Cututtukan da ake jin kunyar faɗa sun fi cutarwa – Dr. Aissata Issoufou

Spread the love

Idan mace tana fama da yoyon fitsari, wajibi ne a riƙa nuna mata tausayi da taimako – Sheikh Abdullahi

Daga AISHA ASAS 

Akwai wasu matsaloli da mata ke fuskanta waɗanda ake ɗaukar su tamka a matsayin sirrin da bai dace a bayyana ba. Amma duk da haka, waɗannan matsaloli suna shafar lafiyar jiki, ta hankali, da rayuwar zamantakewa. ɗaya daga cikin su shi ne, matsalar yoyon fitsari, wato yanayi inda mace ke rasa ikon riƙe fitsari. A al’ada, mace za ta iya riƙe fitsari har sai lokacin da take so ta fitar da shi. Amma idan wannan iko ya kuɓuce mata, sai ta shiga halin damuwa da takura.

Hausawa sun ce: “Ba a maganin ciwon da aka ɓoye.” Wannan magana ta dace da yoyon fitsari, domin mata da dama suna ɓoye shi saboda jin kunya, alhali akwai hanyoyin magancewa, duk da cewa yana ɗaya daga cikin cututan da ke bayyana kansu, matuƙar ana mu’amalantar jama’a, saidai hakan bai hana wasu matan hawa dokin na ƙi ba kan neman magani. 

A yau shafin Gimbiya ya ɗauko wannan batu domin wayar da kai, ba da shawarwari, da kuma ɗauko wasu maganganu da jan kunne daga masana. Saidai kafin komai bari mu fara da ma’anar ita kanta cutar yoyon fitsari. 

Masana kiwon lafiya suna bayyana yoyon fitsari (urinary incontinence) a matsayin yanayi inda fitsari ke kuɓucewa daga mafitsara ba tare da nufi ko amincewar mace ba. Wannan na faruwa ne saboda matsalar tsokoki, jijiyoyi, ko tsarin mafitsara gaba ɗaya.

Likita mai kula da lafiyar mata a Asibitin Aminu Kano, Dr. Hadiza Sulaiman, ta bayyana cewa:

“Yoyon fitsari na iya zama na ɗan lokaci ko na dindindin. Amma duk da haka, yana da tasiri ga rayuwar mace idan ba a kula ba.”

Ana rarraba yoyon fitsari kashi-kashi:

Stress incontinence: Yana faruwa idan mace ta yi dariya, atishawa, ko ɗagawa sai fitsari ya kuɓuce. Wannan da yawan mata na fuskantar shi har suke sanar da kansu ba komai ba ne, kuma ba ya haifar da kowacce matsala.

Urge incontinence: Wani lokaci sai fitsari ya zubo wa mace kwatsam ta kasa tsayar da shi, ma’anaba ta da iko kan lokutan da fitsarin zai fito.

Miɗed incontinence: Haɗuwar nau’o’in biyu a lokaci guda, wato idan ta yi dariya ko atishawa da sauransu sai ya fito, kuma koda ba ta yi ba zai fito a duk lokacin da ya ga dama.

Dalilan da ke haifar da matsalar yoyon fitsari:

1. Haihuwa da raunin tsokoki;

Yawan haihuwa, musamman ta sananniyar hanya, ta tiyata ba, kan raunana tsokokin mara da mafitsara. Idan mace ta haihu sau da yawa ba tare da samun kulawar kiwon lafiya ba, hakan kan ƙara haɗarin yoyon fitsari.

2. Tsufa da sabanin jiki;

Yayin da mace ke tsufa, tsokokin jikinta suna rauni. Wannan na daga cikin dalilan da yasa yoyon fitsari yafi yawa ga mata masu shekaru 40 zuwa sama.

3. Tiyata da lalacewar jijiya;

Wasu tiyata kamar cire mahaifa ko tiyatar mara na iya shafar jijiyoyin da ke riƙe fitsari. Haka kuma, cututtuka kamar suga da hawan jini na iya lalata jijiyoyi su kawo matsalar.

4. Rayuwar yau da kullum;

Shan abin sha masu ƙara fitsari kamar kofi, shayi da abin sha mai gas, kan sa mace ta fuskanci yoyon fitsari da wuri.

Tasirin matsalar ga rayuwar mace:

1. Tasirin jiki;

Yoyon fitsari ba wai kawai yana kawo rashin jin daɗi ba, yana iya haifar da cututtuka kamar:

Fatar mara ta lalace saboda danshi.

Ciwon mafitsara akai-akai.

Matsalar wari da rashin tsafta.

