
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Wakilai ta ɗauki matakin daƙile amfani da cibiyoyin kuɗi yayin da a ranar Talata ƴaƴanta suka yi karatun farko ga ƙudirin da ke neman hana jami’an gwamnati da iyalansu amfani da makarantu da asibitocin kuɗi.
Ɗan majalisa, Hon. Amobi Ogah (mazaɓar Isuikwuato/Umonneochi a Jihar Abia) ya jagoranci gabatar da ƙudirin, inda ya ce an tsara shi ne domin tilasta wa jami’an gwamnati amfani da makaratu da asibitocin gwamnati.
Ya ce, hakan zai taimaka wajen ƙarfafa musu gwiwa da rage ɓarnartar da kuɗaɗe tare da dawo da martabar cibiyoyin ilimi da lafiya na gwamnati.
Hon. Ogah ya shaida wa manema labarai cewa makarantu da asibitocin gwamnati suna cikin mawuyacin hali a yau, lamarin da a cewarsa ya samu ne a sakamakon rashin ba su kulawa daga jami’an gwamnati.
Ya kuma ce, manyan ƴan siyasa da manyan jami’an gwamnati suna tura ƴaƴansu zuwa makarantu masu tsada a gida ko wajen Nijeriya da kuma zuwa ƙasashen wajen neman magani, yayin da suke watsi da na gwamnati, lamarin da ke taimaka wa kashe maƙudan kuɗaɗe a ɓangaren.
Haka kuma ya ƙara da cewa, a yayin da aka tilasta wa jagorori amfani da cibiyoyinsu na gida, hakan zai farkar da su wajen ɗaukar matakan gyara akansu domin amfaninsu da ɗaukacin al’umma baki ɗaya.
