“Sana’a babbar gata ce a wajen ýa mace”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Fathiyya Auwal Abba ba ɓoyayyiya ba ce a garin Gombe, inda take zaman aure tare da mijinta da ’ya’yanta, kuma take gudanar da harkokinta na kasuwanci. Fitacciyar ýar jarida ce da ke aikin watsa labarai a tashar NTA Gombe, amma kuma duk da ƙalubalen da ke cikin aikin da kasancewar ta uwa, hakan bai hana ta gudanar da kasuwanci da saye da sayarwa ba, don ta ƙara samun hanyoyin shigar kuɗaɗe ta kuma taimaka wa kanta, ýan’uwanta da iyalinta. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Malama Fathiyya ta bayyana masa burin ta na ganin ta kafa babbar cibiyar koyawa mata da ýammata dabarun kasuwanci, kuma ita ma ta ƙara faɗaɗa kasuwancin da take yi.
MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanki da abubuwan da ki ke yi na rayuwa.
FATAHIYYA: Sunana Fathiyya Auwal Abba. Ni ‘yar jarida ce, kuma’ yar kasuwa. Ina yin kayan ƙwalama da maƙulashe irin su tuwon madara, gullisuwa, kwakumeti, iloka, albishi, riɗi da sauransu. Ina ma koyar da mata matasa yadda za su iya yin irin waɗannan kaya na maƙulashe da sauran girke-girke, don su samu madogara. Ina kuma karɓar kwangilar yin girki na manyan taruka kowanne iri, har ma da na gidajen mutane, ga waɗanda ke da ƙyuwar dafawa.
Harwayau, ina sayar da kayayyaki kamar irin su zannuwa da sauransu.
Ba na mantawa, na fara sana’ar sayar da kayan ƙwalama tun ina ‘yar ƙarama, saboda na taso ina da shawarar saye da sayarwa. Tun ba a so a gidan mu, har Allah Ya sa suka yi haƙuri suka bar ni, na cigaba da sayar da iloka da gullisuwa, Har zuwa jami’a. A nan ne ma na samu laƙabin Fatee Condense.
Ki ba mu tarihin rayuwarki da yadda ƙuruciyarki ta kasance.
Ni haifaffiyar Jos ce, a Jihar Filato. An haife ni a Layin ɗanmaraya da ke cikin garin Jos, a ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Na yi karatun firamare a makarantar ƙungiyar mata ma’aikatan Jami’ar Jos, wato Uniɓersity of Jos Women Association. Daga nan sai na tafi Kwalejin Ýammata ta Tarayya da ke Bauchi, ma’ana Federal Goɓernment Girl’s College, inda na yi karatuna na sakandire. Sannan na yi digirina na farko a ɓangaren nazarin aikin jarida a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ƙarƙashin reshen ta dake Kwalejin Koyar da Ma’aikatan Talabijin ta NTA dake Jos. Na samu ƙwarewa akan aikin jarida na talabijin. Cikin ikon Allah yanzu haka ina aikin jarida a tashar NTA dake Gombe. Ina da aure da yara mata guda biyu.
Wanne abu ne za ki ce ya taimaka miki yayin tasowarki da ya ba ki ingantacciyar rayuwa da tarbiyya?
Abubuwan da suka taimaka min yayin tasowa ta suna da dama, amma muhimmi daga ciki shi ne iyayena sun tsaya tsayin daka a kaina wajen bani tarbiyya ingantacciya. Sannan sun saka ni a makarantar Islamiyya ta Darul Ta’adibul Adfaal dake nan Layin ɗanmaraya, inda na ƙara samun tarbiyyar addini da ilimin sanin Allah da ibada. Ba na mantawa da malamin mu na madarassa wanda aka fi sani da Malam Hussaini, ya taimaka min sosai wajen sanin ilimin addini da na inganta zamatakewa Rayuwa. Sannan, wani abu da nake ƙara jin daɗi akai shi ne, idan na tuna cewa na taso a wajen da babu wanda ya yarda zan iya zama wani abu a rayuwa, sai kuma ga yadda Allah ya mayar da ni, nakan ce Alhamdulillahi. Mutane da yawa ba su yi zaton zan iya yin wani abin a zo a gani a rayuwata ba, wai saboda ni bahuguwa ce.
