“Har yanzu aljanu na zo min a barci don gaya min abinda zai faru”
Daga UMAR AKILU MAJERI
Jamila Adamu Gombe ‘yar mafarauta ce da ta yi fice akan harkar tsaro a Hukumar tsaro ta civil defense wadda hukumar take alfahari da ita wajan iya sarrafa bindiga.
Hajiya Jamila, ta taɓa samun lambar yabo akan ƙwarewar harbi a lokacin da ta je samun wani horo na sanin makamar aiki a Jihar Katsina a lokacin da ta halarci horon ƙwarewa akan harbi da aka shiryawa ma’aikatan hukumar su 205 a lokacin ita kaɗai ce mace a cikinsu kuma ita ce ta zamo zakara a wajan gasar harbin.
Jamila ta shaida wa wakilinmu cewa idan mutum zai tsaya a rabin kilomita ya cira mata yatsa ya ce ta harbi yatsan ita kuma zata cire mar yatsan ba tare da ta harbi wani sashe na hannunsa ba saboda haka ne ake ce mata Jamila sharp shooter.
Wakilinmu na Jihar Jigawa Umar Akilu Majeri ya samu ikon zantawa da Hajiya Jamila Adamu a ofishinta na ciɓil defense da ke Dutse. Ga yadda tattaunawar ta kasance;
MANHAJA: Mai karatu zai so ya san tarihinki a taƙaice?
HAJIYA JAMILA: Sunana Jamila Adamu Gombe. Ni ýar asalin Jihar Gombe ce. Ina da kimanin shekara 45 a duniya a halin yanzu. A gefen iyaye kuwa, iyayena mafarauta ne.
Gidanmu suna yin farautar namun daji irinsu gada da maciji, wato mesa. Iyayena suna ɗiban kwan mesa suna dafa mana muna ci, shi kuma ɓawon kwan suna haɗa maganin sanyi ana taimaka wa masu larurar ciwan sanyi.
Tun ban fi shekaru 15 a duniya ba na san iyayena da kakana suna yin farauta a gidanmu, domin farauta gadarta muka yi. Mu gidanmu mafarauta ne, domin kakana idan ya tafi farauta ya kan yi kwana bakwai a daji bai dawo gida ba, kuma a lokacin da zai dawo gida yakan dawo ne da kayan nama niƙi-niƙi ya yi bandar su.
Ance ku mafarauta kuna da sihiri da ku ke amfani da shi wajan shiga daji ko mu’amala da aljanu. Shin haka ne?
To ni dai alokacin ina yarinya na kan yi magana da aljanu domin suna zuwa wajena a siffar mutane kuma na kan yi magana da su.
Kuma har yanzu suna zuwa min a cikin barci su gaya min saƙo ko mai kyau ko marar kyau. Akan duk wani al’amari da yake shirin faruwa ko zai faru su yi min magana su faɗa min duk wani labari daban sani ba.
Shin Gaskiya ne su aljanu sai sun sa mutum yin wasu abubuwa na wasu buƙatunsu, ko aikata wasu ababe da ba su dace ba, matuƙar mutum yana mu’amalantar su?
Mu dai a gidanmu suna samu mu yi sadakar gumba da nono, wani lokacin ma muna yin yanka da kaji mu yi sadaka da naman, in kuma ba mu yi sadakar ba sun dinga bibiyarmu kenan har sai mun yi.
Shin su waɗannan aljanu na gado ne ko kuwa aljanun ƙofar gida ne?
Aljanun gado ne domin yanzu haka ma yara tana can tana bayar da magani acan garinmu.
To ke yaushe ne kika fara ganin aljanun da idonki kuma kika fara yin magana da su?
Na fara ganinsu tun ban fi shekara goma ba a duniya. A haɗuwarmu ta farko aljanun tsorata ni suka yi a lokacin da na je zan yi bahaya a wata matonar ƙasa. Sau uku suna yin tsawa kada na yi bahaya shi ne da na tashi ban yi ba naje gida sai zazzaɓi ya kama ni.
Da na koma gida ina zazzaɓi shi ne aljanun suka lulluɓe ni sanye da fararen kaya da baƙaƙen kaya a jikinsu. Da na farka shi ne na je na shaƙe wata kishiyar kakata saboda mayya ce, shi ne ake zargin ko ta ba ni naman mayu ne, ni ma ko na zama mayya ina gane-gane marasa kyau irin nasu na mayu. Shi ne kakata ta kai ni wajan wani mai magani a wani kauye aka toshe min idanu na daina yin gane-ganen da nake yi.
