Ashabul Kahfi: Ma’abota kogo su bakwai

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ 

Daya daga cikin manyan mu’ujizozin Qur’ani shine labarin da Allah ya bayar na Ashabul Kahfi. Labari ne na tsantsar Imani da kaɗaituwar Allah Wanda ba shi da abokin tarayya. Duk da cewa labarin ya shafi Kiristoci, amma Attaura da Linjila duk ba su kawo labarin ba sakamakon cewa abin ya faru ɗaruruwan shekaru bayan saukar waɗannan littafai.

Labarin ya samo asali ne sakamakon Kafiran Makka sun gayyato wasu malaman Yahudawa daga Madina, saboda su na da ilimin littafi, domin su ƙalubalantar musu Annabi Muhammad (SAW). Yahudawan sun ƙalubalanci Annabi da ya ba su amsoshin wasu tambayoyi guda uku, waɗanda su ka haƙƙake cewa sai Annabin Allah kaɗai zai iya sanin amsoshin. ɗaya daga cikin tambayoyin shine ya ba su labarin ma’abota kogo, domin babu wani saukakken littafi da ya bayar da labarin kuma kasancewa daga Makka zuwa garin da abin ya faru kilomita 3000 ne, don haka Annabi ba zai iya sanin cikakken labarin ba sai dai idan ya na karɓar wahayi da gaske. Ragowar tambayoyin su ne ya yi musu bayanin yaya rai ya ke da kuma labarin Zulƙarnain. Nan da nan Annabi ya ce su dawo gobe zai ba su amsa. Amma, sai Allah ya ƙi saukar masa da wahayi na tsawon kwanakin 15, domin Allah na son koya mana darasin cewa:

Q18:23-24 “Kuma kada lallai ka ce game da wani abu “Lallai ni mai aikatawa ne ga wancan a gobe. Face (ka ce) idan Allah ya so” 

Rashin ambata cewa zai ba su amsa gobe “Insha Allah” sai aka ƙi sanar da shi ta yadda har ya zama abin zunɗen Yahudawan da Kafiran Makka.

Bari mu koma baya cikin tarihi yadda za a fahimci wannan labari na Ashabul Kahfi. Wato kafin zuwan Musulunci a ƙarni na 7, Kiristoci tsawon ɗaruruwan shekaru sun kasance cikin gagarumin rikici na aƙida game da matsayin Annabi Isa (AS); shin Annabi ne ko kuwa ɗan Allah ne?

A shekarar 325 AD ƙarƙashin mulkin Constantine ya kirawo Taron gangami na manyan Malaman Kirista na Duniya, wato taron “Gangamin Nicea” inda bayan tafka muhawara ya goyi bayan masu cewa Allah uku ne; wato Uba, Da da Ruhi Mai tsarki kuma fadarsa ta bi hanyoyin amfani da cin hanci ga malamai, tursasawa, kora har ma da kisa ga masu adawa da haka, wato Ariyawa da suka yadda Allah daya ne. Addinin Allah uku (Trinity) ya zama addinin kasa karkashin gwamnatin Constantine. Sannan kuma aka cuso ranar 25 ga Disamba ta zama ranar kirsimeti domin maye gurbin ranar bautar gunkin Sol Invictus na bautar Rana. Wasu rahotanni sun nuna cewa a gadon mutuwarsa, Constantine ya gano kuskuren daukar Allah uku inda har sai da ya karbi sabuwar baptisma ya koma hanyar Ariyawa. Hakan zai iya yiwuwa idan muka yi la’akari cewa magajinsa Constantius II (337-361 AD) ya dabbaka Ariyanci da kokarin yada shi a Cocinan daular, kuma ya kafa majalisar malamai wadanda Ariyawa su ka fi yawa.

Magajinsa shi ma, wato Valens (364-378 AD) ya ci gaba da goyon bayan Ariyanci, abinda ya ci gaba da rura wutar banbanci a addinin Kirista a wancan zamani.

Akidar Allah uku ta dawo da karfinta a lokacin mulkin Theodosius I (379-395 AD) lokacin da yayi Gangamin  Constantinople a shekara 381 AD inda aka yi shelar Allah uku ce cikakkiyar akida, sakamakon dokar Thessalonica wadda aka zartar a 380 AD.

