Ekiti: An yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai bisa lalata da ƴar matarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata Babbar Kotu a Ado Ekiti ta yanke wa wani Jayeoba Oluwafemi hukuncin ɗaurin rai-da-rai bisa lalata da wata ƴar shekara 14, wadda ƴar matar da ya ke aure ne.

Mutumin, mai shekaru 56, an gurfanar da shi ne a ranar 4 ga watan Disambar 2020 bisa tuhumar sa da aikata lalata da ƴar shekara 14 wanda yin hakan saɓa wa sashe na 31 ga dokar kare ƴancin ƴaƴa ta jihar ta 2012.

Yarinyar, wadda ƴar aji shida ce a makarantar firamare, a yayin bada ba’asi a kotun, ta ce mutum bayan ya auri matafiyarta, ya kasance ya kan je gidansu a lokacin da mahaifiyartan ba ta nan ko kuma idan ta yi tafiya.

A ranar 26 ga watan Oktoban 2020 ne bayan matar ta yi tafiya, sai mutumin ya je gidan, inda cikin dare ya tashe ta a barci tare da tilasta yin lalata da ita, lamarin da ya sa ta fara zubar da jini.

Bayan hakan ne da wayewar gari, sai ta kira mahaifiyar ta sanar da ita abinda ya faru, inda bayan ta dawo ne sai ta nemi ya ji ta bakinsa, shi kuma ya musanta aikata laifin.

Daga lokacin ne ya cigaba da yin lalata da ita a-kai-a-kai sakamakon mahaifiyar tayi buris da lamarin.

A lokacin da ya fahimci tana sanar da mahaifiyar a duk lokacin da ya kusance ta, sai ya fara mata barazana, inda wata rana da ya nufi dukan ta, sai ta fice daga gidan a guje, sannan ta haɗu da wata mata, wadda ta taimaka wajen sanar da hukuma, lamarin da ya yi sanadin kama shi.

Bayan tabbatar da laifin akansa ne sai Alƙali Adeleye ya yanke masa hukuncin kamar yadda doka ta tanadar.

By Babaji