Sarkin Oyo ya ba Oonin Ife sa’o’i 48 ya soke sarautar Okanlomo da ya ba ɗan kasuwa, Ilaji

Spread the love

Dafa BELLO A. BABAJI a Abuja

Sarkin Masarautar Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade ya bai wa Ooni na Ife, wato Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi kwana biyu na ya soke sarautar Okanlomo na Masarautar Yarbawa da ya ba ɗan kasuwa Dotun Sanusi wanda ake kira da Ilaji.

A sanarwar da Kakakin sarkin, Bode Durojaiye ya fitar, Alaafin ya bayyana matakin da Oonin ya ɗauka a matsayin karan-tsaye ga dokar Masarautar Yarbawa.

Saboda haka a matsayinsa na babban sarki, shi ke da ikon bada sarauta a baki ɗaya yankin ƙabilarsu.

Ya kuma zargi Oonin da wuce iyakarsa gami da yin watsi da hukuncin Kotun Ƙoli da ya bai wa Alaafin cikakken ikon naɗa sarauta a faɗin ƙasar Yarbawan.

Kazalika, ya bayyana matakin Oonin a matsayin abinda aka yi ta haramtacciyar hanya da ƙoƙarin taka doka, yana mai gargaɗinsa da ya janye cikin kwana biyu.

Har’ilayau, ya ce matuƙar ya yi buris da umarnin, zai iya fuskantar hukunci mai tsanani a ƙarƙashin majalisar dokokin sarautar ƙasar.

By Babaji