Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hon. Sani Aliyu Ɗanlami da ke wakilan Katsina ta tsakiya ya bayyana haka a lokacin da yake miƙa aikin asibitin ga ƴan kwamitin unguwar Makera da ke mazaɓar shikanfi (B) da ke ƙaramar hukumar katsina, bayan ya amshi aikin daga ɗan kwangilar da ya yi aikin gina asibitin.
Ɗan majalisar yace “Bayan wannan asibiti da na miƙa maku, akwai ƙarin asibitoci guda shida da za a gina a wasu unguwanni da ke cikin ƙaramar hukumar katsina don inganta harkar kiwon lafiya.
Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya ƙara da cewa” yin haka ina koyi da mai girma Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa wajen ganin al’ummar jihar , sun samu inganttatar lafiya mai ɗorewa.
Ya bayyana cewa” bada jimawa ba, za sanya ma asibitin kayyayakin aiki na zamani, bugu da ƙari za a gayyato mai girma Gwamna domin ƙaddamar da aikin asibitin.
Mutane da dama suka tofa albarkaci bakin su tare da gode ma Hon. Sani Aliyu Danlami akan wannan aikin alheri da al’ummar unguwar Makera suka daɗe suna nema.
Daga ciki akwai shugaban kwamitin unguwar Kabir Matazu, shugaban kansiloli na ƙaramar hukumar katsina Hon. Ishak Tasi’u Modoji da dai sauran su.
