
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ƴan sanda a Jihar Neja, ta cafke wata yarinyar shago, Sarah Ogbonna mai shekaru 23 bisa zargin ta da sace kadarorin da kuɗinsu ya kai kimamin Naira miliyan 29 a Minna.
Lamarin ya auku ne a wani shagon sayer da wayoyin hannu, kamar yadda kakakin ƴan sandan, Wasiu Abiodun ya bayyana a wata takarda, ranar Litinin.
A cewarsa, mai shagon, wanda ke yankin Obasanjo Complex a cikin garin Minna ya rawaito wa shiyyar A ta rundunar al’amarin tun a ranar 8 ga watan Agusta.
Baya ga haka, jami’ansu suka gaggauta kamo Sarah bisa tuhumar ta da aikata laifin.
A yayin bincike aka gano cewa matashiyar ta kasance tana aiki a shagon tun a shekarar 2023, kuma ba ta san ko abinda ta ɗauka a shagon zai kai na Naira miliyan 29 ba.
Kakakin ya ƙara da cewa, bayanan da ta bayar sun taimaka wajen kama wasu mutane uku da ke da alaƙa da lamarin a ranar 9 ga Agusta.
Sauran waɗanda aka kaman sun haɗa da Ruth Omor Emmanuel (23) daga Tunga, Minna; Mercy Ogbonna (30) ta Okada road; da kuma Nurudeen Musa (32) na Obasanjo Complex, Minna.
Kakakin ya ce, a yayin gudanar da bincike akan baki ɗayansu ne aka ƙwato wasu ababe daga hannun Sara.