2. Tasirin aure;

Wasu mata na guje wa kusanci da mazajensu saboda tsoron kuɓucewar fitsari a lokacin jima’i. Wannan kan kawo rashin jituwa a cikin aure.

3. Tasirin zamantakewa:

Mata da yawa na ƙin fita taro ko biki saboda kunya. Wannan na hana su shiga cikin al’umma.

4. Tasirin zuciya da hankali:

Damuwa, kunci, da jin ƙasƙanci suna yawaita ga mata masu yoyon fitsari. Wani bincike na WHO ya nuna cewa mata masu wannan matsala sun fi shiga damuwar zuciya sau biyu fiye da waɗanda ba su da ita.

Sheikh Abdullahi, malamin addini, ya bayyana cewa:

“Addinin Musulunci ya umarce mu da taimaka wa marasa lafiya. Idan mace tana fama da yoyon fitsari, wajibi ne a riƙa nuna mata tausayi da taimako. Wulaƙanci ba zai magance matsalar ba.”

Tsohuwar ministar lafiya ta Nijar, Dr. Aissata Issoufou, ta jaddada cewa:

“Cututtukan da ake jin kunyar faɗa sun fi cutarwa, domin suna ɓoye gaskiyar da ake buƙatar sani. Yoyon fitsari yana ɗaya daga ciki.”

Haka kuma marubuciya Maya Angelou ta ce, “gaskiya za ta ‘yantar da mu, amma sai mun yi ƙarfin hali mun faɗe ta.” Wannan magana ta dace da mata masu yoyon fitsari: sai sun faɗi gaskiya ne za a iya kawo musu ɗauki.

ƙalubalen da mata ke fuskanta idan suna ɗauke da matsalar yoyon fitsari:

Yoyon fitsari, musamman bayan haihuwa ko wani rauni na lafiya, na daga cikin matsalolin da ke da matuƙar nauyi ga mace, domin ba wai ciwon jikinta kaɗai ya taƙaita ba, har da tasirin da yake yi mata a rayuwarta gaba ɗaya. Wannan cuta tana shiga zuciyar mace ta wurare da dama, ta jiki, ta tunani, ta al’umma, har ma ta fuskar aure.

1. Rashin goyon bayan miji;

Da yawa daga cikin mata da ke fama da yoyon fitsari suna fuskantar matsala daga mazajensu. Wani miji kan ɗauki ciwon tamkar abin kunya, ya fara nuna ɓacin rai, ya guji kusantar matarsa saboda warin fitsari ko kuma ya fara ganin cewa matar ta zama “ɗawainiya.” Wasu lokuta ma hakan na kaiwa ga sakinta ko auren mata ta biyu, wanda hakan ya bar ita mai ciwon cikin ƙarin raɗaɗi da tunani. Wannan rashin fahimta daga miji na daga cikin manyan ababen da ke raunana mace mai fama da wannan matsala.

2. Kyama daga al’umma;

Mace mai yoyon fitsari kan shiga halin takura a cikin al’umma. Wani lokaci warin fitsarin da ba ta iya dakatarwa kan sa ta zama abin dariya ko ƙyama a idon wasu. Za ka samu tana zaune a taro, amma mutane suna ta kallo ko guje mata saboda wari, har ta kai ga ta riƙa jin kamar ba ta da daraja a cikin mutane. Wannan ƙyama tana ruguza mata girmamawarta, ta kan ji kamar an tsare ta cikin duhu, babu wanda ya fahimce ta.

3. Rashin walwala da ƙuncin zuciya;

Ci gaba da yoyon fitsari yana sa mace ta rasa walwala. Ta kan guji zuwa taruka, guje wa baƙi, guje wa zama a cikin jama’a, saboda tsoron wari ko ƙazanta. Wannan ke jefa ta cikin damuwa (depression), ta kan ji babu wanda ke son ta, babu wanda ya damu da ita. Da yawa daga cikin irin waɗannan mata kan zama masu yawan kuka, masu rabuwa da mutane, har ta kai ga ta ji kamar duniya ta kulle mata ko ba ta da amfani.

4. Halin da ake tsintar su ciki;

Matsalar yoyon fitsari ba wai cuta ce kawai ba, ita ma wata gwagwarmaya ce ta zuciya da rayuwa. Mace mai fama da shi kan tashi daga barci jikinta lulluɓe da fitsari. Tana so ta rungumi ‘ya’yanta amma tana jin kunyar wari. Idan mijinta ya matsa kusa da ita, tana firgita, saboda tana tsoron kada ya ƙi jinta ko ya gudu. Wannan hali na sa mace ta ji ba ta cancanci soyayya ko kulawa ba.

