Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cikakken adawarsa da cin zarafi da danniya da ake yi wa yara, yana mai alƙawarin samar da ƙasa mai lafiya da kariya ga dukkan yara. Wannan ya fito ne a saƙonsa na ranar yara ta duniya da aka gudanar a shekarar 2025. Shugaban ya ce taken bana mai taken “Tsaya tsaida, yi magana: Gina zuri’ar da ba a cin Zarafi” ya dace ƙwarai domin ƙarfafa ɗabi’ar mutunta kowane yaro a cikin al’umma.
Tinubu ya bayyana cewa cutar da yara ta hanyar danniya da cin zarafi ko sakaci ba su da wuri a sabuwar Najeriya. Ya ce, fiye da ɗaya cikin uku na yara a duniya suna fuskantar cin zarafi a kai a kai, inda a Najeriya bincike ke nuna cewa kusan kashi 65% na yara masu zuwa makaranta sun fuskanci danniya ta jiki ko ta tunani. A cewarsa, yaro da ke koyo cikin tsoro ba zai samu ilimi yadda ya kamata ba, haka kuma yaro da ke girma cikin tsoro ba zai girma cikin ƙoshin lafiya ba.
Shugaban ya ƙara da cewa gwamnati tana ɗaukar matakai na kariya ga yara, da suka haɗa da aiwatar da tsarin ayyuka na ƙasa kan kare yara daga cin zarafi (2024–2030). Har ila yau, ya yaba da matakin da jihohi 36 suka ɗauka na ɗaukar dokar kare haƙƙin yara, yana mai cewa doka kaɗai ba za ta wadatar ba. Shugaba Tinubu ya buƙaci iyaye, malamai, shugabannin addinai da al’umma gaba ɗaya su ɗauki rawar gani wajen kare yara. Ya kuma jaddada cewa yara ba ƙididdiga ba ne, su ne zuciyar ƙasar nan da makomarta.
