“A wannan lokacin ya zama dole mata su kama sana’a”
Daga MUKHTAR YAKUBU
A yanayi na rayuwa a yanzu mata sun farka wajen neman na kansu wajen kama sana’o’i da sauran ayyuka domin samun yadda za su gudanar da rayuwarsu ba tare da sun jira a kawo musu ba.
Saddiƙa Jibrin Abdullahi wadda aka fi sani da Mama Saddiƙa tana cikin mata ‘yan kasuwa da take gudanar da harkokin kasuwanci kala-kala domin ta samu ta rufawa kanta asiri. Wani abu da ya fi burge mutane shi ne yadda ta ke gudanar da harkar kasuwancin dankalin turawa da ake ganin harka ce da maza kawai za su iya gudanar da kasuwancin, amma ita Saddiƙa Jibrin Abdullahi ta shiga harkar dosai kuma har ta kasance babbar’yar kasuwa a cikin harkar dankalin turawa.
Domin jin yadda Saddiƙa Jibrin Abdullahi take gudanar da kasuwancinta nasarori da matsalolin da ta ci karo da su, wakilinmu ya nemi jin ta bakin ta. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.
MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatun mu.
SADDIƙA JIBRIL ABDULLAHI: To assalamu alaikum, ni dai suna na Saddiƙa Jibrin Abdullahi, da nake gudanar da kasuwanci kala-kala, sai dai a yanzu an fi sani na da harkar kasuwancin dankalin turawa.
Ko ya aka yi kika samu kanki a wannan harkar kasuwancin dankalin Turawa?
To kafin wannan daman ni ‘yar kasuwa ce da na daɗe Ina harkar kasuwancin, tun lokacin Ina tare da mijina kafin Allah ya yi rabuwar mu da shi. Duk da a lokacin da nake tare da mijina babu abin da ya rage ni da shi, amma saboda na dogara da ƙafafuwana kada kullum ina cewa ya yi mini har ya gaji, don haka ban zauna zaman jira a ba ni ba. Kuma bayan mun rabu na ci gaba da yin kasuwancina, tun Ina sayar da shaddodi da kayan mata su takalma da jaka, har ma da na maza duk na dade ina yin kasuwancina ta wannan ɓangaren, kuma Ina yin amfani da soshiyal midiya ne wajen tallata kayana, kuma Alhamdulillah Ina samun kasuwa sosai.
Dama ta soshiyal midiya kika fara tallan kayan ko daga baya ne?
Gaskiya da soshiyal midiya na fara inda na fara yin kasuwancin turaruka, daga baya kuma da jarina ya yi kwari, sai na koma ina zuwa Legas na saro kaya haka ma a Kano na sara. Kuma gaskiya na ci gajiyar harkar sosai, daga baya ne da na ga abin ya yi yawa kowa ya shiga harkar kusan an yi mata yawa sai na ɗan ja baya, duk da dai ba na daina ba ne duk lokacin da ake buƙatar kaya a wajena za a samu saboda na daɗe a harkar duk mutane sun sanni.
Idan na fahimci maganar ki harkar kasuwancin kayan mata an yi mata yawa shi ya sa kika ɗan ja baya a yanzu?
Gaskiya ne an yi mata yawa, sai ya zama kasuwar ba kamar da ba, duk da dai kowa rabon sa yake ci, amma dai samun bai kai na baya ba lokacin da ba a yi yawa ba.
Kasuwancin soshiyal midiya ana ganin bai tsaya ga jarin da kake da shi ba, idan dai ka na da babbar waya za ka tallata kayan ko da ba ka da shi don haka ake ganin harka ce ta ka yi na yi.
