Akwai iyaye da dama da ba su san wa ‘yarsu ta aura ba – Aisha Gambo

Spread the love

 “Yanayin yadda ake neman aure a da kan taka rawa a ingancinsa” 

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barka da war haka, barkan mu da sake kasancewa a shafin Gimbiya na jaridarku mai farin jini, Manhaja.

Kamar yadda ku ka sani, shafin namu bai tsaya a iya tattaunawa da mata kan sana’oinsu ko ayyukansu ko kuma ƙalubalen da suke fuskatan a rayuwa ba. Shafin kan yi duba kan darrusan da ke buƙatar tattaunawa, don wayar da kan al’umma.

A wannan makon, za mu tattauna kan lamarin da ya shafi neman aure, wanda da yawa kan ce yana da bambanci da na shekarun baya, tun daga neman har zuwa ga ɗaurin aure.

A shekaru da dama da suka shuɗe, neman aure ya kasance mai sauƙi kuma ana yin sa cikin jin daɗi da kuma kwanciyar hankali.

Kamar yadda na ji wasu magabata na magana, aure a da yana tattare ne da karamci da kuma girmamawa, wannnan ne ya sa a yayin neman aure, mutuncin gida ake dubawa ba yawan arziki ba ko kyau.

Binciken da wasu suka yi a baya, ya nuna yadda neman aure a wannan zamani ke zama ƙashin bayan yawaitar lalacewar aure a wannan zamani. Yayin da suke ganin cewa, matuƙar iyaye ba su kawar da wasu bidi’oin da aka ƙirƙira ba tun daga farkon haɗuwar saurayi da budurwa ba, to danasani da dama za su yawaita.

Idan muka ɗauki zuwa zance a misali, iyayen da suka ce ba a zuwa zance wurin ‘ya’yansu mata, sai ka ga ana kallonsu a matsayin waɗanda ke yin abinda ba daidai ba, a cewarsu ta ya yaran za su fahimci juna idan ba sa haɗuwa su na hira.

Da farko dai ni ba na ce kada a yi hirar ba, sai dai inda matsalar take yadda ake hirar. An kai lalacewar da iyaye za su bar samarin ‘ya’yansu mata wucewa har ɗakinsu, su yi hira da ‘ya’yansu, su kuma su koma falo, ko wani ɗakin.

Wasu ma maƙwabta suke shiga idan gidan ba mai girma ba ne, wai saurayin ɗiyarsu ne ya zo. Ko muka a bar su a falo, ba tare da kowa na wucewa ta wurin ba, tsayin awanni. A nan ya ku ke tunanin shaiɗan ba zai gwada sa’arshi ba.

Ko a da, akwai iyayen da ke barin ‘ya’yansu fita hira, amma daga cikin sharaɗin, za su zauna a inda akwai haske, kuma wurin da idan ka gitta za ka iya ganin su, ko kuma a haɗa yarinyar da ƙanenta ko ƙwanwarta da ba ta isa fahimtar maganganu ba, amma duk abinda aka yi tana da bakin da za ta iya faɗar yadda abin ya faru.

A nan hikimar da ke ciki ita ce, ba ta yadda ɓarna za ta iya shiga tsakaninsu.

Idan mun karkata akalar kan yanayin matsin tattalin arziki da muke fama da shi a wannan ƙarni, inda za ka tarar kaso mai yawa na mutanen ƙasar nan cin abinci sau uku a rana ya zama barazana a tattare da su, kuma su ɗin ne suke matsa lamba kan raya al’adun neman aure da ke wahalar da su.

Mu ɗauki wani labari da can watannin baya Manhaja ta ruwaito, inda aka zo neman aure a Jihar Sakkwato, abinda suke cewa ‘I see, I loɓe’, wato dai baiko a taƙaice. Shi wanda ke son yarinyar ko taku ɗaya ba shi da shi na wurin ajiye yarinyar, baya ga haka, babu wani shiri da yake da shi a ƙasa, ita ma a ɓangaren iyayen yarinyar, duk da hakan sai aka nemi a yi masu baiko, a saka sadaki, duk lokacin da Allah Ya yassare masa sai a yi auren, wannan kuma ba laifi ba ne. Inda matsalar take, cewa sai an yi irin babbar bidi’ar da a ke yi a irin wannan rana.