5. Tasiri ga aure da iyali;

Aure wani ginshiƙi ne na rayuwar mace a al’adunmu. Amma yoyon fitsari kan zama ƙalubale mai girma a wannan fuska. Yawanci miji ba ya jurewa wannan halin na tsawon lokaci, yana iya fara zargin cewa matar ta gaza kula da tsafta ko ba ta da amfani a matsayin abokiyar aure. Wannan zargi da ƙin yarda da ita na ƙara danƙwafar da ciwon, ya jefa ta cikin rashin kwanciyar hankali, ya kuma haifar da rabuwar zuciya a cikin gidan aure.

Yoyon fitsari ba kawai matsalar lafiya ba ce, wata irin jarabawa ce da ke shafar martaba, mutunci, da rayuwar mace gaba ɗaya. Rashin goyon bayan miji da al’umma na sa mace ta shiga cikin wani irin yanayi mai ciwo fiye da na jiki. Ita mace mai yoyon fitsari tana bukatar kulawa, fahimta, da taimako, ba kyama ko guduwa daga gare ta ba. Duk wanda ya kyamace ta ko ya gudar da ita saboda wannan ciwo, ya ƙara mata raɗaɗin da ya fi na jikinta muni.

Abubuwa biyar da ya kamata mace mai yoyon fitsari ta gujewa:

1. Guje wa shan shayi, kofi da lemun da ke ɗauke da caffeine;

Waɗannan abubuwa suna ƙara yawan fitsari, suna kuma iya fusatar da mafitsara. Yin amfani da su kan sa mace ta riƙa jin gaggawar yin fitsari fiye da kima.

2. Guje wa nauyin jiki mai tsanani (Obesity);

ƙarin ƙiba na matsa wa mafitsara da ƙashin ƙugu, yana ƙara lalata matsalar yoyon fitsari. Likitoci na ba da shawarar mace ta riƙa motsa jiki mai sauƙi domin rage klƙiba da ƙarfafa tsokokin ƙugu.

3. Guje wa ɗaga nauyi mai yawa;

A guji ɗaga kaya masu nauyi ko yin ayyukan da ke matsa ƙarfi a ƙashin ƙugu, domin hakan na ƙara raunana tsokokin da ke riƙe mafitsara.

4. Guje wa cin abinci ko abubuwan sha masu fusata mafitsara;

Abinci masu yaji, kayan zaki da abin sha masu ƙamshi (irin su ‘soft drinks’) na iya ƙara fusatar da mafitsara. Hakan na sa mace ta riƙa jin fitsari da wuri-wuri ko yoyon fitsari.

Shawarwari da hanyoyin magani:

1. Tuntɓar likita;

Maganin yoyon fitsari yana samuwa ta hanyoyi daban-daban. Wasu mata na buƙatar tiyata, wasu kuma na warkewa da magunguna ko motsa jiki.

2. Motsa tsokoki (Kegel Eɗercises);

Wannan motsa jiki na taimaka wa tsokokin mara su ƙarfafa. Ana yin sa ta hanyar matsewa da sakin tsokoki na mara na ‘yan daƙiƙoƙi, a maimaita sau da dama a rana.

3. Sauya salon abinci;

Rage shan abin sha masu ƙara fitsari kamar kofi, shayi, da soda. A kuma ƙara shan ruwa cikin lokaci ba tare da wuce gona da iri ba.

4. Taimakon iyali;

Miji da iyali su nuna goyon baya da tausayawa, kada su ƙyamace mace. Wannan tallafi shi ne mafi girman magani ga zuciya.

5. Wayar da kai;

ƙungiyoyi da hukumomi su ci gaba da wayar da kai, musamman a karkara inda mata da yawa ke fama da wannan matsala ba tare da taimako ba.

Matsalar yoyon fitsari ta shafi dubban mata a Najeriya da duniya baki ɗaya. Abin bakin ciki shi ne, mata da yawa suna ɓoye matsalar saboda jin kunya, alhali ana iya samun mafita.

Hausawa sun ce: “Idan aka yi shiru da ciwo, sai ya yi shura da rai.” Don haka, mace ta nemi taimako, ta yi ƙarfin hali ta bayyana matsalar. Idan aka kula da wuri, za a iya magance ta cikin sauƙi.

Daga ƙarshe shafin Gimbiya na wannan satin yana kira ga kowace mace da kada ki ji kunya, ki nemi magani, ki yi ƙarfin hali na fifita samun lafiyarki fiye da jin kunyar da ki ke yi, kuma muna kira ga iyalai da mazaje, ku kasance ginshiƙi na taimako da fahimta, domin lafiyar mace ita ce ginshiƙin lafiyar iyali, kuma lafiyar iyali ita ce ginshiƙin al’umma bakiɗaya.

By ukarofi