Na sha ganin yara mata na wulaƙanta saboda jinin al’ada – Hauwa Musa Babaji 

Spread the love

“Iyaye su ba wa ‘ya’yansu mata murya, su saurare su”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Hauwa Musa Babaji matashiya ce ýar gwagwarmaya, malamar makaranta, kuma ýar kasuwa, wacce ke zaune a garin Gombe. Ita ce shugabar ƙungiyar Teens Care Foundation, wacce ke tallafawa rayuwar yara mata da suka fara shiga shekarun balaga. Tana gudanar da ayyuka da dama na wayar da kai, da suka haɗa ba da shawarwari ga ýammata kan yadda za su tunkari ƙalubalen rayuwa, ta fuskar ilimi, lafiya, tsafta, da mu’amalarsu da yara maza. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya tattauna da ita game da yadda take samun nasarar gudanar da waɗannan ayyuka da kuma burin ta nan gaba a siyasa. A sha karatu lafiya. 

MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.

HAUWA: Sunana Hauwa Musa Babaji. Ni ‘yar asalin Jihar Gombe ce. Ni ce shugabar ƙungiyar mata ta Nigerian Girls Guide Association reshen Jihar Gombe. Sannan harwayau, ni malamar makaranta ce, kuma ƙwararriyar mai ba da shawara ga yara masu tasowa, wato adolescent counselor. Ni ƴar kasuwa ce kuma mai wayar da kai kan lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa. Ina cikin gwagwarmayar kare haƙƙoƙin yara mata ce (girl child adɓocate), da ba da shawarwari kan cigaban rayuwar mata, ma’ana Gender Deɓelopment Adɓocate, kuma mai koyar da ƙwarewa kan ayyukan baiwa da basira, wato life skills facilitator.

Ni ce na kafa Gidauniyar Teens Care Foundation, wata ƙungiya mai zaman kanta da ke mai da hankali kan tallafa wa matasa, musamman ƙananan yara mata masu tasowa, wanda aka fi sani da Young Adolescent Girls. Gidauniyar na aiwatar da shirye-shirye da ayyuka da suka shafi ilimi, kiwon lafiya, kare hakkin yara mata, da koya musu ƙwarewar rayuwa domin su tashi da cikakken tunani da damar kare kansu daga haɗurra rayuwa. Muna kuma gudanar da wayar da kai a makarantu da unguwanni kan batutuwan da suka shafi cin zarafi, jinin al’ada, da mahimmancin ilimi ga yara mata.

Gaya mana tarihin rayuwarki?

An haife ni a Jihar Gombe, inda na girma tare da samun ilimi na farko da na sakandire. Na tashi ina da sha’awar ilimi da taimakon al’umma, musamman mata da matasa. Wannan sha’awa ta sa na cigaba da karatu har na samu digiri na farko a fannin koyarwa, sannan na wuce na yi digiri na biyu (M.Ed) a fannin Guidance and Counseling.

A rayuwata, na fuskanci ƙalubale da dama, musamman a matsayin mace da ke burin ganin ‘yan mata sun samu ilimi da ‘yancin da ya dace da su. Wannan ne ya zaburar da ni na fara aikin wayar da kai da kuma tallafa wa yara mata da matasa ta hanyar kafa gidauniyata mai suna Teens Care Foundation da kuma aiki da wasu kungiyoyi a Jihar Gombe harma da wajenta.

A wannan Gidauniya, na aiwatar da shirye-shirye da dama a makarantu da al’umma da suka shafi kare hakkin yara mata, lafiyar jiki da kwakwalwa, da koyar da ƙwarewar rayuwa. Haka kuma, ina aiki da hukumomi da kungiyoyi wajen wayar da kai kan batutuwan da suka shafi cutar yoyon fitsari( ɓɓF), jinin al’ada, cin zarafi, da lafiyar Kwakwalwa, da kuma bada shawarwari ga yara masu tasowa, da sauransu.