A shekarar 427 AD kuma sai Emperor Theodosius II, ya gayyato Bishop din  Antioch, wato Nestor saboda ya na da ra’ayin aƙidar Ariyanci. Nestor bai yarda da cewa Maryamu Uwa ce ga Allah ba kuma babban abokin hamayyarsa shine Cyril, wato Bishop din Aleɗandria wanda ya kashe zakakurar masaniyar nan, wato Hypatia wadda ta ke bada darasin kimiyya da falsafa a birnin Aleɗandria. A Cocin Constantinople, Nestor yayi doguwar huduba na watsi da matsayin Maryamu a Uwar Allah, ya baje kolin siffofin ubangiji sannan ya kammala da tambayarsu “Shin Ubangiji me wadannan siffofi shine za’a ce ya na da Uwa?”

Malaman Cocin da ba su ji dadin kalaman Nestor ba sun dauki makami don kare waccan akida, abinda ya tilastawa Emperor kiran taron muhawara wadda aka fi sani da “Muhawarar Ephesus” (Council of Ephesus) kamar yadda shekaru Dari a baya, Emperor Constantine ya kira taron Muhawarar Nicea a shekarar 325 AD inda aka tabbatar da maganar Allah uku a Kiristanci. Daular Byzantine ta sake fadawa rudanin banbancin akida musamman a garuruwan Constantinople (Babban birnin daular), Aleɗandria (Cibiyar ilimi) da birnin Rum (wanda yake Cibiyar kasuwanci).

Dole Theodosius II, ya kira wannan taro a Ephesus domin a jaddada akidar Allah uku (Trinity) a fadin daular. Duk kokarin Nestor wajen ganin an dubi hujjoji daga linjila wadanda su ka ci karo da wannan akida, Malaman sun yi kunnen-uwar-shegu da bukatarsa, kuma ba tare da bashi dama ko sauraren hujjojinsa ba an yanke hukuncin korarsa zuwa hamadar Egypt inda aka yi ta azabtar da shi har mutuwarsa. Makiyansa, sun shaida bayan mutuwarsa cewa “Tsutsotsi sun cinye harshensa Mai Ridda, Kuma daga zafin hamadar Egypt, yanzu ya kare a tsananin zafin jahannama”

Tun da aka yi shelar wannan akida ta Allah uku a shekarar 325 AD, akasarin Kiristoci sun rungumi akidar, Yan kalilan ke marawa akidar Allah daya baya, duk da sanin barazanar tursasawa ko kisa da zasu iya fuskanta. Wadannan Yan kalilan su ake kira da Ariyawa, saboda ba su yarda da Allantar Yesu ba. Cikin irin wadannan masu akida ne aka sami mutanen nan bakwai ma’abota kogo. Sun tsere cikin daji inda su ka buya a wani kogo. Daga dukkan alamu, wadannan waliyyan Allah a zamanin Sarki Constantine lamarinsu ya faru, idan mu ka yi la’akari da wasu hujjoji. Abin la’akari na farko shine; hujjar Qur’ani cewa sun yi shekaru 309 su na barci, kuma ita Surar da Allah ya kawo labarinsu, wato Kahfi, an saukar da ita a shekara ta takwas da da’awar Manzo ta kira. Idan muka hada lissafin kaga zai kasance lallai a tsakanin shekarun mulkin Constantine (306-337 AD) ne, kuma shine yayi daidai da lokacin da aka fara yiwa masu akidar Allah uku barazana bayan an fidda dokar Nicea wadda ta haramta Ariyanci sai dai akidar Allah uku.

Allah ya bude labarin Kahfi da gargadi cewa;

Q18:4 “Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda suka ce: “Allah yanã da ɗa.”

Allah ya saukar da labarinsu domin jaddada kadaituwar sa, kuma da Jan kunne ga bautawa waninsa, abinda ka iya kutsawa cikin addini ya sami gindin zama har ya kori akida ta gaskiya. Duk da Annabi Isa bai gushe yana kira ga kadaitar Allah ba, kuma bai taba yada akidar cewa Allah uku ne ba, yau an wayi gari wannan dabi’ar ita ta mamaye akidar Kiristanci.

Labarin ya ci gaba da cewa;

Q18:10-11 “A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: “Ya Ubangijinmu! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al’amarinmu.”Sai Muka yi dũka a kan kunnunwansu, a cikin kõgon, shẽkaru mãsu yawa.”

