Yanzu-yanzu: Jami’an tsaro sun hana Sanata Natasha shiga majalisa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Talata ne jami’an tsaro a Majalisar Dokoki ta Ƙasa suka hana Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan shiga zauren majalisar duk hukuncin kotu na dawo da ita bakin aiki.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sanatar ta isa majalisar ne da nufin koma wa aiki, bayan wata babbar kotun tarayya ta umarci Majalisar da ta ɗage dakatarwar da ta yi mata na watanni shida.

Duk da cewa ta ci alwashin komawa a yau, jami’an tsaro sun ki amince mata shiga ciki, a lokacin da ta ke ƙoƙarin shiga tare da mai fafutukar ƴancin al’umma, Aisha Yusufu, wadda ita ma aka hana ta shiga.

Lamarin da ya sa ta fito daga motar da zo aciki, inda ta yi tattaki da ƙafa zuwa cikin majalisar.

Saidai, babu masaniya game da ko ta samu shiga ko kuma hakan bai yiwu ba a lokacin haɗa rahoton.

By Babaji