To ni gaskiya da jarina nake kasuwancin, kuma shi harkar kasuwanci za ka iya haɗuwa da ƙalubale, amma ni a kasuwancin soshiyal midiya babu abin da zan ce sai godiyar Allah babu wani ƙalubale da zan ce na samu da ya taɓa jarina, saboda kaya ne aka saka, abin da ka gani shi za a sayar maka, kuma sai ka tura kuɗi sannan za a tura maka da kaya. Kuma babu wanda zai ce ya sayi kaya a wajena na cuce shi ko na damfare shi, ko ban tura maka da kaya ba. Don ba zai yiwu ka bani kuɗi ban tura maka da kaya ba. To ta wannan ɓangaren gaskiya ba ni da ƙorafi, sai dai ta bayan fage waɗanda ka sani masu karɓar bashi, to sun taka muhimmiyar rawa wajen karya mini jari, kuma mafi yawan su maza ne suka karya ni. A Lokacin saboda ina kawo kaya masu yawa Shaddodi da kaya na alfarma. To za ka ga wani Mutum da mutuncin sa da girman sa ya zo ya ce ba ni kaya, kana tunanin ya fi karfin abin. Amma daga baya sai a fara kai ruwa rana, har sai rai ya baci. Mutum ba wai ba shi da shi ba ne, kawai mugunta ce za ta hana ya baka kudin ka . To gaskiya wadansu ma idan ka gan su aka ce sun ci kudi sun ki biya sai ka yi mamaki. To har sai da ta kai maza masu cin bashi sai da suka karya ni. Kuma har yanzu da za a ce maza su biya ni bashin da nake bin su Ina tabbatar maka ya isa na ja wani jarin. Maza su ne suka karya ni na zamo ba ni da ƙarfin jari a yanzu, don ni a kasuwancin da nake yi a yanzu mata biyu ne nake bi bashi da suka hana ni, amma duk sauran maza ne. Kai wani ma da na yi ta bin sa ya ba ni bai bayar ba, har sai da ya mutu aka biya ni.
To a yanzu an fi sanin ki da harkar kasuwancin dankalin Turawa, kuma ana ta mamakin yadda mace take kasuwancin dankalin turawa da ake ganin kasuwancin maza ne.
To ka san shi kasuwanci buga can buga nan ne. Allah ne ya san inda dacen ka yake. Gaskiya ka san ita harkar kasuwancin dankalin turawa ta maza ce, to amma a yanzu mata ma sun shiga harkar, don ko a can garin Jos da nake sarowa ni mace ce take turo mini, ƙawata ce ‘yar Jos, idan ta tashi za a kira ta a ƙauye manoma su yi cinikin gona ta saya ta cika motoci ta fito da shi. To ita ce ta fara jawo ra’ayina , har na ji Ina da sha’awar kasuwancin dankalin turawa kuma na fara, gaskiya Alhamdulillah Ina samun kasuwa sosai sai godiyar Allah.
Duk da kin saba harkokin kasuwanci, amma dai wannan shi ne karo na farko da kika fara harkar kasuwancin dankalin turawa. Ko ya kike gudanar da kasuwancin?
To da yake ita wannan harkar ta gwari ce, don haka tana cike da ƙalubale, don ko a kwanakin baya na ɗan yi asara, to ita harkar gwari yau ne riba gobe faɗuwa. Gaskiya na samu alheri, na tallata kayana a soshiyal midiya, haka waɗansu masu kaunata sun taya ni na samu kasuwa sosai, kuma kowa ya sa yi kayana ya biya ni kamar yadda ake buƙata. Kuma akwai wani lokaci da aka kawo mini kaya mota guda, sai kafin a zo mota ta lalace a hanya har sai da aka kwana biyu da wuni direba yana daji mota ta lalace, sannan aka dakko dankali aka zo. Ko da aka zo yawanci rabi da kwata duk sun ruɓe, saboda shi dankalin Turawa ba ya son ruwa kuma ba ya son zafi, to saboda yanayin ruwa dankalin ya lalace, gaskiya na yi asara sai dai Allah ya mayar da alheri. Sai dai fa hakan bai sa na karaya ba ina nan ina ci gaba da harkar. Sai kuma ƙalubale na cinikayya, don akwai lokacin da za mu sayo dankalin a bisa farashi ya yi sama sai kuma ya yi ƙasa .
Kasancewarki tsohuwar ‘yar kasuwa, idan har mace za ta fara kasuwancin me ya kamata ta yi?
To na farko dai kada ta ce sai ta samu jari mai yawa, don ko ni da ƙaramin jari na fara harkar turare, don lokacin da dubu arba’in na fara, kuma na samu alheri sosai sai kuma na juya kan harkar kayayyakin mata da na maza , don haka ko da yaya mace ta samu kada ta ce sai ta jira ta samu kuɗi mai yawa, kuma kada ta ce za ta sa dogon buri a riba. Ko yaya kika samu, ki yi haƙuri ki ci gaba da juyawa da haka za ki jawo masu saye wata rana sai ki ga kin samu babban jari. Don haka dai mata a tashi a rungumi sana’a, don yanzu sai kina yi za a yi da ke, idan ba ki da sana’a, ko a cikin danginki ba za a yi da ke ba, haka a cikin ƙawaye da sauran jama’a, ke ko a wajen mijinki sai kin fi daraja har ma a wajen ‘yayanki. A taƙaice, a wannan zamani sana’a ta zama wajibi ga kowacce mace.
To Madalla mun gode.
Ni ma na gode sosai.