Sun buya a kogo, sai Allah ya yi amfani da wani tsari na halittar dabbobi, wanda ke iya baiwa dabba damar dadewa sosai ta na barci, wato hibernation. Dabbobi masu zama a yanayin sanyi kan iya kiwo sannan su shiga barci na tsawon watanni kafin Hunturu ya wuce saboda ana samun karancin abinci. A wannan yanayi sai dumin jiki ya sauka sosai, haka ma bugun zuciya, sadarwa ta yi kasa yadda za a iya dadewa ana barci, yadda jiki baya bukatuwa da abinci kamar ana farke. A wannan yanayi ma’abota kogo suka kasance;

Q18:25 “Kuma suka zauna a cikin kõgonsu shẽkaru ɗarĩ uku kuma suka daɗa tara.”

Koda yake wannan yanayi na dogon barci (hibernation) ba a taba samunsa a Dan Adam ba, bincike da ake gudanarwa na kimiyya ta zamani ya nuna cewa jikin Dan Adam zai iya shiga wannan yanayi ta hanyar abinda ake kira da induced hypothermia, wato rage bugawar Zuciya, sauke dumin jiki (Temperature) ya yi kasa sosai yadda bukatar iska (oɗygen) zai yi matukar raguwa. Kuma ko wajen yin tiyata (surgery) da a induced coma, mun ga yadda amfani da anaesthetic (maganin barci) ka iya sa a yi irin wannan barci mai kama da mutuwa na dogon lokaci.

Bayan farkawar su, sai su ke tsammanin barci su ka yi na gajeren lokaci, abinda ke dada tabbatar mana da cewa a cikin barci lokaci na tsaya mana cak har sai mun farka. Kuma wannan farkawa tasu bayan shekaru 300 tabbaci ne na afkuwar tashin kiyama;

Q18:21 “…Waɗanda suka rinjãya a kan al’amarinsu suka ce: “Lalle mu riƙi masãllãci a kansu.”

Allah ya Adana mana labarinsu ba kawai a Qur’ani ba, har a tarihance yadda aka gano kogon da su ka zauna wanda a yanzu haka ke cikin kasar Turkiya a wani dutse da ake kira Mount Pion (ko Mount Coelian) a can Ephesus (kusa da garin Selçuk  da ke kasar Turkiya), wannan masallaci da aka gina a wajen, a shekarun  1926–1928 masana ilimin tarihi ta hanyar binciken kaburbura (Archeologist) sun hake shi kuma an sami kasusuwan mutane binne a wajen. Wajen ya zama wajen ziyara daga masu yawon bude Ido da mahajjata. Allah ya yi bayanin hatta inda kogon ke fuskanta, cikin;

Q18:17 “Kuma kanã ganin rãnã idan ta fito tanã karkata daga kõgonsu wajen dãma kuma idan ta fãɗi tanã gurgura su wajen hagu, kuma su, sunã a cikin wani fili daga gare shi” 

Allah ya tabbar cewa bakin kogon na fuskantar Arewa, yadda Rana ke fitowa ta damansa, ta fadi a hagunsa yadda zafin Rana ba zai doshe su kai tsaye ba.

Labarin ma’abota kogo, labari ne na juriya da jajircewa da Imani da kadaita Allah, da kuma yaki tsakanin alheri da sharri. Babban darasi gare mu shine, wajibi mu rike koyarwar littafi duk rintsi. Idan mu ka ki dabbaka littafi, to da sunan malanta za’a shigowa addini da shirka da bautar wasu ba Allah ba, da sunan addini. Kamar yadda kiri-kiri Kiristoci su ka koma bautar Allah uku maimakon daya. Abinda kuma ya jefa su haka bai wuce rashin aiki, sau-da-kafa, da linjila ba. Domin babu inda maganar Allah uku ta zo a bakin Yesu. Amma an wayi gari wannan shirka ta mamaye kaso 80% na masu bin addinin Kirista.

Tun shekarar 325 AD Kiristoci ke fama da shirka, sakamakon fassarorin littafi na manyan malamansu irinsu St Paul, St Augustine, Tertullian, Calvin da wasu da dama. To ahir din mu musulmi, domin mu ma fa, tun Karni na farko bayan wafatin Manzo, addininmu ya karkasu zuwa bangaranci daban daban, irin na su Kharijawa, Yan Shi’a da Yan Sunna, wanda wutar ke ta ruruwa kawo yanzu kuma ta kassara mu.

Jummu’a Mubarak.

Ali Abubakar masani ne a birnin Kano

By ukarofi