Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Sheikh Ra’is Sodangi, Babban Limamin Masallacin Gidauniyar Musulmi da ke Gusau, Jihar Zamfara, ya yi gargaɗi ga Musulmi game da rashin aminci, ƙarya da cin amana, yana mai cewa munanan halayen na iya lalata zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’umma.
Limamin ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a yayin da yake gabatar da huɗubar Juma’a a masallaci.
A cewar Sheikh Sodangi, al’umma da aka gina bisa yaudara da cin amana ba za ta iya tsayawa da kanta ba, yana mai jaddada cewa Musulunci yana ba da fifiko ga gaskiya da riƙe amana.
Ya ce Annabi Muhammad (Sallal Lahu Alaihi Wa Sallam) ya haramta cin amana da rashin gaskiya a tsakanin Musulmai.
Ya yi kira ga musulmai da su riƙe kyawawan halaye na aminci a duk mu’amalarsu.
“Rashin riƙon amana, ƙarya da gulma a tsakanin al’ummar Musulmi na iya lalata zamantakewar al’umma.” Ya ce
Babban limamin ya lura cewa idan aka bari ƙarya da yaudarar da cin amanar juna suka cigaba da bunƙasa a rayuwar yau da kullum, a hankali suna lalata ɗabi’u kuma daga ƙarshe suna haifar da rugujewar jituwa a cikin al’umma.
Saboda haka, ya yi kira ga Musulmai da su kasance masu aminci a tsakaninsu kuma su guji duk wani nau’in cin amana, gami da ɓata sunan wasu don neman abin duniya.
Sheikh Sodangi ya ƙara gargaɗin al’umma da su kiyaye harsunansu kuma su guji faɗin kalamai masu iya ɓata mutuncin mutane ko ƙungiyoyi, musamman don samun amfanin abin duniya.
Ya jaddada cewa ya zama dole al’umma su girmama amana, su riƙe gaskiya, kuma su guji duk wani aiki da ke ɓata mutuncin ‘yan’uwa Musulmi.
