
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Iran ta ce ta kai hare-haren makamai masu linzami a sansanin sojojin Amurka, lamarin da ƙasar ta kira da martani mafi girma da nasara kan hare-haren Amurka a cikin ƙasar.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar na Tasnim ya ce, dakarun juyin juya halin ƙasar sun ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka dake Ƙatar da Iraƙi
A sa’o’in da suka gabata ne aka samu labaran jin ƙarar abubuwan fashewar a Ƙatar.
Saidai a yayin tsokaci game da hakan, Amurka ta ce adadin makamai masu linzami da ta yi amfani da su wajen kai wa Iran hari a ma’ajiyar nukiliyarta sun yi daidai da wanda Iran ɗin ta jefa wa sansanin sojojin nata.
Haka kuma hukumomin Ƙatar sun ce, sun yi nasarar daƙile harin makami mai linzami da Iran ta harba mata a sansanin sojin Amurkan.
