Kamfanonin DisCos na barazanar rufewa kan yawan bashi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kamfanonin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa (GenCos) sun koka game da ƙamarin rashin wadataccen kuɗaɗen gudanarwa, lamarin da ka iya haifar da lalacewar rumbun lantarki na ƙasa saboda bashin sama Naira tiriliyan 5.2 da suke bi.

A sanarwar da Shugabar ƙungiyar kamfanonin (APGC), Dakta Joy Ogaji ta fitar a ranar Litinin, ta ce GenCos daga yanzu ba za su cigaba da dogaro akan kishin ƙasa ba wajen gudanar da tashoshin raba lantarki a Nijeriya.

Ta ce, sun yi haka na tsawon shekaru, amma hakan kaɗai ba zai wadatar wajen cigaba da gudanar da su ba, inda a cewarta ka iya haddasa rashin wuta matuƙar ba a ɗauki matakin gaggawa a kai ba.

Dakta Joy ta bayyana cewa, akwai tsohon bashin da suke bi tun daga shekarar 2015 da adadinsa ya kai tiriliyan N1.9, sai na takardun wasu kuɗaɗe a 2024 – kimanin tiriliyan N2.

Haka kuma, akwai tiriliyan N1.2 na wuta da suka raba a zangon farko na shekarar 2025, wanda ya kai jimillar kuɗaɗen zuwa sama da tiriliyan N5.2.

Dakatar ta ƙara da cewa, adadin kasafin kuɗin wutar lantarki da aka ware daga kasafin tarayya na 2025 shi ne Naira biliyan 900, wanda ko da kaso ɗaya bisa uku bai kai ba daga bashin nasu.

Ƙungiyar kamfanonin ta kuma soki ragin kuɗin wuta da Hukumar kula da Harkokin Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta yi daga N209 ga kowane kWh zuwa N160 ga kwastomomin farko na ‘Band A’, wanda zai fara aiki daga ranar ɗaya ga watan Agusta, lamarin da ta ce zai ƙara danƙwafar da su ta fuskar ƙarfin kuɗaɗe.

Da ya ke tsokaci game da batun, Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ta ofishin mataimakinsa kan yaɗa labarai, Bolaji Tunji, ya ce suna sane da halin takunkumin kuɗaɗe da kamfanonin suke fuskanta kuma gwamnati tana aiki tuƙuru wajen ganin ta warware matsalolin bashin.

Saidai, bai bayyana takamaiman lokacin da za a biya su ba.

Wannan ba shi ne karo na farko da kamfanonin ke miƙa ƙorafi ko kokawa akan al’amarin ba.

By Babaji