
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta sanar da soke faretin da ta shirya da farko domin bikin cikar shekera 65 da samun ƴancin kan Nijeriya a ranar 1 ga watan Oktoba.
Daraktan yaɗa labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), Segun Imohiosen ya faɗi haka a wata takarda.
A cewar saƙon da ke ciki, gwamnatin ta bada haƙuri akan takura da hakan ka iya haifar wa al’umma.
Imohiosen ya bayyana cewa, hakan bai ragi muhimmanci ko darajar ranar ba, sannan gwamnatin tana aiki tuƙuru wajen ganin ta an yi bikin cikin walwala.
Za kuma a gudanar da sauran shirye-shirye kamar yadda aka tsara su a jaddawalin taron.
Kazalika, gwamnatin ta yaba wa ɗaukacin al’ummar ƙasa bisa fahimtarsu, taimako da haɗin kai da kuma sauran baƙin da aka gayyata daga ƙasashen waje.
