‘Yan fashi sun halaka ƴar jaridar Arise News, Sommie a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar gudanarwa da ma’aikatan gidan talabijin na ARISE News na jimamin rasuwar ɗaya daga cikin jami’ansu mai haskawa, wato Somtochukwu Christelle Maduagwu.

Ta rasa ranta ne a hannun ƴan fashi a gidanta da ke Katampe a Abuja, a lokacin da suke je fashi a yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa iftila’in ya auku ne a safiyar ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025, wanda a yanzu Hukumar ƴan sandan take bincike a kai.

Somtochukwu da aka fi sani da Sommie, an haife ta ne a ranar 26 ga watan Disambar 1995, ma’ana a matsayinta na ƴar shekera 29 ta kasance ƴar jarida ta musamman wajen jagorantar harkar yaɗa labarai, ruwaitowa da kuma mai shiryawa a ARISE News.

Akan haka ta zama ɗaya daga cikin ƴan jarida masu haskawa a fagen yaɗa labarai.

Baya ga kasancewarta ƴar jarida, Sommie ta yi karatun a fannin shari’a, wanda hakan ya sa ta ke da ƙwarewa ta fuskar tsara bayanai da nuna son adalci yayin haɗa rahotonta.

By Babaji