
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kai wa Shugaba Bola Tinubu ziyarar ba-zata a Faɗar Shugaban Ƙasa dake Abuja.
Saidai ba a samu bayanai game da sakamakon zaman nasu ko musabbabin hakan ba.
Wannan shi ne karo na biyu da ake ganin jagororin biyu sun gana a tsakanin su a tsawon shekaru biyu tun a watan Yunin 2023 da Kwankwaso ya kai wa Tinubu ziyara a Fadar domin taya shi murna lashe zaɓe.
Masu sharhi akan harkokin zaɓe na ganin hakan a matsayin wani yunƙuri na haɗewar manyan ƴan siyasar biyu a inuwa guda a yayin tunkarar babban zaɓen 2027.
Kwankwaso mai shekaru 67, wanda shi ne ya samar da tafiyar Kwankwasiyya a siyasar Arewacin Nijeriya, ana ganin sa a matsayin ginshiƙin siyasa musamman a Arewa masu Yammacin Nijeriya.
Lamarin da ya haifar da cecekuce acikin al’umma duba da yadda raɗe-raɗin komawar Kwankwaso cikin jam’iyya mai mulki ta APC ke ƙara ƙarfi.
