Gwamnatin Katsina za ta ɗauki nauyin mahardata Kur’ani karatun likita

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a lokacin da yake buɗe taronta masu ruwa da tsaki don gyara tsarin ilimin almajiri da islamiyya a jihar.

Gwamna Raɗɗa ya sanar da sabbin makarantun Tsangaya guda uku da za a gina kafin ƙarshen shekara.

Ya bayyana cewa masu haddar Alkur’ani za su samu guraben karatu kan MBBS, Nursing, da sauran fannoni na ƙwarewa kan kiwon lafiya.

Masu ruwa da tsaki a wajen taron da sun bada goyon baya ga gyare-gyaren da gwamnatin jihar ta ɓullo da su don ƙarfafa ilimin addini da na zamani.

Taron da ya gudana a babban ɗakin taron na hukumar kula da ma’aikatan ƙananan hukumomi a Katsina, ya sami halartar malamai, shugabannin al’umma, malaman makaranta, wakilan ƙungiyoyin fararen hula, da masu tsara manufofin gwamnati don tsara hanyoyin magance matsalolin ilimin Alkur’ani da na islama a jihar.

An gudanar da taron ne da nufin cimma gagarumar nasara a ɓangaren gyara tsarin ilimin Almajiri da na Islamiyya.

Gwamna Raɗɗa ya jaddada aniyar gwamnatinsa na sauya tsarin ilimin Almajiri da Islamiyya, yana mai cewa yana ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da zai gaggautawa aiwatarwa a jihar.

Ya bayyana cewa kashi 90 bisa 100 na al’ummar jihar Musulmai ne, domin haka ya jaddada cewa dole ne gwamnati ta hada kai da malaman Musulunci da al’ummomi don ƙarfafa tsarin.

Gwamnan ya jaddada cewa manyan malamai ne za su jagoranci kowane mataki na tsarin gyaran. “Ba za a iya samun nasara ta haƙiƙa ba tare da goyon baya na daga malaman mu ba,” in ji Dikko Raɗɗa.

Ya sanar da kafa sabbin Makarantun Tsangaya guda uku, inda za a ƙaddamar da na farko a Katsina kafin ƙarshen shekarar nan. Waɗannan makarantu za su haɗa haddar Alkur’ani da ilimin zamani, tare da koyar da Islamiyya, Turanci, Lissafi, da koyon sana’o’i ga yara maza da mata.

Gwamna Raɗɗa ya kuma bayyana cewa “duk ɗan Jihar Katsina da ya haddace Alkur’ani mai tsarki kuma ya cika sharuɗɗan ilimi da aka gindaya, gwamnati za ta ɗauki nauyin karatunsa gaba ɗaya don yin ƙwararrun kwasa-kwasai kamar su MBBS, Nursing, da sauran fannoni makamantan su,”Inji gwamnan.

Ya ƙara da cewa za a bai wa masu haddar Alkur’ani takardun shaida da aka amince da su kuma za a ba su horo na dabarun zamani don faɗaɗa damammaki a gare su.

Gwamnan ya jaddada muhimman matakai da gwamnatinsa ta ɗauka ciki har da kafa Hukumar Kula da Zakka da Wakafi, kafa Hukumar Hisbah, da naɗa mai ba da shawara na musamman kan Tsangaya da yara marasa zuwa makaranta. Ya kuma yi bayani kan gyaran makabartun Ɗanmarna, Dan Takum, da Filin Samji a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa ɗabi’un Musulunci da rayuwar al’umma.

Gwamnan ya yabawa malaman Allo da sauran malamai, ya yi kira gare su da su goyi bayan gyare-gyare inda ya ce gwamnati kaɗai ba za ta iya magance ƙalubalen Almajiri ba sai da haɗin gwiwar al’ummomi, iyaye, da shugabannin addini.

Da yake gabatar da wata takarda mai take “Tsarin Ilimin Almajiri a Jihar Katsina: Me yasa gyare-gyare na baya suka faskara,” Farfesa Umar Alƙalin ya nazarta gazawar da aka samu a baya, yana mai ambaton raunin mallakar al’umma, rashin kulawa da jin daɗin malamai, rashin kariya ga yara, da rashin haɗin kai.

Farfesa Alƙali ya ambaci bayanai daga CPIMS (Afrilu 2022) waɗanda suka rubuta yara sama da 314,000 marasa zuwa makaranta a Katsina, ciki har da almajirai 140,495, ‘yan mata 157,884, da yara maza 203,297—adadi da ke nuna gaggawar gyaran.

Ya yaba da ƙoƙarin da al’ummar Katsina ke yi kuma ya ba da shawarar da a samar da wani tsari na kulawar iyali, kariya ga yara, horar da malamai, da samar da kayan karatu a Hausa, Larabci, da Turanci.

Tun da farko, Babban jami’in ƙididdiga na Jihar Katsina, Farfesa Saifullahi, ya yi maraba da mahalarta taron kuma ya jaddada muhimmancin ingantattun bayanai wajen tsara gyare-gyare da ya bayyana a matsayin ginshiƙai guda uku don samun nasara,
ingantaccen tattara bayanai, koyi daga tsarin da ya yi nasara, da zurfafa haɗin gwiwa tsakanin malamai, gwamnati, da ƙungiyoyin fararen hula.

Wakilin UNICEF daga Ofishin Kano, Malam Rahmah, ya yabawa Gwamna Raɗɗa kan ƙirƙiro wannan shiri kuma ya ba da tabbacin cewa UNICEF za ta cigaba da ba da goyon baya.

Ya lura cewa UNICEF ta shafe sama da shekaru biyar tana aiki tare da Katsina kan ilimin Alkur’ani da na Islamiyya.

Sauran fitattun masu magana sun hada da Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, Malam Aminu Ibrahim Daurawa, Farfesa Muhammad Mansir Sokoto, Sheikh Jabir Sani Maihula, da wakilin Sheikh Dahiru Usman Bauchi dukkansu sun yi alƙawarin goyon bayan gyare-gyaren.

Wakilan ƙungiyoyin fararen hula, ƙarƙashin jagorancin Malam Bishir Usman Ruwan Godiya, sun yaba da ƙoƙarin gwamnati kuma sun yi kira da a haɗa kan makarantun tahfiz.

Mahalarta taron sun haɗa da shugabannin makarantun tsangaya, malamai, abokan hulɗa, da sauran masu ruwa da tsaki.

By ukarofi