“Uwar da ta san daɗin sana’a ce ke koyar da ‘ya’yanta”
Daga AISHA ASAS
Har zuwa yanzu ba a daina samun al’ummar da ke nuna ƙyara da tsangwama ga matan da suka yunƙura don neman na kansu a ƙasar Hausa ba. Wasu kan la’ance su don irin sana’ar da suka zaɓa, wadda suke ganin bata dace da su ba a matsayin ‘ya’ya mata ba, yayin da wasu ke yin kuɗin goro kan mata masu neman na rufa wa kai asiri, wato matan da ba su da kamun kai ne kawai ke fita nema.
Duk da wannan matan da suka san ciwon kansu ba su bari wannan ƙalubalen ya zama hujjar zaunewa a gida suna zaman kashe wando ba, sai dai sun yi dogon tunani don samar wa kansu maslaha, ta hanyar zaɓo sana’ar da ta yi daidai da su, wadda zata kare mutuncin su na mata.
A wannan mako kamar kowanne lokaci, shafin Gimbiya ya yi wa masu karatu babban kamu, wadda muke da tabbacin mata da yawa za su ƙaru da irin rayuwa da matakan da ta taka da suka isar da ita ga nasara.
Hajiya Farida Musa Kalla, wadda ku ka fi sani da FMK, jajirtacciyar mace ce, da ta iya haɗa taura biyu a lokaci guda ta taune. Mai ilimi ce da ta ba wa boko dama sosai a ƙwaƙwalwarta, domin ta mallaki digiri a ɓangaren Tattalin Arziki, duk da haka, bata tsaya jiran kammala karatu don cin moriyarsa ba, Hajiya Farida ta duƙufa neman na kanta ta hanyar kasuwanci, wanda a halin yanzu ta ke cin moriya.
A tattaunawarta da Manhaja, mai karatu zai ilimintu da ababe da dama musamman ta ɓangaren kasuwanci da sauran batutuwan da muka tattauna da ita.
Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Hajiya Farida FMK:
MANHAJA: Mu fara da jin tarihinki.
FMK: Assalamu alaikum. Sunana Farida Musa Kallah. An haife ni a unguwar Gwammaja da ke Jihar Kano. Na yi karatuna na firamare a Model Nursery and Primary da ke Sharaɗa, sannan na yi sakandare a Saint Louis secondary school. daga nan kuma na wuce Jami’ar Kano, inda na soma da difiloma a ‘Banking and Finance’, daga nan na ɗora da BSc a ɓangaren Tattalin Arziki, wato Economics. Na yi bautar ƙasa a asibitin ƙashi ita ma dai a cikin Jihar Kano, wato asibitin ƙashi da ke Dala.
Ina da aure kuma Allah Ya azurta ni da ‘ya’ya guda huɗu, mata biyu, maza biyu. Alhamdu lillah. Wannan shi ne tarihina a taƙaice.
A matsayinki ta mace ‘yar kasuwa da Allah Ya tarfa wa garinki nono ta fuskar kasuwanci, masu karatunmu za su so jin ta yadda ki ka fara wannan kasuwancin.
Alhamdu lillahi, zan iya cewa, na fara kasuwanci da ɗan kuɗi ƙalilan, domin na fara ne tun a lokacin da nake zuwa makaranta, ‘yan kaya kaɗan, waɗanda za ka iya riƙewa a hannu, ka siyar wa da ƙawaye da sauran abokanen karatu da suke zagayen ka.
Da irin haka na fara, har zuwa lokacin da na fara BSc, a lokacin Ina da aure, ba zan manta ba a shekarar 2010, mahaifiyata ta ba ni wasu kuɗaɗe da niyyar in siye mota, saboda samun sauƙin zuwa makaranta, saboda ga aure ga kuma haihuwa da na yi, to shi ne fa ta ba ni kuɗi dubu ɗari shida in samu motar zuwa makaranta.
To waɗannan kuɗin ne sai maigidana ya ga bai kamata a ce a take na siye mota da su ba, ya ce, na yi haƙuri da abinda muke da shi, idan lokaci ya yi da kansa zai siya min motar. Da wannan muka ajiye kuɗin har zuwa lokacin da nake bautar ƙasa. To a lokacin ne ya kawo shawarar me zai hana kuɗin na yi amfani da su na ƙara jari, na juya su , na dinga siyen ire-iren su atamfa, tunda ya ga sana’ar atamfar ya fi ƙarɓa ta. Saboda kamar lokacin salla haka, zan iya siyar da atamfofi kamar ɗari haka, kuma akafar sada zumunta ta Fesbuk (Facebook) kawai, domin a lokacin ma babu irin su Instagram da sauransu.
Da wannan ne ya ga zan iya bunƙasa sana’ar da waɗannan kuɗin, domin idan har zan iya siyar da atamfa kusan ɗari a shafin sada zumunta, kuma ba bashi ba, to ina ga na haɗa da fita da su, tunda a lokacin Ina zuma asibitin ƙashi.
To a lokacin gaskiya ban so hakan ba, domin Ina ganin yin amfani da wannan kuɗin da nake ajiyewa kamar ba zai haifa min ɗa mai ido ba, kuma ma a lokacin jin kuɗin nake tamkar kuɗin cizo, saboda tsoron kar kuɗin su zo su lalace, kin san yadda farkon kowanne kasuwanci yake, akwai tsoron faɗuwa.
To fa sai da ya kwantar min da hankali kan cewa, idan kuɗin sun lalace shi zai biya ni, kuma a matsayin sa na ɗan kasuwa sai abin ya zo min cikin sauƙi, domin ya ɗora ni kan layi, don haka ban samu matsaloli masu yawa ba.
Kowacce sana’a tana tattare da ƙalubale. Ko akwai waɗanda ki ka samu a farkon fara kasuwanci?
Zancen ƙalubale kam sai dai mu yi hamdala, saboda a matsayina ta ‘ya mace kuma ‘yar Arewa, kuma yanayin sana’ar da nake yi sai ya kasance ba mata ne aka fi sani da ita ba. Babban ƙalubalen da na fuskata shi ne, kutsawa cikinsu don yin irin abinda aka fi sanin su da shi, sai na kasa ‘coping’, sannan su suka dinga yi min kallon baƙuwa, saboda ba abu ne da suka saba gani ba, to amma alhamdu lillahi, tafiya da ta yi tafiya ne sai suka haƙura, suka amshe ni a matsayin ɗaya daga cikinsu. Suka karɓe shi a matsayin canji ne ya zo, saboda idan kin yi duba da sana’ar a wasu jihohi kamar Iko, za ki ga sana’a ce ta mata, amma mu anan mazan ne aka fi sani da ita. kinga kuwa su baƙo a can su ga namiji a kasuwa, mu kuma anan aga mace a kasuwa tana sana’a.
Idan na fahimce ki sosai, kuɗin da aka ba ki don siyan mota ne ya ƙarfafa kasuwancin da ki ke yi. Shin hakan ya zama alkhairi a gaba, ko kuɗin sun samu matsala?
ƙwarai kuwa da gaske, hakan ya zama alkhairi, alhamdu lillahi, domin a cikin shekara ɗaya da fara juya kuɗin, zan iya cewa, na mayar da kuɗin, zan iya ma siyan mota a lokacin duk da cewa, farashin mota a lokacin ba ɗaya ba ne da lokacin da na yi niyyar siya. Don haka ya zama alkhairi gare ni sosai. Kuma kinga ban samu matsala sosai a kasuwa ta ba, tunda kinsan dai babbar matsalar kasuwanci shi ne, bada bashi, yana matuƙar karyar d asana’a, to kinga ni ban fara da bashi ba, kuