Ɓarayin daji sun halaka mutane 13 a wani masallaci yayin sallar Asuba a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙara tura jami’an tsaro bayan wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai ƙauyen Unguwan Mantau a ƙaramar hukumar Malumfashi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13 a wani masallaci yayin sallar Asuba.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne a matsayin ramuwar gayya bayan da al’ummar ƙauyen suka yi musu kwanton-ɓauna kwanaki biyu da suka gabata, inda suka yi ajalin wasu daga cikinsu, tare da kuɓutar da waɗanda ɓarayin suka yi garkuwa da su, tare da ƙwace babura uku da bindigogi AK-47 guda biyu.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Dr. Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun isa yankin domin dawo da zaman lafiya, tare da tura sojoji da ’yan sanda don fatattakar ’yan bindigar da ke fakewa da amfanin gona a lokacin damina.

Daga ƙarshe gwamnatin jihar ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda harin ya rutsa da su tare da shan alwashin ɗaukar matakan da suka dace don magance matsalar.

By ukarofi