
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙalubalanci Ministan Abuja Nyesom Wike da ya bayyana ainihin alƙiblarsa ta siyasa kan shigarsa cikin tafiyar Rainbow Coalition gabanin zaɓen 2027.
Wike, wanda ɗan jam’iyyar PDP ne, ya kasance yana danganta kansa da Rainbow Coalition, tafiyar siyasar da ke ƙoƙarin tara wa Shugaba Bola Tinubu mutane domin sake zaɓar sa a 2027. Saidai wannana ci-gaba ya janyo adawa daga ɓangaren gwamnonin APC, waɗanda suka ce suna da manufar goya wa Tinubu da sauran ‘yan takarar APC baya yayin zaɓen a yayin da Wiken ya taƙaitu akan mara Shugaba Tinubu baya kaɗai.
A wata hira da gidan talabijin na Channels kan taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 da ke gudana a New York, Gwamna Lawal ya ce ba zai yiwu Wike ya kasance mai goyon bayan APC da wasu jam’iyyu ba a lokaci guda, yana mai cewa wajibi ne ya zaɓi tafiyar siyasarsa guda. “Saƙonmu a fili yake, ka zama a waje guda, ba zai yiwu kana ɓangarori biyu ba. Idan a APC ka ke, ka fito ka goyi bayan APCn, ba wai kana goyon bayan APC a nan kuma kana goyon bayan wasu jam’iyyun siyasa a wani waje ba,” inji shi.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnonin APC ba za su sauya matsayarsu ba duk da Wike na cigaba da bayar da kariya ga Rainbow Coalition da goyon bayan sake zaɓar Tinubu. Ya ƙara da cewa, a matsayinsu na gwamnonin APC, suna nan akan bakarsu ta a zaɓi jam’iyyar daga sama har ƙasa, yana mai cewa Wike na da ‘yancin faɗar abin da yake so.
Kazalika, gwamnan ya ce zai tattauna da Shugaba Bola Tinubu a sa’ilin da ya dawo daga hutunsa a Faransa akan matsayar siyasar ministan Abujan.
Waɗannan kalamai dai suna zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Gwamnonin APC (PGF) ta yi watsi da wasu haɗaka da shirye-shiryen siyasa da suke ganin ka iya haifar wa jam’iyyar da ‘yan takararta koma-baya a zaɓen 2027. Ta ce, mambobinta za su goyi bayan Tinubu da kuma sauran ‘yan takarar da suke ƙarƙashin inuwar APC a babban zaɓen da ke cigaba da ƙaratowa.
