Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da shirin Tarayyar Turai na kuɗin Dalar Amurka miliyan 5.1 domin kawo ƙarshen rikici, daƙile fitintunu, da kuma dawo da zaman lafiya a jihohin Katsina da Zamfara.
Za’a shafe watanni 18 ana aiwatar da shirin wanda ƙananan hukumomi 10 da ke jihar za su amfana.
Shirin zai mayar da hankali kan zaman lafiya, farfaɗo da tattalin arziki da kuma ƙarfafa shugabanci.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana shirin a matsayin mataki na sauya al’umma daga “ƙangin rayuwa zuwa farfaɗo da hidimar yau da kullum,samar da tsaro, tare da ƙarfafa mata, matasa da marasa galihu.
Jakadan Tarayyar Turai a Najeriya, H.E. Grantier Migrot, ya jaddada goyon bayan EU ga gwamnatin Jihar Katsina, yana mai cewa shirin zai karkata ne kan fagen ilimi, rage talauci, makamashi na zamani da kiyaye muhalli.
Ya ƙara da cewa za a baiwa masu gudun hijira da sauran al’umma horon na koyon sana’o’i, noma mai amfani da fasahar zamani, damar zuwa kasuwa,kai wa da komowa tare da kafa tsarin zaman lafiya a ƙauyuka da aiwatar da ayyuka aƙalla 20 masu tasiri.
Aƙalla kashi 60 bisa 100 wanda za su ci gajiyar shirin matasa ne, wanda za’ayi haɗin guiwa da IOM, CDD da Mercy Corps.
