Da Ɗumi-Ɗumi: PDP ta tantance Pantami da wasu biyu yayin da ta shirya sabon zaɓen fidda gwani a Gombe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe, ta sanar da tantance Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, Khamisu Ahmed Mailantarki da Usman Aliyu Garry domin shiga sabon zaɓen fidda gwanin ɗan takarar gwamnan jihar da ta sake shiryawa.

A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa labaran jam’iyyar, Abdulƙadir Ahmed Dukku ya fitar a ranar Juma’a, ya ce an tantance ‘yan takara ukun ne domin gwabzawa a zaɓen fidda gwanin da aka sake shiryawa a karo na biyu. Ya ce, hakan ya biyo bayan hukuncin wata kotu ne na soke takarar Pantami a jiya Alhamis.

Akan hakane jam’iyyar ta sake sake shirya sabon zaɓe, wanda za a gudanar a ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026. Ta yi kira ga dukkan masu zaɓe da suka cancanta daga gundumominsu da su fito domin zaɓar ɗan takarar da suke so ya wakilci jam’iyyar a zaɓen na 2027 da ke tafe.

A wata sanarwa daban, jam’iyyar ta ce ta karɓi hukuncin kotun hannu biyu-biyu tare da girmama matakin da ta ɗauka kan al’amarin. Haka kuma tana maraba da sashin hukuncin da ya amince da sahihancin shiga da zama mamban jam’iyyar na Farfesa Pantami da kuma shigarsa takara a zaɓen fidda gwani da aka yi a Mayu, 2026.

Sakataren ya kuma shawarci mambobin jam’iyyar da su ƙaurace wa jita-jita da kalaman ɓatanci da ka iya tayar da zaune-tsaye acikin al’umma, yana mai tabbatar musu da cewa jam’iyyar za ta bi dukkan matakan da suka dace wajen bayar da kariya ga muradunta da dimukraɗiyya a matakin cikin gida.

A ranar Alhamis ne dai wata Babbar Kotun Tarayya a Gombe ta yanke hukuncin soke zaɓen fidda gwanin ɗan takarar gwamna da PDP ta gudanar da fari tare da umartar ta sake wani zaɓe acikin wata guda.

By Babaji

Leave a Reply