“Yin amfani da tsumma lokacin al’ada na iya haifarwa mace matsala”
Daga UMAR AKILU MAJERI
Hajiya Balaraba Abdullahi ita ce Shugabar ƙungiyar Ayman Care ta Jihar Jigawa kuna Shugabar ƙungiyar mata manoma, wato Women in Agric Bussine reshen Jihar Jigawa ta tofa albarkacin bakinta akan yadda kiwon shanu da raguna ke kawo wa mata kuɗi.
Hajiya Balaraba ta faɗi kaɗan daga cikin alfanon kiwo da yadda idan mata za su yi za su anfana kuma kiwon zai taimaka wajan magance zaman banza a tsakanin al’umma .
Wakilinmu na Jihar Jigawa Umar Akilu Majeri ya samu zantawa da Hajiya Balaraba akan irin alfanon kiwo da noma musamman a wajan mata.
Ga dai yadda hirar tasu ta gudana;
MANHAJA: Mu fara da jin wacce ce Hajiya Balaraba?
HAJIYA BALARABA: Da farko dai sunana Hajiya Balaraba Abdullahi, ni ce shugabar ƙungiyar mata manoma ta Arewacin Nijeriya reshen Jihar Jigawa, wato Women in Agric Business, baya ga haka, na kasance shugabar gidauniyar Ayman Care Foundation ta Jihar Jigawa.
Ita ma wata ƙungiya ce da na kafata domin taimaka wa mata da ƙananan yara da kuma tsofaffi marasa galihu.
Ita wannan ƙungiyar na kafata ne da nufin taimakon jama’a, musamman a lokacin azumi, muna taimaka wa marasa lafiya da ke kwance a asibiti da kuma lokutan bukukuwan sallah saboda a wannan lokacin ba a samun abincin sayarwa hakan yana jefa rayuwar marasa ƙarfi da marasa lafiya cikin wani hali.
Hakan ya sa ƙungiyata ta ɗauki aniyar dafa abinci ta raba kyauta ga marasa lafiya da ke kwance a asibitoci, gado-gado, suna zaman jinya a asibitin.
Wannan irin taimako kike bayarwa bayan raba abinci?
Bayan abinci muna raba kayan sallah da kayan sawa ga tsofaffi da kayan makaranta ga ɗaliban firamare.
Me ya sa kika ƙirƙiri wannan ƙungiyar?
Na ƙirƙiri wannan ƙungiyar ne da nufin tallafa wa jama’a.
Kamar mutun nawa kika tallafa wa a ƙugiyarki?
Ni bazan iya sanin yawan waɗanda na tallafa wa ba, amma dai na san Ina taimaka wa yara da kayan makaranta, kayan karatu da kuma taimaka wa tsofaffi da kayan abinci da kayan sawa, baya ga haka, ƙungiyarmu muna bai wa marasa ƙarfi tallafin kayan abinci.
Matsalar tsaro ta yi katutu a Aarewacin Nijeriya. Shin wacce gudunmawa ƙungiyarki ta bayar wajan taimaka wa waɗanda suke fuskantar rashin tsaro.
Dayake mu a Jihar Jigawa mu na zaune lafiya,bmagana ta gaskiya ban taɓa bada tallafin komai ba, amma a lokacin da Jihar Borno suka samu matsalar ambaliyar ruwa na yi iyakacin bakin ƙoƙarina na bada gudunmawa ga waɗanda suka samu matsalar ambaliyar ruwa a yankin Borno, amma lokacin ya ƙure ban samu damar zuwa na kai gudunmawar ba saboda ban samu dama ba.
Ko gwamnati tana ba ki gudunmawa domin tafiyar da harkokinki na gidauniya?
Gwamnati ba ta taɓa bani gudunmawa ba, saidai abokan arziki waɗanda muke tare da su, da ‘yan uwana ne suke taimaka min wajan cigaban harkokin kungiyar. Amma yanzu ni kaɗai nake ƙoƙarin na kai ga samun nasara. Ina iyakacin ƙoƙarina a yanzu na ga, gwamnati ta shigo ta taimakamin domin duk wata ƙungiya da take son ta cigaba dole sai ta haɗa kai da gwamnati.