Me ya fara sa miki sha’awar kasuwanci a rayuwar ki?
Kamar yadda na faɗa a baya, tun ina ƙarama Allah Ya sa min son kasuwanci. Ina son saye da sayarwa gaskiya, domin ba na son tambayar a yi min abu, na fi son na yi wa kaina.
Waɗanne abubuwa ki ke yi na kasuwanci?
Ina kwangilar aikin girkin manyan taruka da bukukuwa. Ina saye da sayarwa. Ina sarrafa kayan ƙwalam daɓmaƙulashe, da sayar da zannuwa, mayafai da sauransu.
Yaya ki ke gudanar da duk waɗannan abubuwa a lokaci guda kuma ga hidimar iyali?
Hmm… Gaskiya akwai ƙalubale sosai, musamman kasancewa ta ýar jarida da ke ɓangaren watsa labarai na talabijin, mukan tafi tun safe har dare, sai bayan mun kammala labarai kafin mu koma gida. Sai dai ranakun da ba mutum ba shi da aiki ne zai zauna da iyali har ya gudanar da wasu ayyuka. Amma a hakan Allah yake taimakon mu, mu da yaran bakiɗaya. Abinda na sani shi ne komai yana da lokacinsa kuma kowanne hakki da ke kaina ina ƙoƙarin sauke shi, ba na yarda ɗaya ya danne ɗaya.
Akasari abin da nakeyi shi ne ina tashi tun ƙarfe uku na dare na fara ɗora ruwan wanka, sannan ya shirya abincin da yara za su tafi da shi makaranta. Kafin asuba ta yi na gabatar da ayyukana na ibada. Sai in tashi yara na yi musu wanka ko su yi da kansu, na shirya musu abin karyawa. Idan ranar da zan je aiki ne, na kan shirya abincin rana da abin da zan yi na dare, kafin na fita.
Idan na je ofis kuma, na kan gudanar da ayyukan da aka shirya gudanarwa na ranar, a cikin hakan na kan ɗora tallan kayana a waya, saboda yanzu fiye da rabin kasuwancin a waya muke yin sa. Idan na samu masu buƙatar saye sai na kira wanda ke kai min saƙo ya je ya kai, ko kuma su su zo su karɓa. Bayan na koma gida zan bai wa iyalina lokacin su, idan akwai wani aikin gida na makaranta in taimaka musu. Idan na gama kuma sai in duƙufa aikin sarrafa kayan madara da nake sayarwa kafin na kwanta.
Duka wannan aikin ni kaɗai nake yin su ba tare da tallafin mai aiki ba, kuma yara har yanzu ƙanana ne ba su yi girman da za su min wasu manyan ayyuka ba, sai ɗan abin da ba a rasa ba.
A matsayin ki ta ýar jarida kuma ma’aikaciyar gwamnati, shin kina samun sukunin gudanar da ayyukan ki na ofis da kasuwanci ba tare da wani cikas ba?
Eh kamar yarda na fada kowane ina iya ƙoƙari na wajan bashi hakinsa amma wani lokacin wani ya shiga wani domin ɗan adam ajize ne, amma ina iya ƙoƙarina wajan ganin cewa na ba wa kowa hakkin sa musamman ma yarda nake shiryawa da kuma tsara aikina.
Yaya ki ke kallon muhimmancin sana’a a wajen mace mai iyali?
