Raɗɗa ya jaddada aniyarsa ta inganta tsaro yayin da Jihar Katsina ta cika shekaru 39 da kafuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya sake tabbatar da aniyarsa ta gina jiha mai tsaro da wadatar tattalin arziki, ta hanyar ci gaba da zuba jari a fannonin tsaro, wutan lantarki, noma, ilimi, kiwon lafiya da kuma damammakin bunƙasa tattalin arziki.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana hakan ne a yayin taron cin abincin dare da ba da lambobin girma na cika shekaru 39 da ƙirƙirar Jihar Katsina, inda mataimakinsa, Malam Faruk Lawal Joɓe, ya wakilta.

Gwamnan ya ce wannan ranar tunawa tana ba da damar yin bincike kan tafiyar da jihar ta yi tun bayan ƙirƙirar ta shekarar 1987, tare da cigaban da gwamnati mai ci yanzu ke samu.

A fannin noma, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnati ta sayo tare da rarraba taraktoci 400 a faɗin ƙaramar hukuma 34 na jihar, tare da injunan girbi na zamani (combine harvesters) guda 10, injunan noma na hannu (power tillers) 4,000 da kuma injunan shuka 2,000. Ya ƙara da cewa gwamnatin tana gudanar da aikin samar da ma’alluran ban-ruwa 3,000, inda aka tsara guda 1,000 ga kowace shiyyar sanata.

Ya ce haka zalika, gwamnatin ta gudanar da manyan ayyukan gina hanyoyi da gyaran birane a fadin jihar. Waɗannan sun haɗa da kammalawa da gudanar da ayyukan hanyoyi biyu-biyu a Katsina, Funtua, Daura, Malumfashi, Mashi da sauran al’ummomi.

A kan tsaro, Gwamna Raɗɗa ya ce aƙalla jami’an tsaro na sa-kai na Community Watch Corps 3,000 aka ɗauka aiki, tare da ‘yan banga 1,500 da sauran gine-ginen tallafin tsaro na al’umma. Ya ƙara da cewa gwamnatin tana samar da tallafin lafiya, kuɗi da na dogaro da kai ga waɗanda ‘yan bindiga suka shafa da iyalan da aka raba da muhallansu.

Haka kuma Gwamnan ya fito da tallafin tattalin arziki na gwamnatin. Ya ce sama da ƙananan da matsakaitan sana’o’i (SMEs) 5,000 ne suka samu rancen biliyan ₦2.5 ta hanyar hukumar bunƙasa sana’o’i ta jihar (SEDA), wanda ya taimaka wajen samar da ayyukan yi 15,000, yayin da mata 14,450 suka samu kayan fara sana’o’i na ƙananan sana’o’i na darajarsu ta fice miliyan ₦700.

A fannin ilimi, Gwamna Raɗɗa ya ce an gina makarantun sakandare 152 ƙarkashin shirin AGILE, aka kafa makarantu na zamani guda uku, aka kuma gina da gyara azuzuwa 3,090. Ya ƙara da cewa malamai 20,000 suka samu kwamfyutocin hannu (tablets) da horaswa kan na’urorin zamani, yayin da ɗalibai sama da 2,000 suka amfana da horaswar fasahar hannu.

A fannin kiwon lafiya, an inganta cibiyoyin lafiya guda shida zuwa manyan asibitoci(General Hospitals), yayin da cibiyoyin lafiya na farko 271 daga cikin 361 na jihar aka inganta tare da sanya musu kayan aiki. Gwamnatin kuma ta ɗauki ma’aikatan lafiya 808 ƙarƙashin hukumar gudanar da ayyukan lafiya da kuma ma’aikata 1,020 ƙarkashin hukumar kiwon lafiya matakin farko.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa ta biya sama da bilyan ₦45 na kuɗin sallama (gratuities) ga ‘yan fensho a matakin jiha da na ƙaramar hukuma, yayin da take gudanar da biyan albashi da fensho a kai a kai.

Ya amince cewa rashin tsaro, rashin aikin yi da kuma canjin yanayi sun kasance ƙalubale, amma ya ce gwamnatin za ta ci gaba da maida hankali kan tsarin ci gaba.

Yayin da yake gabatar da tsokacinsa, tsohon Sanata kuma Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim M. Ida, ya ja hankalin baƙi kan tarihin Jihar Katsina, tun daga fafutukar ƙirƙirar ta har zuwa aikin gina sabuwar jiha bayan Satumba 23, 1987.

Sanata Ida, wanda ya yi aiki a matsayin Kwamishinan kudi bayan kusan shekaru biyu da ƙirƙirar jihar, ya tunatar da cewa Katsina ta fara ne da ƙaramar hukuma bakwai, ƙarancin kuɗi da kuma tsarin gwamnati mai sauƙi. Ya bayyana cewa farkon gwamnatin ta dogara ne kan yin amfani da kuɗi cikin hikima da tarbiyya wajen kafa gine-gine na muhimmanci, ciki har da faɗaɗa Dam ɗin Ajiwa, Hedkwatar ‘Yan Sanda, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC), Kotun Koli, Filin Wasa na Karkanda da kuma Gidan Radio.

By ukarofi

Leave a Reply