Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar ƙaramar Hukumar Tarauni a Majalisar Tarayya da ke Abuja, kuma Kwamishina a wata hukuma ta gwamnatin tarayya, Hon. Hafizu Kawu Tarauni, ya bayyana cewa Sahal College of Health Science and Technology (SCOHST) da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Muhammad Alkanawi, ta taka muhimmiyar rawa wajen horar da matasa maza da mata 174 a fannin kimiyya da fasahar kiwon lafiya.
Hon. Hafizu Kawu ya bayyana cewa horar da matasan zai taimaka wajen samar da ƙwararrun ma’aikatan lafiya da za su bayar da gudunmawa wajen inganta harkokin kiwon lafiya a asibitoci da cibiyoyin lafiya na gwamnati da masu zaman kansu a Kano da Nijeriya baki ɗaya.
Hon. Hafizu, wanda Hon. Hassan Yahya Kila, ɗaya daga cikin manyan makusantansa, ya wakilta, ya ce babban burinsa shi ne ganin matasa da sauran al’umma sun samu ilimi da ci gaba a fannoni daban-daban na rayuwa.
Ya ce wannan shi ne dalilin da ya sa a lokacin da yake wakiltar al’ummar Tarauni a Majalisar Wakilai ta Abuja, ya yi ƙoƙarin kawo ayyukan ci gaba a yankin, musamman a fannonin lafiya, samar da ayyukan yi ga matasa, koyar da sana’o’i da sauran muhimman abubuwa, inda ya ce har yanzu al’ummar Tarauni na ci gaba da cin gajiyar irin waɗannan ayyuka.
Da yake jawabi tun farko, shugaban kwalejin, Ibrahim Muhammad Alkanawi, ya bayyana ranar a matsayin tarihi mai muhimmanci ga makarantar, yana mai cewa bayan kafa kwalejin shekaru kaɗan da suka gabata, an samu damar karrama dalibai 174 da suka kammala karatu.
Ya ce daliban sun samu takardun izini da shaidun karatu daga hukumomin da ke da alhakin kula da harkar ilimin da suka samu, domin su shiga cikin al’umma su bayar da gudunmawarsu a fannin kiwon lafiya.
Alkanawi ya yaba wa wasu mutane masu kishin al’umma, ciki har da Sheikh Ibrahim Khalil, saboda taimakawa wajen ɗaukar nauyin biyan kuɗin karatun dalibai, inda ya ce an samu damar biyan kuɗin karatu ga kusan kashi 50 cikin 100 na daliban.
Ya kuma yaba wa sauran masu kishin al’umma da suka taimaka wajen ganin harkar ilimin kiwon lafiya ta samu ci gaba.
A ƙarshe, ya yabawa ɗaukacin mahalarta taron, musamman shugabanni, iyaye, masana da sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci taron.
Ya kuma yaba wa waɗanda suka gabatar da jawabai, ciki har da Dakta Abdullahi Dahiru, wanda ya gabatar da takarda mai shafuka 13, inda a shafi na 12 ya bayyana muhimman abubuwa 10 da ya ce ya kamata duk wani jami’in kiwon lafiya ya sani kuma ya yi aiki da su domin samun nasara wajen hidimtawa al’umma da kare lafiyar jama’a.
Haka kuma, Dakta Yakubu Muhammad Baba, ta bakin wakilinsa a taron, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin buɗe wani sashe a kan iyakokin Nijeriya guda 145, inda za a ɗauki mutum 10 a kowace iyaka domin kula da lafiyar mutanen da ke shigowa ƙasar, da nufin hana shigowar wasu cututtuka.
Ya kuma bayyana yiwuwar kafa wata sabuwar hukuma da za ta taimaka wajen ɗaukar ma’aikatan da suka yi irin wannan karatu aiki, bisa wani sabon tsarin da ake ƙoƙarin tabbatar da shi ta hanyar doka a Nijeriya.
