Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci rundunar ’yan sandan Nijeriya da ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin ƙwarewa da rashin nuna son kai, musamman yayin da ake shirin babban zaɓen ƙasa na shekarar 2027.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a taron shekara ta 2026 da kuma taron nazari na manyan jami’an ’yan sanda da aka gudanar a Owerri, Jihar Imo, inda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya wakilce shi wajen gabatar da jawabin.
Taken taron shi ne “Samar da Tsarin Aiki na Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya Domin Ingantaccen Gudanar da Tsaro a Lokutan Zaɓe”, inda aka mayar da hankali kan ƙarfafa shirin rundunar domin tunkarar ƙalubalen tsaron da ka iya tasowa yayin zaɓen 2027.
Tinubu ya ce bai kamata a riƙa kallon ’yan sanda a matsayin masu yi wa wata jam’iyya ko wata ƙungiyar siyasa hidima ba, yana mai jaddada cewa ya kamata duk wani ɗan Nijeriya, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa, ƙabila, addini, matsayi ko wurin da yake zaune ba, ya ji cewa rundunar ’yan sanda na kare shi.
“Inji Tinubu, ‘Ya kamata a ga ’yan sanda ba a matsayin wata kafa ta biyan bukatun siyasa ba, amma a matsayin wata hukuma ta ƙasa da ke yi wa al’ummar Nijeriya hidima tare da kare tsarin mulkin ƙasar.’”
Da yake magana kan taken taron, Shugaban ƙasar ya ce zaɓen 2027 zai buƙaci shiri mai kyau, ƙwarewa, rashin nuna son kai, amfani da bayanan sirri wajen gudanar da ayyukan tsaro da kuma kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da na zaɓe.
A cewar wata sanarwa da mai ba Sakataren Gwamnatin Tarayya shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Mista Yomi Odunuga, ya fitar, Tinubu ya tabbatar wa rundunar ’yan sanda cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ba ta goyon baya domin ƙarfafa ƙarfin aikinta da kuma aiwatar da sauye-sauyen da ake yi a rundunar.
Ya ce tsaron zaɓe bai tsaya kawai kan kare rumfunan zaɓe da kayan zaɓe ba, domin ya ƙunshi kare rayuka da dukiyoyin jama’a da jami’an zaɓe, tabbatar da zaman lafiya yayin yakin neman zaɓe, hana tashin hankali da tsoratarwa, da kuma samar da yanayin da ’yan Nijeriya za su iya shiga harkokin zaɓe ba tare da fargaba ba.
Shugaban ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen yin gyare-gyare a rundunar ’yan sanda, yana mai cewa samun sauyi mai ɗorewa zai buƙaci ci gaba da zuba jari wajen ma’aikata, horaswa, fasahar zamani, kayan aikin tattara bayanan sirri, kayan aiki, walwala da tsarin gudanar da hukumomin rundunar.
Ya kuma buƙaci ’yan sandan da su ƙara ƙarfafa tattara bayanan sirri, inganta saurin kai ɗauki, ƙara hulɗa da al’umma, yin amfani da fasahar zamani yadda ya kamata da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin tunkarar sabbin barazanar tsaro.
Tinubu ya yabawa Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, da tawagar gudanarwar rundunar bisa ƙoƙarin da suke yi na sake fasalin rundunar da kuma tunkarar matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.
Ya kuma amince da irin sadaukarwar da jami’an ’yan sanda ke yi wajen yaƙi da satar mutane, ta’addanci, ’yan bindiga, fashi da makami, ƙungiyoyin asiri da sauran laifukan tashin hankali, ciki har da jami’an da suka rasa rayukansu yayin gudanar da ayyukansu.
Shugaban ƙasar ya buƙaci manyan jami’an rundunar da su ci gaba da ƙoƙarin dawo da amincewar jama’a ta hanyar bin doka da oda, ɗaukar alhaki, ƙwarewa da kuma mutunta haƙƙoƙin ɗan Adam da mutuncin ’yan ƙasa.
Ya kuma ɗora wa mahalarta taron alhakin samar da wani tsari mai amfani kuma za a iya aiwatar da shi, wanda zai ƙarfafa tsaron zaɓe da kuma shirin rundunar gabanin zaɓen 2027.
Ya ce hakan zai taimaka wajen aza tubalin samar da rundunar ’yan sanda ta zamani, ƙwararriya, mai amfani da fasahar zamani, mai dogaro da bayanan sirri wajen gudanar da ayyukanta, kuma mai mayar da hankali kan bukatun ɗan ƙasa.
Tun da farko, Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta bayyana cewa taron na 2026 zai haɗa manyan jami’an ’yan sanda, masana harkokin aikin ’yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki domin duba sabbin ƙalubalen tsaro da suka shafi zaɓe da kuma samar da dabarun da za su taimaka wajen gudanar da zaɓe cikin aminci, zaman lafiya da sahihanci.
Rundunar ta ce tattaunawar za ta kuma mayar da hankali kan amfani da bayanan sirri wajen aikin ’yan sanda, haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda da al’umma, fasahohin zamani na dijital da kuma amfani da basirar na’ura mai kwakwalwa (AI).
Tinubu ya sake tabbatar wa jami’ai da sauran ma’aikatan rundunar cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ba su goyon baya, yayin da ya buƙace su da su mayar da martani ta hanyar nuna jarumta, gaskiya, ladabi da ƙwarewa wajen gudanar da nauyin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ɗora musu.