A halin yanzu, ina koyarwa a makaranta, ina aikin ba da shawara wa yara, kuma ina jagorantar ayyukan ƙungiyar Nigerian Girls Guide Association a matsayin shugabar mata a Jihar Gombe da sauran wasu gogarmayar rayuwa wanda ba a rasawa. 

Tun a wanne lokaci ki ka fara shiga ayyukan ƙungiyoyin sakai?

Na fara shiga harkokin ƙungiyoyin sa kai tun ina ƙarama, amma na fara aiki da ƙwazo a hukumance tun lokacin da nake a jami’a. A lokacin ne na fara shiga ƙungiyoyin da ke tallafa wa yara mata da matasa, inda nake halartar taruka, bada gudummawa a shirye-shirye da kuma gudanar da wayar da kai a makarantu da unguwanni.

Sha’awata ta taimakawa jama’a da kare hakkin yara mata ne ya ƙarfafa ni na shiga ƙungiyoyi da dama da kuma kafa Teens Care Foundation. Wannan ya ba ni dama in taimaka wa matasa musamman ‘yan mata ta fannoni da dama – daga kiwon lafiya, ilimi, shawarar rayuwa, har zuwa tsare kansu daga cututtuka da cin zarafi.

Haka kuma, shigata aikin sakai ya buɗe min ƙofofin haɗin gwiwa da hukumomi da ƙungiyoyi da suka haɗa da Girl Guides, ƙungiyoyin mata da na matasa da wasu ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin mata a cikin gida da wajen Jihar Gombe.

Me ya ja hankalinki ki ga ya dace ki fara gangamin wayar da kai akan jinin al’ada?

Abin da ya ja hankalina na fara gangamin wayar da kai akan jinin al’ada shi ne ganin irin yadda yara mata ke fama da rashin ilimi kan jinin al’ada, kunya, da kuma rashin kayan tsafta yayin da suke cikin al’ada. A wasu lokuta, hakan na sa su daina zuwa makaranta ko su ji kunyar yin hulɗa da jama’a a cikin gida ko a waje. Na kuma sha ganin yara mata suna fuskantar tsangwama da wulaƙanci saboda jinin al’ada ya fara fita musu a bainar jama’a ba tare da sun fahimci me ke faruwa da su ba.

Wannan lamari ya taɓa zuciyata, ya kuma sa na fahimci cewa akwai buƙatar a wayar da kai sosai akan wannan batu, musamman a yankunanmu na Arewa inda har yanzu jinin al’ada ana ɗaukar sa a matsayin abin kunya ko haramun a yi magana akai.

Ta hanyar Teens Care Foundation da kuma matsayin da nake da shi a Girl Guides, na fara shirya taruka da ziyartar makarantu da al’umma domin ilimantar da yara mata game da jinin al’ada, yadda za su kula da kansu, da kuma ƙarfafa musu gwiwa su fahimci cewa wannan al’ada ce ta halitta, ba abin kunya ba ne.

Ina kuma raba kayan tsafta kamar audugar tsare jinin al’ada wato pad, da koyar da yadda ake sarrafa su cikin tsafta da mutunci. Wannan aiki ya zamo wani muhimmin ɓangare na aikina na kare haƙƙoƙin yara mata da ƙarfafa su.

Waɗanne hanyoyi ku ke bi ƙarƙashin ƙungiyar ku wajen isar da saƙonnin ku ga waɗanda abin ya shafa?

