Da wuri na gano haɗarin sankarar mama na yanke shawarar cire nonona – Angelina Jolie
Daga AISHA ASAS
Nono ba kawai abin ƙawa ba ne, tushen lafiya da rayuwa ne:
Mai karatu barkan mu da sake ganin zagayowar sati lafiya, sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja.
Kamar satin da ya gabata, mun sake zaƙulo maku darasi mai muhimmanci da muke hasashen za mu ƙaru da shi, wato za mu tattauna kan nonon mace, yadda yake, amfanin shi, cututtukan da ka iya samun mace ta ɓangaren sa, da ma ma’anar shi a ilimance.
Amma kafin komai bari mu fara shimfiɗa da labarin wara matashiya da mu ke fatan ya wanke ƙwaƙwalwar mai karatu don ɗaukar darasin yadda ya kamata.
Hauwa’u matashiya ce daga Jihar Katsina, mai shekaru 34, uwa ga ‘ya’ya uku. Ta yi rayuwa cikin walwala har zuwa lokacin da ta fara jin ɗan kumburi a nononta na hagu. Ta yi tunanin wannan ba komai ba ne, wataƙila sakamakon shan sanyi ko gajiyar aiki. Wata rana, yayin wanke kaya, ta sake jin wannan ƙurji yana ƙara tsananta. Lokacin da ta kai kanta asibiti, likitoci suka gano cutar sankarar nono a matakin farko. A yau, Hauwa’u na raye cikin ƙoshin lafiya, saboda ta samu gano matsalar da wuri.
Wannan labari na tuna mana cewa, lafiyar nono ba magana ce da za a yi wasa da ita ba, kuma ba ta jiran lokaci.
Duk da cewa, darasin namu ba wai zai karkata a iya sanƙarar nono ba, saidai na yi amfani da wannan ne don yin tarba da fuskantar da aka fi sani. Domin mutanen mu da zaran an yi maganar nono ko cutar da ta shafe shi, abu na farko da ke zo masu shi ne sankarar nono.
Idan kun fahimce ni, mu je ga sanin ma’anar nono a ilimin kimiyya.
A fannin likitanci, nono wanda ake cewa mammary gland tsari ne mai rikitarwa da aka gina musamman domin shayarwa da kuma tallafa wa tsarin hormone na mace. An raba shi zuwa lobes (sassa) 15–20, kowanne yana ɗauke da lobules, wato ƙananan ɓangarori masu samar da madara. Hanyoyin milk ducts su ne titunan da ke kai madara daga lobules zuwa nipple (nono), yayin da areola ke taimaka wa jariri ya gane inda za a tsotsa.
ƙwayoyin kitse suna zagaye da waɗannan sassan, suna ba nono laushi da siffa, yayin da jijiyoyi da hanyoyin jini ke kawo iskar oɗygen da sinadaran gina jiki. Wannan tsari ba wai kawai yana hidima ga shayarwa ba, har ma da tasiri ga tsarin rigakafi da kyawun mace.
Idan zan ƙara bayyani ga waɗanda ba su fahimci abin ba, zan yi shi ta fuska kamar haka:
Tsarin ciki na nono (Anatomy)
Idan aka dubi nono daga ciki, masana sun tabbatar yana da ɓangarori masu muhimmanci:
1. Lobes (sassan nono):
Nono na mace yana da kusan lobes 15 zuwa 20. Waɗannan lobes su ne ginshiƙan samar da madara, suna zagaye da ƙwayoyin kitse da jijiyoyi.
2. Lobules (ƙananan sassa):
A cikin kowanne lobe akwai lobules, wato ƙananan sassa da ke samar da madara kai tsaye lokacin shayarwa.
3. Milk Ducts (hanyar madara):
Waɗannan su ne hanyoyin da madara ke bi daga lobules zuwa ga nono (nipple).
4. Areola:
Wannan shi ne yankin da ke zagaye da nono, mai launi mai kauri, wanda ke taimaka wa wajen jan hankali ga jariri yayin shayarwa.
5. Kwayoyin Kitse:
Kitse shi ne ke ba nono laushi da siffa. Mafi yawan girman nono na da alaƙa da yawan kwayoyin kitse, ba wai adadin lobes ba.
6. Jijiyoyi da hanyoyin jini:
Suna kawo jini, iskar oɗygen, da sinadaran gina jiki zuwa nono, tare da ɗaukar gurɓatattun abubuwa daga ciki.
Abin tambayar anan shin meye ayyukan nono ga lafiyar jiki?
Ayyukan nono za su kai uku zuwa huɗu, wanda kowane yake da muhimmanci ga lafiyar ta, su ne kamar haka:
1. Samar da madara (Lactation) A ƙarƙashin tasirin da masana ke kira da hormone prolactin da oɗytocin, nono ke samar da madara mai wadataccen sinadarai ga garkuwar jiki.
2. Tallafa wa tsarin Hormone. Nono na amsa alhakin canjin estrogen da progesterone, wanda ke da alaƙa da al’adar mace da kuma haihuwa.
3. Kariyar jariri: Madarar farko (colostrum) na ƙunshe da sinadaran kariya masu hana cututtuka ga abinda ake shayarwa.
4. Ado da alaƙa ta zamantakewa: Wannan shi ne sanannen ma’anar nono da muka fi sani, wato a wasu al’adu, nono na waƙiltar kyawun mace, har ake ganin mai shi a matsayin wadda ta fi saura komai. Wasu kuma a tasu al’adar suna danganta yanayin nonon mace da haihuwa ma’ana suna fitar da matan da ake wa hasashen haihuwa da adadin yawan ta ta nononsu. Wasu kuwa suna danganta siffar nonon mace da irin tasu sha’awar.