Ai sana’a babban gata ce a wajen ýa mace. Zan ma iya cewa yanzu sana’a ta zama wajibi ga kowacce mace, musamman matar aure. Saboda ita kaɗai ce hanyar da mace za ta iya dogaro da kanta, ta rufa wa kanta asiri. Sannan da sana’a ne za ta taimaki iyalinta da ýan’uwanta. Ita kanta rayuwar aure yanzu ta zama cuɗani-in-cuɗeka, saboda halin da jama’a ke ciki, mazaje na buƙatar tallafin mu, idan mun haɗa kai da su za mu inganta rayuwar iyalinmu bakiɗaya.
Shin kuna samun haɗin kan mata masu sana’o’i daban-daban a Jihar Gombe?
Kwarai da gaske. Mata ‘yan kasuwa a Jihar Gombe na iya ƙoƙarin su wajen ganin sun tallafa wa ‘yan’uwansu. Misali akwai zaurukan da muke da su a kafafen sada zumunta, inda muke bai wa ‘yan kasuwa damar yin tallan kayayyakin da suke sayarwa. Sannan akwai abinda muke yi da a turance muke cewa, ‘Status Collaboration’, inda kowa zai ɗora sana’ar da ɗan’uwansa yake yi yana taya shi tallatawa. Da zarar kuma ana buƙatar wani abu da ka sa, sai ka yi wa mai kayan magana. Ko ka haɗa mai saye da mai sayarwa su yi magana.
Waɗanne cigaba ko nasarori ki ka samu a dalilin wannan kasuwanci da ki ke yi?
Alhamdulillahi, ni dai sana’a ta yi min komai a rayuwa. Kamar yadda na fara faɗa a baya, tun ina ƙarama nake sana’a. Kuma da ribar sana’a ta na fara sayar wayata ta farko a shekarar 2009. Sannan duk wata buƙata ta yau da kullum sana’a ta yi min.
Kin taɓa fuskantar wani ƙalubale da har ya sa ki ka yi tunanin daina abubuwan da ki ke yi na samun kuɗin shiga?
Dama ai dukkan nasara tana tare da ƙalubale. Sau da yawa na kan cinye jarina, saboda wasu dalilai, sai na sake nema kafin na farauto wani jarin. Akwai kuma wani lokaci da a wajen aiki aka ba ni zaɓi, ko na yi aiki ko kuma na sayar da tuwon madara. A haka dai na dage sosai wajen cigaba da sana’ata, ina kuma cigaba da aikina. Ko shi ma maigidana wani lokaci ya kan yi ƙorafi idan ya ga ina bai wa sana’ata ko aikina muhimmanci, sai na yi ta ba shi haƙuri ina yi masa bayani, kafin Allah Ya sa ya gane.
Wacce shawara za ki bai wa mata masu iyali da marasa aure da ke sha’awar fara sana’a?
Duk sana’ar da mata za su yi to, su nemi albarkar iyaye da amincewar mazajen su, Kuma su bari sana’a ta hana su aiwatar da hakkin ubangiji ko kuma na iyalinsu. A matsayinki ta matar aure ki sani komai yana da lokacin sa. Sannan yana da muhimmanci mu sani amincewar mazajen mu shi ne kwanciyar hankalin mu. Kar ki ga kina samun kuɗi ki yi tunanin kin fi ƙarfin mijinki, wannan kuskure ne da wasu mata kan yi, lallai mu yi musu ɗa’a da biyayya, domin Allah ne ya fifita su a kanmu.
Yaya mace mai ƙaramin jari da ke da iyali za ta iya tattalin kasuwancinta?
Shi kuɗin kasuwanci daban yake da kuɗin ki na hidimar rayuwa. A duk lokacin da ki ke son yin sana’a to, ki sani fa dole ki kawar da kai daga jarin ki, domin ba a taɓa kuɗin da ake kasuwanci da shi. Idan kuwa har za ki taɓa to, sai dai in a matsayin bashi za ki ɗauka, kuma ki tabbatar kin mayar. Yana da kyau mata ku sani cewa jaricewa shi ke sa ka cigaba, sannan ko da wasa idan maigida ya ce ki bashi kuɗin sana’arki ƙi san dabara Ko bayanin da za ki yi masa, yadda zai gane cewa ba a taɓa kuɗin kasuwanci. Domin shi wannan kuɗin ba naki ba ne na sana’ar ne, akwai lokacin kashe su amma sai sun tsaya da ƙafafunsu.
