci,”gwamnan ya ce.

Gwamnan ya bayyana marigayi Alhaji Ɗan Hamidu, a matsayin shugaba mai gaskiya da riƙon amana kuma mai kishin ƙasa,wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen ƙoƙarinsa na kawo sauyi a mulkin ƙaramar hukumar Bakori.

A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Katsina,gwamnan ya miƙa ta’aziyar ga iyalai da al’ummar ƙaramar hukumar Bakori bisa wannan rashi da akayi.

By ukarofi