A ƙarƙashin ƙungiyata ta Teens Care Foundation da kuma matsayin da nake da shi a Nigerian Girls Guide Association reshen Jihar Gombe, muna amfani da hanyoyi daban-daban wajen isar da saƙonni ga yara mata da matasa. Muna ziyartar makarantu don gudanar da tarurruka da wayar da kai kai tsaye kan batutuwan da suka shafi jinin al’ada, kariya daga cin zarafi, da kuma ƙarfafa yara su amince da kansu. Haka kuma, muna shirya tattaunawa da iyaye, malamai da shugabannin al’umma domin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen kare martabar yara mata. Muna kuma raba kayan tsafta kamar sanitary pads, tare da koyar da yadda ake amfani da su cikin tsafta da mutunci. Muna amfani da kafafen sada zumunta kamar Facebook da WhatsApp wajen yaɗa bayanai da bidiyo masu ilimantarwa. Haka zalika, muna zuwa gidan talabijin da rediyo domin yada shirye-shiryen wayar da kai ga jama’a da ke cikin gari da karkara. Muna kuma shirya horo na musamman domin koyar da ƙwarewar rayuwa da dogaro da kai. A ƙarshe, muna haɗin gwiwa da hukumomi da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin ƙarfafa ayyukanmu da kai saƙonni ga al’umma da cibiyoyi masu tasiri. Ta waɗannan hanyoyi ne muke tabbatar da cewa saƙonninmu sun isa inda suka fi dacewa.

Akwai wani abu da ya taɓa faruwa da ke ne wanda ya zaburar da ke ki ka fara wannan faɗakarwar?

E, akwai wani abu da ya taɓa faruwa da ya ƙarfafa ni sosai wajen fara wannan faɗakarwa, musamman a ɓangaren jinin al’ada da kare haƙƙoƙin yara mata. A wani lokaci na haɗu da wata yarinya a makaranta wadda ta samu jinin al’ada a karon farko, amma saboda rashin sani kuma bata da kayan tsaftace jiki, ta ji kunya ƙwarai, har ta fita daga aji tana kuka. Abokan karatunta sun fara tsangwama da dariya a kanta, kuma malamai ba su fahimta ba, hakan ya sa ta daina zuwa makaranta na tsawon lokaci. Wannan lamari ya ɗaure min kai, ya kuma motsa zuciyata – sai na fahimci irin gagarumin giɓin da ke akwai wajen ilimantar da yara mata game da jikinsu da lafiyarsu.

Haka kuma, na ci karo da wasu yara mata a karkara da ke amfani da tsofaffin kaya a matsayin pad, wanda hakan ya haddasa musu cututtuka da jin kunya. 

Daga wannan ne na fahimci cewa akwai buƙatar a buɗe tattaunawa da wayar da kai game da jinin al’ada da sauran hakkokin jiki na yara mata, ba tare da jin kunya ba. Wannan ƙwarewar rayuwa da abubuwan da na gani da ido ne suka zaburar da ni na sadaukar da kai wajen wannan aiki.

Wanne tallafi ku ke bai wa yara mata da suke fama da talaucin audugar tare jinin al’ada?

Mun fahimci cewa talauci da rashin kayan tsafta yana shafar yara mata sosai lokacin da suke cikin jinin al’ada, musamman a yankunan karkara. Saboda haka, muna bayar da tallafi iri daban-daban domin taimaka wa waɗanda abin ya fi shafa.

Na farko, muna raba kayan tsafta kyauta kamar sanitary pads, omo, da panty ga yara mata da ke fama da talauci, makarantu da yankunan karkara. Wannan na taimaka musu su ci gaba da zuwa makaranta cikin kwanciyar hankali ba tare da jin kunya ko barazana ba.

Na biyu, muna koyar da hanyoyin yin pad ɗin mai tsafta da hannu (reusable pads) domin waɗanda ba za su iya saye kullum ba. Hakan na ba su dama su kula da kansu cikin tsabta da mutunci.

Na uku, muna ba su ilimi da ƙarfafa gwiwa, ta hanyar shirya horo da tarurruka kan yadda za su kula da kansu yayin al’ada, su fahimci jikinsu, su kuma daina jin kunya. A wasu lokuta, muna haɗa wannan da shirin koyar da sana’o’i domin su samu dogaro da kai.