Wanne tallafi gwamnati da masu ruwa da tsaki ke taimaka wa mata a ɓangaren sana’o’in dogaro da kai?
E, ana samun masu taimakawa sosai, daga ɓangaren gwamnati da masu ruwa da tsaki, musamman a ɓangaren tallafin jarin yin sana’a ko bashi, da kuma ba da horo kan yadda za a yi tattalin ƙaramin jari. Sai dai ba kowa ne yake samu ba.
Kina nufin ke ba ki taɓa cin moriyar tallafin da gwamnati ke bayarwa na taimakawa masu ƙananan sana’o’i ba?
E, gaskiya ni dai har yanzu bai iso gare ni ba. Sai dai ina sa rai ko zan dace in samu nan gaba.
Waɗanne damarmaki masu ƙananan sana’o’i suke da shi a Jihar Gombe, don bunƙasa kasuwancinsu?
To, damar dai ita ce taimaka wa juna, musamman tarukan baje-kolin da ake yi, yana bada damar bunƙasa harkokin kasuwanci. Sannan sai batun koyar da dabarun kula da sana’o’i wanda gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu suke yi, shi ma yana ƙara bunƙasa hakar kasuwanci sosai. Kuma mata ýan kasuwa a Gombe suna buƙatar irin haka sosai.
Wanne ƙalubale kasuwancin onlayin yake fuskanta a halin yanzu, kuma yaya za a gyara?
Gaskiya ƙalubalen da kasuwancin onlayin yake fuskanta daga mu ‘yan kasuwar ne. Yawanci mutane za a ɗauki bidiyo ko hoto wanda ba na asalin kayan ba ne, sai a ɗora. Da zarar mutum ya gani ya ce yana so har ya biya kuɗin sa sai kawai a kai masa wani abin daban, ko wanda darajar sa ba ta kai kuɗin da ya biya ba. Yadda za a magance hakan kuwa shi ne mutum ya zama yana da riƙo da gaskiya, kuma ya zama abin da yake tallata wa yana da tabbaci a kansa. Sannan kuma ya zama yana da tambarin kasuwancinsa, mai ɗauke da sunansa da zai sa, wanda zai nuna mallakinsa ne. Kamar ni yanzu in dai kayana ne to, akwai sunan kamfanina ko tambarina, wanda mutun bai isa ya cire ba, ana gani an san nawa ne.
Menene burinki nan gaba a wannan harkokin kasuwancin da ki ke yi?
Na zama malamar koyar da sana’a, kuma na buɗe gidan abinci da shagon sayar da kayayyaki. Na zama idon mata wajen ba da gudunmawa, don inganta rayuwarsu, da ta sauran al’umma baki ɗaya. Ina so na zama mace abin kwatance ga kowa, in sha Allah.
Da karatu, da kasuwanci, wanne ya fi inganta rayuwar mace?
Kowanne da matasayinsa. Sai ka samu ilimi za ka gane abin da ka ke yi, domin ko ba karatun boko ba, shi kansa sana’ar idan ba ka da iliminta to, gaskiya ba ka shirya yin ta ba. Don haka ilimi ginshiƙi ne na zamantakewar rayuwa. Ita kuma sana’ar maganin duk wani hali na rayuwa ne, da inganta harkokin yau da kullum, da kuma samun rufin asiri.
Gaya mana wata karin magana da take ƙara miki ƙwarin gwiwa a rayuwarki?
Duk macen da ba ta sana’a aura ce. Lallai sana’a tana maganin duk wani ƙalubale na rayuwa.
Na gode.
Masha Allah. Ni ma ina godiya.
