Ilmi da wayar da kai su ne makamin farko wajen yaƙar cutar sanƙarar nono – Dakta Susan Love 

Spread the love

Babu kyauta mafi girma fiye da kulawa da kanki – Oprah Winfrey

Daga AISHA ASAS 

Mai karatu barkanmu da yau, barkanmu da sake kasancewa a shafin Gimbiya na wannan mako. Idan mai karatu na bibiye da mu, a makom da ya gabata, mun fara kwararro jawabi kan muhimmancin kula da lafiyar nono da kuma ma’ana tare da tasirin sa ga jikin ‘ya mace. Daga ƙarshe mun dasa aya ne akan shawarwari kan yadda za ta kula da lafiyar nononta. 

A wannan makon da yardar mai kowa mai komai, za mu so ma ne da kawo maku wasu daga cikin cututtukan nono da kuma yadda ake samun su har ma da hanyoyin neman lafiya, amma kafin nan zan so na ƙara jawo hankalin masu karatu kan cewa, lafiyar nono na da matuƙar muhimmanci ga kowace mace, ba wai don kyawu ko ado ba, har ma don lafiya da rayuwar gabaɗaya.

Ta hanyar bin shawarwarin da masana suka bayar, yin gwajin kai-da-kai, da neman kulawar likita lokaci-lokaci, za ki iya kauce wa matsaloli masu yawa.

Kada ki manta, rigakafi ya fi magani. Idan kika fara kulawa tun da wuri, nononki zai ci gaba da kasancewa cikin ƙoshin lafiya da siffa mai kyau.

Kamar yadda shahararriyar malamar ilimin nan Maya Angelou ta ce: “When you know better, you do better.” (Idan ki ka samu sani da yawa, za ki aikata ya kamata da yawa).

Mata ku kula da nononku kamar yadda kuke kula da rayuwarku.

Bari mu soma da alamomin gargaɗi, wato alamomin da za su hankaltar da ke cewa nononki na tare da matsala.

Jin ƙurji ko ƙarfi a nono ko kusa da ƙirji.

Canjin launi ko tsari a fata.

Fitar ruwa ko jini daga nono ba tare da shayarwa ba.

Jin zafi mai yawa.

Kumburi ko zafin ƙirji mai ɗorewa.

Da waɗannan alamomi ‘yar uwa za ki iya gane nononki na tare da matsala wanda ya kamata ki hanzarta kai kanki asibiti.

Idan mun fahimta, muje ga cututtukan da ke shafar nono, zuwa hanyoyin samuwarsu, alamomin su da kuma rigakafin kamuwa da su.

Nono na mace ba wai kawai cibiyar shayarwa ba ne, har ma yana iya fuskantar wasu cututtuka daban-daban waɗanda ke buƙatar kulawa ta musamman don kauce wa matsaloli masu tsanani. Wannan sashe zai yi bayani kan wasu daga cikin cututtukan da suka fi yawan damun nono, yadda ake gane su, hanyoyin magani, da matakan kariya.

1. Cutar sanƙarar nono (Breast Cancer)

Yadda take Samuwa:

Sauye-sauyen gado musamman BRCA1 da BRCA2 (genetic mutations).

Canjin tsarin hormone.

Rashin yin gwajin nono na kai-da-kai da kuma rashin kulawa.

Shan taba, rashin motsa jiki, yawaitar ƙiba, da rashin abinci mai kyau, ko in ce cin abincin da ka iya haifar da cutar.

Alamomi:

ƙurji ko kumburi a nono ko ƙasan hannu.

Canjin siffa ko launi na fata.

Zubar ruwa mai jini daga ƙashin nono.

Ciwo ko jin zafi da ba a saba ji ba.

Magani:

Yiwuwar tiyata don cire ƙwayar cutar.

Hanyar radiation therapy wato abinda muka yi wa suna gashi.

Magungunan chemotherapy (maganin kashe ƙwayoyin cutar).

Magungunan hormone therapy.

Kariya:

Yin gwajin nono na kai-da-kai.

Ziyarar likita lokaci-lokaci.

Canza salon rayuwa da cin abinci mai kyau.

Cutar sanƙarar nono (Breast Cancer) wacce WHO ta tabbatar ita ce cutar da ta fi kashe mata fiye da kowace cuta mai yaɗuwa a duniya.

Dr. Aisha Abdullahi, ƙwararriyar likitar cututtukan mata a Asibitin Koyarwa ta ABU Zaria, ta ce: “Matsalar cutar sanƙarar nono na iya shafar kowace mace, babba ko mai ƙarancin shekaru. Gano ta da wuri shi ne hanya mai muhimmanci na yaƙar ta.”

Haka zalika, Dr. Maryam Abdullahi ta bayyana sanƙarar nono a matsayin yanayin da ƙwayoyin nono ke girma ba bisa ƙa’ida ba, suna iya haifar da cuta mai tsanani.

2. Mastitis (Ciwon Nonon Shayarwa)

Yadda yake samuwa:

Cutar bacteria ta shiga nono yayin shayarwa.

Rashin fitar madara yadda ya kamata.

Alamomi:

Zafi, kumburi, ja da zafi a nono.

Zazzaɓi da jiri.

Jin ciwo yayin shayarwa.

Magani:

Antibiotics don kashe bacteria.

Shan ruwa mai yawa.

Ci gaba da shayarwa don fitar da madara.

Hutu da wanke nono da ruwan ɗumi.

Kariya:

Tsabtace nono da wanke hannaye kafin shayarwa.

Canza wurin shayarwa don kauce wa kumburi.

Dr. Fatima Usman ta bayyana mastitis a matsayin kumburi a nono da bacteria ke haifarwa, musamman ga masu shayarwa.