Muna kuma haɗin gwiwa da wasu kungiyoyi da hukumomi wajen samun tallafin kayan al’ada da yaɗa saƙon cewa jinin al’ada ba laifi ba ne kuma bai kamata ya hana mace cigaba da rayuwa ba.

Ina ku ke samun kuɗaɗen gudanar da ayyukan ku da tallafin da ku ke bayarwa?

Muna samun kuɗaɗen gudanar da ayyukanmu daga hanyoyi daban-daban. Na farko, muna dogaro da gudunmawar kai tsaye daga abokai, iyalai, da masu ruwa da tsaki da suka yarda da manufofinmu kuma suke goyon bayan abin da muke yi. Wasu lokuta, muna karɓar tallafi daga ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) da ke son haɗin gwiwa da mu don aiwatar da shirye-shiryen wayar da kai a makarantu da al’umma.

Haka kuma, a matsayina na mai hulɗa da cibiyoyi da dama, muna iya samun dama daga shawarwari ko gayyatar haɗin gwiwa daga hukumomi ko masu tallafawa matasa, inda muke kawo shiri da aikin da za a yi tare. A wasu lokuta kuma, ni da wasu daga cikin mambobinmu muna saka kuɗi da kayanmu na ƙashin kai don ganin cewa mun cika alƙawuran da muka ɗauka, musamman lokacin da ba mu da masu ɗaukar nauyi kai tsaye.

A ƙarshe, muna da burin faɗaɗa ayyukanmu ta hanyar neman tallafi daga manyan ƙungiyoyi na cikin gida Nigeria domin mu iya kaiwa ga yara mata da dama da ke cikin buƙata fiye da yanzu

Waɗanne matsaloli ýan mata suke fuskanta wajen tafiyar da rayuwar su, da ya kamata iyaye, ýan’uwa da sauran jama’a su duba?

Yara mata na fuskantar manyan ƙalubale a rayuwarsu da yakamata iyaye, ‘yan’uwa da al’umma su duba sosai. Babbar matsala ɗaya ita ce rashin ýancin yi wa kansu zaɓin abin da suke so, kan rayuwarsu, kamar inda za su yi karatu, lokacin aure, ko yadda za su kula da lafiyar jikinsu. A mafi yawan lokuta, ana yanke musu shawara ba tare da an saurare su ba.

Haka kuma suna fama da matsalar cin zarafi, da fyaɗe, da nuna musu bambanci, auren dole, da nuna wariya ko a gida, ko makaranta. Iyaye da dama na fifita ‘ya’ya maza fiye da ‘yan mata, musamman wajen karatu da samun dama. Waɗannan abubuwa suna tauye cigaban mata da hana musu cimma burikansu.

Wata babbar matsala kuma ita ce talaucin yadda za ta kula da al’adar ta ta wata-wata, inda yawancin ‘yammata ba sa samun pad ko ilimin kula da jinin al’ada. Wannan yana sa su rasa darussa a makaranta, su kuma ji kunya da rauni a kai. Bugu da ƙari, akwai rashin ilimi a kan jima’i da matakan hana ɗaukar ciki, wanda ke jefa su kamuwa da cututtuka. 

Don haka ina kira ga iyaye da duk masu ruwa da tsaki da su riƙa bai wa yara mata murya, ana sauraron su, ana tallafawa burikan su, don su cimma nasara a rayuwa. Yarinya na da burin rayuwa kamar kowa kuma idan aka ba ta dama, za ta iya kaiwa ga kowanne mataki na rayuwa.

Shin kin gamsu da kulawar da gwamnati ke cewa tana bayarwa a ɓangaren inganta ilimin ýaýa mata?