Kafin mu kai ga bayyana cututtuka da ke iya samuwar nono, za mu fara da tambayar da na san da za a ba wa masu karatu da yawa dama za su fara da ita ne, wato dalilan da ke sa nono ke faɗuwa ko rage girma.
Kamar yadda masana suka bayyana, ababe da yawa na kawo dalilin faɗuwar nono, wanda suke kamar haka:
1. Tsufa (Aging)
Yayin da aka fara manyanta, kitse a nono na raguwa, fata na rasa taushinta, kuma tsokokin goyon baya (Cooper’s ligaments) sukan yi rauni, hakan na sa nono ya faɗi.
2. Canjin nauyin jiki:
Tashi da saukar ƙiba, wato mutum ya yi ƙiba ya zo ya rame na iya sa nono ya yi girma ko ya ragu, domin yawan kitse a nono yana canzawa daga nauyin jiki.
3. Shayarwa da haihuwa:
Lokacin shayarwa, nono na kumbura saboda samar da madara. Bayan shayarwa, yawanci yana komawa, ya yi ƙanƙanta, wani lokaci ya fi ƙanƙantar da yake a baya.
4. Rashin motsa jiki na tsokokin ƙirji:
Ko da yake tsokokin ƙirji ba sa cikin nono kai tsaye, suna goyon bayan siffarsa. Rashin motsa jiki na iya sa nono ya faɗi.
5. Gado (Genetics):
Halittar kwayoyin halitta na da tasiri a girma, siffa, da yanayin faɗuwar nono. Ma’ana ana iya gadon nono masu girma ko ƙanane daga wurin dangi ko iyaye.
6. Canjin Hormone:
Lokacin shigar mace cikin shekaru na tsayawar al’ada (menopause), yawan estrogen yana raguwa, wanda ke sa nono ya rasa tsayuwa da laushin da yake da shi a baya.
7. Cututtuka ko rauni:
Wasu cututtuka ko rauni na iya rage yawan kitse ko tsokar goyon baya a nono.
Kalaman Dakta Zuwaira Musa, ƙwararriyar likitar mata a asibitin ABUTH Zaria, za su zama hujja ga wannan bayani da muka yi, inda take cewa, “Nono na canzawa da shekaru, canjin hormone, da yanayin rayuwa. Kula da lafiyar jiki gabaɗaya, motsa jiki, da rigakafin cututtuka na taimaka wa wajen kiyaye lafiyar nono na dogon lokaci.”
Waɗanne irin shawarwari ne ya kamata a hau kansu don kula da tsayuwar nono?
A al’adar Hausa, akwai karin magana da ke cewa “Riga ya fi magani.” Wannan magana na da muhimmanci musamman a batun lafiyar nono. Nono ba kawai ado ba ne, ɓangare ne na lafiyar mace wanda ya shafi haihuwa, shayarwa, da ma yanayin kwanciyar hankali na mace. Idan mace ta kula da nononta tun da wuri, za ta guji damuwar da wasu ke shiga daga baya.
Masana lafiya sun bayyana cewa, kashi 40 cikin 100 na matsalolin nono a Najeriya ana iya kauce masu idan ana bin wasu ƙananan matakai na kiwon lafiya a kai a kai. Wannan ya haɗa da tsafta, motsa jiki, cin abinci mai gina jiki, da yin gwaje-gwajen duba lafiya.
“Mace mai kula da nononta tana rage yiwuwar kamuwa da cutar kansar nono har zuwa kashi 30 cikin 100,” a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, ɓangaren rahoton kansar mama na 2024.
Ga wasu shawarwari masu muhimmanci da kowace mace za ta iya aiwatarwa:
1. Yin gwajin nono na akai-akai (Breast Self-Eɗamination).
Duk wata, musamman bayan al’ada, mace ta tsaya a madubi ta duba nononta ta hanyoyi uku:
Ta duba idan akwai wani canji a siffa, launi ko girma.
Ta taɓa da yatsa don jin ko akwai kumburi ko ƙurji.
Ta lura da ko akwai zubar wani ruwa ko jini daga ƙashin nono.
Idan an lura da canji, a gaggauta zuwa asibiti.
2. Ziyarar asibiti duk shekara:
Masana sun ba da shawarar cewa, mace ta je yin gwajin nono a wurin ƙwararren likita aƙalla sau ɗaya a shekara. Wannan gwajin na iya haɗawa da mammogram ko ultrasound idan ya zama dole.
3. Saka rigar nono mai inganci:
Rigar nono mai kyau tana goyon bayan nono yadda ya kamata, tana hana tsokoki su yi rauni. A guji saka riga mai matse jiki ko kuma wadda ta yi sako-sako sosai.
4. Motsa jiki akai-akai:
Ayyukan motsa jiki kamar push-ups, iyo (swimming), ko amfani da dumbbell don chest press na taimaka wa tsokokin kirji su ƙara ƙarfi, wanda ke goyon bayan nono.
5. Cin abinci mai gina jiki:
Abinci mai wadataccen; ɓitamin C da E don lafiyar fata,
Protein don ƙarfafa tsokoki, Omega-3 fatty acids daga kifi ko man gyada don hana kumburi.
A guji abinci mai yawan kitse mara kyau da sukari.
6. Kauce wa canjin jiki da sauri:
Saurin yin ƙiba ko ramewa na iya sa fata ta yi rauni, yana haifar da faɗuwar nono.
7. Gujewa shan taba da barasa:
Hukumar Lafiya ta Duniya, wato WHO ta nuna cewa, shan taba na ƙara haɗarin kamuwa da cutar kansar nono har zuwa kashi 25 cikin 100.
8. Yin hutu da isasshen barci:
Rashin barci na rage iskar melatonin a jiki, wanda ke da alaƙa da kariya daga wasu cututtuka.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa da yardar Allah.