Ko akwai abinda kuke yi a ƙungiyance wadda zaisa gwamnati ta ba ku haɗin kai ta taimaka wa ƙungiyarki?
A yanzu haka ƙungiyata tana faɗakar da mata yadda za su kula da tsaftar jikinsu yayin jinin al’ada da kuma bayan sun kammala jinin al’ada. Mun ɗauki matakin haka ne domin kare mata daga kamu wa da cututtuka da suke kama mara da mahaifa su haifar da ciwon sanyi ga mata lamarin da yake haifar da matsala tsakanin ma’aurata musamman a wasu yankuna na karkara saboda matsalar ƙarancin ilimi da rashin sanin mahimmancin zuwa asibiti.
Haka zalika muna faɗakar da su yadda za su bai wa kansu kulawa wajan yadda zasu kare kansu daga kamuwa da ƙananan cututtuka ta hanyar nusar da su mahimmancin yin amfani da auduga maimakon yin amfani da tsumma da suke yin ƙunzugi da shi.
Kuma sau da yawa na lura rashin zuwan mata asibiti da yin amfani da magangunan garganiya da kuma amfani da tsumna a yi ƙunzugu yana taimaka wa wajan yaɗuwar cututtuka ƙanana da manya a tsakanin mata, musamman matan karkara.
Muna faɗakar da mata akan yadda za su bada gudunmawa wajan hana yaduwar fyaɗe a tsakanin al’umma musamman ganin an daƙile yaɗuwar fyaɗe a faɗin jihar.
Mun ɗauki matakin haka ne da nufin taimaka wa mata musamman yara ƙanana danganin mun magance yaɗuwar fyaɗe a tsakanin al’umma.
Me ya sa kike son gwamnati ta shigo ta taimaka miki a ƙungiyarki?
Gaskiya na gaza wajan cimma burina domin na fuskanci duk wata ƙungiya ba ta ci gaba sai gwamnati ta tallafa mata matuƙar ana son ƙungiyar ta ci gaba.
Ina da buƙatar taimakon gwamnati aƙallah domin in samu damar buɗe ofishina kuma na sayi kayan aiki, kuma idan so samu ne a ce gwamnati ta ba ni kamar miliyan 100 zai taimaka min wajan inganta ƙungiyata, kuma ko miliyan 200 gwamnati ta ba ni wallahi zan iya halakar da ita wajan tallafaɓwa al’umma ta.
Bari mu koma ɓangaren noma, da yake kina cikin ƙungiyar mata manoma. Yaya za abyi a taimaki mata su zama masu dogaro da kansu?
Gwamnati ce zata fito da kuɗi da tsare-tsare da mata za su amfana ta fuskar noma ko kiwo duk matar da aka ba ta jarin miliyan goma ta sayi raguna ta baibwa matan, bayan shekaru biyu su biya za su iya dogaro da kansu.
A ɓangaren ki, ko kina yin noma ko kiwon ne?
Ni ina yin kiwo da noma domin a duk shekara ina yin kiwon raguna da shanu kuma Ina amfana, amma ribar kiwo shi ne a saya a baka kuɗin a dunƙule, rashin samun haka zai sa mai kiwon ya faɗi, faɗuwar da in ya karye ba zai ɗoru ba.
Zan baka misali ni akaran kaina na yi kiwon raguna lokacin da marigayi Tijjani Gaya yake raye, ya sa yi raguna da na kiwata da shanun gabaɗaya ya rabar da su, kuma yaban kuɗina a dunƙule, hakan ya taimaka min sosai na samu damar da nake amfani da ita a harkar kiwo.
Idan ace za a samu mutane irin su Tijjani Gaya wajan sayan kiwon da mata suka yi, ko shakka babu mata za su samu sauƙin rayuwa, kuma za a samu raguwar talauci a tsakanin al’umma.
Har yanzu kina kiwon?
Har yanzu ina yin kiwo kuma yana taimaka min kuma akwai buƙatar ace gwamnati ta shigo ta tallafa wa mata ‘yan ƙungiyata a harkar noma da kiwo, domin su ma su zama masu dogaro da kansu.
Na gode.
Ni ma na gode.