3. Fibrocystic Breast Changes (Canje-canje na nonon da aka fi samu)

Yadda yake samuwa:

Canje-canjen hormone musamman kafin ko lokacin al’ada.

Alamomi:

ƙurji-ƙurji masu taushi a nono.

Jin zafi kafin ko yayin al’ada.

Magani:

Sauƙaƙa ciwon da magunguna irin su paracetamol.

Rage cin caffeine.

Yin amfani da rigar nono mai goyon baya.

Kariya:

Kulawa da salon rayuwa.

Rage damuwa da motsa jiki.

Dr. Aisha Bello ta ce wannan yanayi ne na canje-canje a nono masu janyo ƙurji-ƙurji masu laushi da zafi musamman kafin al’ada.

4. Non-Cancerous Tumors (Fibroadenomas)

Yadda yake samuwa:

Haɓakar ƙwayoyin da ba cutar sanƙara ba.

Alamomi:

ƙurji mai kauri da motsi a ƙarƙashin fata.

Ba shi da zafi yawanci.

Magani:

Idan ƙurjin ba babba ba ne, ana iya barinsa a haka.

Tiyata idan yana da girma ko ya dame mace.

Kariya:

Bincike lokaci-lokaci.

Kulawa da canjin hormone.

Dr. Kabiru Usman ya bayyana fibroadenomas a matsayin ƙurji da ba su da illa, don haka ba cuta ce ba.

5. Nipple Discharge (Zubar ruwan nonon da ba na al’ada ba)

Yadda yake samuwa:

Matsaloli na ciki kamar cutar sanƙara, ko kumburin ƙwayoyin ruwa.

Alamomi:

Zubar ruwa mai launi ko jini daga ƙashin nono.

Magani:

Gwaje-gwaje don gano musabbabi.

Magani ko tiyata gwargwadon yadda likita ya nuna.

Kariya:

Kulawa da lafiya da hanzarin ɗaukar mataki.

Dr. Hadiza Ibrahim ta bayyana cewa, ba kowane zubar ruwa daga ƙashin nono ba ne yake zama alamar cutar sanƙara ba, amma yana iya zama domin shi ma yana ɗaya daga cikin alamomin cutar.

Fitacciyar likita kuma masaniyar bincike a fannin sanƙarar nono, Dr. Susan Love, ta yi rubuce-rubuce da dama kan yadda mata za su gane alamomin cutar da yadda za su kula da lafiyarsu.

Ta yi nuni da cewa: “Ilmi da wayar da kai su ne makamin farko wajen yaƙar cutar sanƙarar nono.”

Uche Jombo Jarumar Nollywood ta bayyana ta samu cutar sanƙarar nono da wuri, ta kuma yi kira ga mata su kasance masu lura da lafiyarsu.

Na san mai karatu na da tarin tambayoyi game da ciwon da muka fara ambata, wato sanƙarar nono, don haka idan ka numfasa, bari mu amsa wasu tambayoyi da muke fatan naku na daga ciki:

TAMBAYA: Shin kowane kumburi a nono cutar kansa ne?

AMSA: A’a. Amma kowanne kumburi ya kamata likita ya duba.

TAMBAYA: Zan iya yin gwajin nono a gida?

AMSA: E, amma wannan ba ya maye gurbin gwajin likita ba. Sai dai WHO ta kuma bayyana cewa, gwajin nono na kai-da-kai (self-breast eɗamination) na rage haɗarin gano cutar kansar nono a mataki mai tsanani da kashi 40%.

Kuma kashi 40% na mace-mace daga cutar kansar nono a nahiyar Afirka na faruwa ne saboda gano ta a mataki na gaba, wanda zai iya ragewa idan ana yin gwajin nono na kai-da-kai da wuri.

TAMBAYA: Idan na samu cutar a mataki na farko fa?

AMSA: Ana samun damar warkewa, inda fiye da kashi 90 bisa 100 suka warke a matakin farko.

Rahoton World Health Organization (WHO, 2024) ya nuna cewa, sama da kashi 70% na mata a duniya suna fuskantar canjin siffa ko girman nono kafin su kai shekara 50.

Kashi 16% na mata na samun matsalar nono mai alaƙa da cututtuka ko rauni kafin su kai shekaru 40.

Daga ƙarshe muna janyo hankalin mata kan kulawa da lafiyar nono, wanda ke buƙatar sanin irin cututtukan da ke iya damunsa, yadda za a gane alamominsu, da kuma matakan kariya. Yin hakan zai taimaka wajen rage damuwa da haɗarin da ke tattare da cututtukan nono, musamman sanƙarar nono, wanda ya fi shafar mata a duniya.

Nono shi ne ginshiƙin rayuwar mace, ba wai kawai wurin shayarwa ba ne, har ma cibiyar lafiyarta gaba ɗaya. Lafiyar nono na da matuƙar muhimmanci, domin rashin kulawa da shi na iya janyo cututtuka masu haɗari, ciki har da sanƙarar nono, cutar da ta zama babbar barazana ga mata a duniya. 

Nono na ɗaya daga cikin mahimman gaɓoɓin jikin mace wanda aka tsara musamman domin samar da madara ga jariri. A kimiyyar likitanci, nono na ƙunshe da ƙwayoyin glandular da ke samar da madara, da kuma ƙwayoyin connective tissue da fat tissue da ke ba shi ƙarfi da siffa.

Babban aikin nono shi ne samar da madara mai gina jiki, ta hanyar glandular tissue wanda ke samar da madara lokacin da mace ta haihu. Haka kuma, nono yana ɗauke da jijiyoyi masu yawa da ke taimaka wa wajen jin sanyi, zafi, ko wasu canje-canje a jikin mace.

By ukarofi