Gwamnati ta yi ƙoƙari wajen inganta ilimin yara mata a wasu fannoni kamar ba da ilimi kyauta, samar da daidaito wajen neman ilimi, amma har yanzu akwai giɓin da ake buƙata a cikinsa. Gwamnati yakamata ta samar da pad a kowacce makarantar sakandire domin yara mata su samu damar gudanar da jinin al’ada cikin girmamawa da mutunci. Wannan zai taimaka wajen rage matsalolin da suke faruwa lokacin da yaran mata ke cikin jinin al’ada, musamman a ƙauyuka da yankunan da yara mata ba su da kayan tsafta ko kudin sayen pad. Idan gwamnati ta samar da wannan tallafi, zai bai wa yara mata damar cigaba da karatu cikin kwanciyar hankali ba tare da jin kunya ko wata irin matsin lamba ba. Wannan zai tabbatar da cewa yara mata suna samun damar yin rayuwa mai kyau, suna kauce wa matsalolin lafiya da kuma samun ingantacciyar ilimi.

Kin taɓa fuskantar wani ƙalubale da ya kusa canza miki tunani kan gwagwarmayar da ki ke yi?

Eh, na taɓa fuskantar ƙalubale da dama da har sai da na fara jin kamar na ja da baya. A wasu lokuta, rashin goyon baya daga wasu shugabannin al’umma ko makarantu yana iya sanyawa mutum jin ƙasa da gwiwa. Haka kuma, akwai lokacin da mutane ke ganin faɗakarwar da muke yi musamman game da jinin al’ada ko illimin ‘ya’ya mata wani abu ne da ya saɓa da al’ada ko addini, sai su fara kallonmu da wani irin idon tuhuma.

Na fuskanci irin waɗannan matsaloli a wasu lokuta da har sai da na tambayi kaina ko abin da nake yi yana da amfani ko kuma ko jama’a suna fahimta. Amma duk da haka, duk lokacin da na ga yadda yara mata ke amfana da ayyukanmu, yadda suke samun ƙwarin gwiwa da damar da ba su da ita a da, sai na samu sabuwar ƙarfafa gwiwa in cigaba.

Kuma a gaskiya, waɗannan ƙalubale sun koyar da ni juriyar zuciya, sadaukarwa da kuma fahimtar cewa canji ba ya zuwa da sauƙi, amma muddin ni da sauran masu kishin al’umma mun tsaya tsayin daka, to za mu ga sakamako mai kyau a ƙarshe.

Ba kya ganin wasu za su ce bai dace mace kamar ki, mai ƙananan shekaru ta shiga irin wannan aikin yawon faɗakar da jama’a ba?

E, gaskiya akwai wasu lokuta da mutane ke cewa, “Ai wannan aikin babba ne, bai kamata yarinya ‘yar ƙanana shekaru ta riƙa yawo tana faɗakarwa ba.” Amma ni ina ganin wannan ra’ayi tsohon tunani ne. Ba maganar shekaru ba ce, amma abin tambaya shi ne mece ce manufar mutum? It’s not about age, it’s about purpose. Shekaru ba su hana mutum yin abin da zuciyarsa ke kiransa ya yi, musamman idan yana da niyyar kawo sauyi mai kyau.

Ni dai na shiga wannan aiki ne saboda na fahimci cewa yara mata da yawa suna buƙatar a ji muryarsu, kuma in har mutum yana da ƙwarewa da nutsuwa, to shekarunsa ba matsala ba ne. Domin yaran mata sun fi sauƙin buɗe zuciyarsu ga mutumin da suke gani tamkar su, wanda ya fahimci damuwarsu.

A matsayina na mace kuma matashiya, na fuskanci ƙalubale da dama, amma hakan bai taɓa hana ni cigaba da wannan faɗakarwa ba. Kuma idan ba mu fara magana yanzu ba, wa za mu jira? 

Don haka, ni ina ganin yana da muhimmanci mu ƙarfafa matasa su tsaya, su bada gudunmowa domin ceto rayuwar waɗanda ke buƙata.

Waɗanne nasarori ki ka cimma kawo yanzu?

Za mu ci gaba mako mai zuwa.

By ukarofi