2027: Gwamnatin Tarayya ta magantu kan tsayawa takarar Jonathan, ta zarge shi da almubazzarantar da Dala biliyan 66

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi tsokaci game da rahotannin da ke cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ka iya tsayawa takara a zaɓen 2027, tana mai gargaɗin cewa ƴan Nijeriya ba za su manta da abinda da ta kira da tarihin ƙuncinsa a karagar mulki ba.

Kakakin shugaban ƙasa Bayo Onanuga a wata takarda, ya ce bayyana haka bayan da tsohon ɗan siyasa, Jerry Gana ya ce akwai yiwuwar Jonathan ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

A cewar Gana, Jonathan ka iya kayar da Shugaba Bola Tinubu da sake koma wa karagar mulki bayan shekaru 12.

Saidai, duk da wannan ikirari, Fadar Shugaban Ƙasar ta yi watsi da hakan inda ta ce matuƙar ta tabbata Jonathan zai tsaya takara, hakan zai iya tuna wa ƴan Nijeriya halin raɗaɗin da suka shiga a baya.

Onanuga ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu zai marabci Jonathan a matsayin abokin karawarsa, saida a gefa guda kuma zai tuna wa al’umma irin bala’in da suka shiga a tsawon shekaru kusan shida da ya yi a baya, inda daga bisani aka kada shi a 2015.

Fadar ta kuma zargi gwamnatin Jonathan da kashe-kashen kuɗaɗe na babu gaira babu dalili, rashawa da rashin kula da harkar tattali yadda ya dace.

Kazalika, ta tuno yadda aka zargi gwamnatin nasa da almubazzarantar da maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai Dala biliyan 66 na asusun rarar kuɗi da na rarar albarkatun mai daga 2010 zuwa 2015.

By Babaji