Ga waɗanda ba su san wannan al’ada ta Sakkwatawa ba, irin wannan rana tamkar ranar aure take, duk wata hidima da ku ka san ana yi wa biki ita ma ana mata daidai gwargwado. Tun daga tara taro, abincin kece reni, da kuma kayan abinci da ake yi kala-kala wanda za a ba wa dangin miji a matsayin garar ranar. Su kuwa za su siyo lemu mai yawa, alawa, biskit da sauransu su kawo, wanda shi ɗin ne za a raba wa dangi da abokan arziki na cewa an yi wa yarinyar baiko.

A irin wannan kawai, ba ƙaramin kuɗi ake kashewa ba, wanda a nan kawai mai ƙaramin hali zai iya zube rabin tanadinshi na auren.

To a cikin wannan yanayin aka shirya wannan taron, uwar amarya daƙyar ta haɗo abinda aka shirya abinda za a ba ɓanagren masu neman, wanda za a iya cewa har da bashi. Shi ma a nasa ɓangaren haka aka yi, da kama-kama aka haɗa na alawa, don haka aka juya kan yadda za a samu sadaki, don  bai kamata a je wurin tunda an tara jama’a a yanka sadaki a kasa zube shi a take kowa ya gani ba, a cewar su za a ji kunya. Saidai mijin ba shi da komai da ma za a iya kai jingina a karɓo sadakin, don haka aka yanke shawarar a yi hayar kuɗin, idan an je an nuna kowa ya gani, sai su nemi a ba su kayansu, idan ya samu gaba sai ya kawo. Haka kuwa aka yi, saidai aka samu tangarɗa yayin da suka nemi dangin amaryar su mayar da kuɗin.

Kunga anan duk mai ya yi zafi, zai fa a iya zuwa da waliyanshi biyu zuwa uku, su tsaya a ƙofar gidansu tare da waliyanta biyu ko uku a nemi auren kuma a yanka sadaki, ayi addu’a, kowa ya koma gidansa ya ci abinci. Kuma biɗar ta yi, kuma shi ranar da duk ya samu na kansa sai ya zo ya kowo sadaki, a sa ranar ɗaura aure. Ita kuma uwar ɗiya ta huta da cin bashi, kuma ɗan abinda ta kashe sai ta fara yi wa ‘yar tata tanadin auren da shi.

Sau da yawa ire-iren waɗannan bidi’oin kan sa miji fara jin yarinyar ta fita kansa tun ba a kai ta ba, wanda hakan zai iya sa ba jimawa da kawo ta faɗa ya fara ɓulla. 

Kada na cikaku da zance, kamar yadda muka saba, a duk lokacin da za mu yi irin wannan tattaunawa, mukan gayyato wata da muke tunanin za ta bada gudunmuw wurin kai saƙon yadda ake buƙata. A wannan makon ma, mun gayyato ɗaya daga cikin mata da suka ga jiya da yau, ƙwararriyar ma’aikaciyar jarida, kuma mai ba wa mata shawarwari kan zamantakewa, kuma shugaba a ƙungiyar Mata Masu Sana’o’in Hannu ta Jihar Kaduna, sannan kuma uwa ce, Hajiya Aisha Gambo, inda muka soma da yi mata tambayoyi kamar haka;

MANHAJA: Ko akwai bambanci a yadda ake neman aure a da da kuma yanzu?

HAJIYA AISHA: Assalamu alaikum. A gaskiya wannan tambaya ta ki, akwai bambanci tabbas. Duk wanda ya haura shekara 40 a misali, zuwa 50, 60 haka, ya san cewa, auren da ake nema a yanzu da na da akwai bambanci sosai ma ba kaɗan ba. 

Idan ki ka dubi ma a da, idan kaga yarinya kana so, kafin ma ka tunkare ta, sai ka fara sanar da iyayenka, kaga wata yarinya ‘yar gidan wane ce. Sannan iyayen naka su je su samu iyayenta, ‘ɗanmu ya ga ‘yar ku, ya ce, yana son ta, amma ba mu sani ba ko tana da wani manemi, ko kun bada ita. Idan ba ku bada ita ba, muna neman izinin ku, ɗanmu ya neme ta.’ To kinga tun daga farko kenan, an fara ne da haɗa gemu da gemu. Idan ba wanda ke nementa za su amince masa ya je ya nemi soyayyarta. Idan da wanda ke nemanta ko an bada ita, a nan zai ji, sai maganar ta kai ƙarshe.

