Gwamnatin Zamfara ta fara rabon rigakafin zazzaɓin cizon sauro

Spread the love


Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara tare da haɗin gwiwar shirin kawar da cutar zazzaɓin cizon sauro na ƙasa (NMEP), da hukumar samar da lafiya ta duniya (GHSC-PSM) tare da tallafin kuɗaɗe daga shirin shugaban ƙasar Amurka na yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro na shekarar 2025, sun fara rabon maganin rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro na shekarar 2025 ga yara ‘yan ƙasa da shekaru 14 na ƙananan hukumomin jihar.

Kwamishiniyar lafiya ta jihar Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta bayyana hakan a wani taron yaɗa labarai na kamfen dangane da rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro na zamani (SMC) na shekarar 2025, wanda aka gudanar a ma’aikatar a Gusau yau Litinin.

“Sama da magunguna miliyan ɗaya na SMC za a raba wa yara ‘yan watanni uku zuwa watanni 59 a Zamfara ta hanyar bi gida-gida”. Dr. Nafisa tace

Kwamishinan wanda ta samu wakilcin daraktan kiwon lafiyar jama’a Dokta Yusuf Abubakar Haske ya ce babban manufar wannan gangamin na SMC shi ne a tabbatar da cewa duk yaran da suka cancanta ‘yan ƙasa da watanni uku zuwa watanni 59 da kuma mata masu juna biyu sun samu magungunan rigakafin zazzaɓin cizon sauro a daidai lokacin da ake fama da zazzaɓin cizon sauro don kare su daga kamuwa da cutar zazzaɓin cizon sauro.

A cewarta, don tabbatar da rigakafin, ana ba da SMC kowane wata sama da watanni huɗu a lokacin damina inda cutar zazzaɓin cizon sauro ta fi yawa.

Ta ce za a fara zagaye na farko na yaƙin ne daga ranar 3 ga watan Yuli zuwa 7 ga watan Yulin 2025. Ta kuma bayyana cewa masu rarraba magunguna na al’umma za su ziyarci kowane gida don ba da magungunan SMC ga yaran da suka cancanta.

Ta buƙaci iyalai da su tabbatar sun bar wani a gida a cikin wannan lokacin don baiwa ‘ya’yansu damar samun alluran a lokacin rabon magungunan.

“Manufar ita ce rage cututtuka masu nasaba da zazzaɓin cizon sauro da kuma mace-macen yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar”.

Ta bayyana cewa ma’aikatar ta da haɗin gwiwa da hukumar kula da lafiya matakin farko ta jiha za ta haɗa dukkan masu ruwa da tsaki domin samar da tsarin aiki da zaɓar ma’aikatan SMC domin samun nasarar yin rigakafin a jihar.

Ta kuma ƙara da cewa darasin da gwamnatin jihar ta koya kan yaƙi da zazzaɓin cizon sauro SMC a shekarar da ta gabata, shine rashin aiki da jami’an tsaro da Sarakunan gargajiya da malaman addini.

“Akwai buƙatar inganta bayar da shawarwari ga hukumomin tsaro da masu riƙe da sarautun gargajiya a matsayin ginshiƙin aiwatarwa cikin kwanciyar hankali a ƙananan hukumomin da ke fama da rikici”.

A bana ma’aikatar lafiya ta Jihar Zamfara ke jagorantar shirin na SMC ta hanyar shirin kawar da cutar zazzabin cizon sauro a jiha tare da taimakawar hukumar GHSC-PSM”.

Dakta Nafisa ta ci gaba da cewa yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro ya ragu zuwa mafi ƙaranci, inda ta yi nuni da cewa yawan cutar a bara ya kai kashi 72 cikin 100 yayin da bana ya ragu zuwa kashi 65 cikin 100.

Kwamishiniyar ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta ƙuduri aniyar kawar da cutar zazzaɓin cizon sauro nan da ƙarshen wannan shekarar a jihar ta Zamfara.

By ukarofi