Shi ne shi mai maganin ya ba wa kakata shawarar su bar min aljanuna za su taimaka min a rayuwa kuma su taimaki jama-a. Ni ba ni da wata maita a tare da ni, amma kakata ta ƙi sai da aka raba ni da aljanun domin na daina gane-ganen.
To yaya aka yi kika shiga aikin ɗamara?
Na shiga aikin ɗamara saboda ina da sha’awar aikin, domin sau tara ina ƙoƙarin shiga aikin ba a ɗauke ni ba, sai a karo na goma na samu na shiga aikin da taimakon wani ɗan siyasa Alhaji Tasiu Soja a lokacin yana aiki a nan.
Kafin na shiga wannan aikin na yi ƙoƙarin shiga aikin soja da police, amma Allah bai yarda ba shi ne na shiga aikin ɗamara na civil defense anan abincin yake.
Na fara aiki a matsayin yar sa-kai a civil defense babu albashi sai da na kai shekara shida ina aiki babu albashi daga baya aka ban takardar ɗaukar aiki na fara aiki a matsayin constable, ga shi yau na kai matsayin inspector a wajan aikin.
Shin da gaske ne kin yi fice wajan harbi da bindiga ?
Haka yake na yi fice a fagen harbi da bindiga. Iya harbi na addu’a ce ba ni na fi kowa ba. Addu’a ce tasa nake yin nasara akan duk abinda na yanke shawara zan harba bana yin kuskure cikin yaddar Allah duk abinda aka nuna min na harba sai na same shi.
Ko kuna da alaƙa da mafarautan zafgai na Jihar Bauchi ?
Ni dai iyakar sanina iyayena ba su da wata alaƙa da maharban zafgai ta Jihar Bauchi domin mu dai ‘yan asalin Jihar Gombe ne kuma muna da ƙwarewa wajan iya harbi tun muna yara harbi gadarsa muka yi domin mu mafarauta ne.
Shekarunki nawa kina wannan aikin?
Yau shekara 21 ina yin wannan aiki. Na fara tun ina ‘yar sa-kai har na kai inspector a yanzu.
Menene burinki?
Burina shi ne Allah ya ɗaukaka wannan hukuma ta civil defense.
Menene ya fi ɓata maki rai a wannan aikin?
Abinda ya fi ɓata min rai shi ne ‘challenge’ ma’ana ayi min faɗa a bainar jama’a. Maimakon a kira ni gefe agaya min laifina bana san ayi min faɗa a gaban jama’a. Ni ýar adam ce ban wuce na yi kuskure ba, amma magana ta gaskiya bana san irin wannan faɗan.
Yaya batun abinci, wane ki ka fi so?
Babu abincin da bana ci, amma na fi san tuwan laushi miyar taushe da miyar ganyan aduwa, su nafi so a rayuwata.
Menene shawararki ga mata ‘yan’uwanki masu sha’awar shiga wannan aikin?
Shawarata ga yara mata su dage sosai, kada su yi ƙasa ga gwiwa wajan bada ƙoƙari. Su bada gudunmawarsu wajan samar da tsaro a Nijeriya domin mata suna da muhimmiyar gudunmawar da zasu bayar a harkar tsaro a Nijeriya.
Wanna abu ne ba za ki taɓa mantawa da shi ba a rayuwarki?
Bazan manta da horon da na samu ba akan harkar harbi da na je na samu a Katsina. Na sha wahala matuƙa gayan, musamman awani ruwa da ake riƙa fesa mana da kuma rarrafe wato scrolling da aka samu muka yi a lokacin da muka je horon ƙwarewa akan harbi domin anan ne na samu lambar yabo ta harbi daga cikin mutun 205 ni ce mace ɗaya tilo cikin maza 205 da na samu damar zama zakara wajan ƙwarewa ta harbi a fagen harbi.
Me ya fi ɓata maki rai a rayuwarki bakiɗaya?
Babu abinda ya fi ɓata min rai kamar lambar yabo da aka ban a Jihar Katsina aka karrama ni akace idan mun dawo gida Jigawa za a ban lambar girmamawa, amma har yanzu aka hana ni ba abinda wannan abin inna tuna shi yana ɓata min rai sosai, domin ban san dalilin da ya sa aka hana ni ba. Ko ƙabilanci ne ko kuma me ya sa ban sani ba.
Ko kuma anyi min haka ne don ni ba ‘yar Jigawa ba ce ko kuma saboda ni kaɗai ce mace a cikinsu kuma aka samu na fi su ƙwarewa ko hakan ya sa aka ƙi ba ni lambar yabo aka hana ni.
Hajiya Jamila na gode.
Ni ma na gode.