To amma a yanzu fa, da rana tsaka idan wani ya ga yarinya, zai mata magana ya ce, yana son ta, su fara soyayya. Tana da wani tsayayye, an bada ita duk bai sani ba. Sai zance ya yi nisa a zo ana ta artabu da yarinya, wataƙila iyaye ma sun karɓi kuɗin gaisuwa na wani, ta dawo ta ce ta fasa wannan take so. Kinga ko akwai bambanci tun daga fara neman auren ma na da da na yanzu akwai bambanci.

MANHAJA: Za mu so jin wasu ɗabi’u na neman aure da ki ka sani, waɗanda ba a yi a yanzu.

HAJIYA AISHA: To ɗabi’u na neman aure da ake yi a da waɗanda ba a yi a yanzu suna da yawa.

Kamar dai misalin da na baki a baya, shi ma ai yanzu ba a yin shi. Abu na biyu, wanda zai nemi ‘yarka, za ka san shi sosai, kasan inda ya fito, don haka idan har aka ba wa wani izini, to iyayen ba za su sake ba wa wani izini ba, har sai an tabbatar da inda aka dosa, idan ba shi ba ne ya zo ya ce ya fasa. Kinga ko yanzu ba a hakan. Yanzu wanda yake neman ‘yarka ma ba ka san shi ba. Saurayi ne ya ga yarinya a hanya, ya ce yana son ta, ya tsire soyayya da ita. Garare-garare ana ta taɗi. Iyaye za su ce ki ce ya turo iyayenshi, don wataƙila ma mahaifinki bai san shi ba, zai ma iya haɗuwa da shi a hanya bai gane shi ba. Wanda zamanin da ba a haka.

Sannan a zamanin da, kinga wannan gaisuwar da ake yi ta ‘na gani, ina so’, da gaisuwar iyaye, duk wani abu ne mai muhimmanci da aka bar shi. To gaskiya akwai bambanci sosai. Wani ma za ki ga a yanzu waɗanda ma zai turo su nema masa auren, waliyansa, ba ma ‘yan uwansa ba ne, kuma a yi ɗin, saboda sake na rashin yin bincike ƙwaƙwara.

MANHAJA: Ko yanayin yadda aka yi neman aure na taka rawa wurin ingancin aure ko akasin haka?

Hajiya AISHA: A’a. A gaskiya yanayin yadda ake neman aure a yanzu bai taka rawa a ingancin aure. Yanayin aure na da shi ke taka rawa wurin ingancin aure. Saboda shi ɗin ne ake wa fandeshon (foundation) mai inganci, yanzu kuma ba fandashon mai kyau. Wallahi a yanzu haka akwai iyaye da dama da ba su san surukansu ba. Wasu kuma ‘yan uwanta na jini ba su san mijin ‘yarta ba. Saboda me, saboda kawai an sakarwa ‘ya zaɓi, idan ta gama sanin sa, suka daidaita kansu, sai kawai a ce a zo a yi aure.

Idan ki ka koma kan yadda ake bikin aure a da, akwai kunya. Idan an fara bikin ma iyayenta ma kunyarsu take ji, mutane da yawa ba za su ganta ba, hatta mijin ma ba zai ganta a lokacin ba. To yanzu fa, ya ake bikin. Za ki ga an kama hall, ga ango, ga amarya, ga iyayen ango ga na amarya, an cuɗe, ana ta rawa, wai wayewa.

Idan zan haɗe dukka tambayoyin naki wuri guda, zan ce, bambanci da ingancin aure na da da na yanzu yana da bambanci, domin ba a yi masa gini mai inganci kamar yadda ake yi wa na yanzu, ba a haɗa gemu da gemu yayin neman aure. A da gemu da gemu za su haɗu wurin sau uku kafin aure, za su nema, za su kawo kuɗin gaisuwa, za su zo kawo sadaki, kafin a zo ɗaurin aure. Kinga an san juna sosai, an san duk abinda ake son sani kafin a bayar da aure. Idan suruki zai haɗu da surukinsa Masallaci, za su yi gaisuwar sani sosai.

MANHAJA: Daga ƙarshe muna masu kira da babbar murya zuwa ga iyaye, su nemi albarkar aure ba yawan bidi’oin da za a yi ba. Sauƙaƙa auren ‘ya ba yana nufin zubar mata da ƙima ba, ba kuma yana nufin kun bayar da ita a arha ba. Yana nufin kun san mutuncin kanku, yana nufin kun san ma’anar aure, kun kuma nemi albarkarsa daga wurin Allah.

By ukarofi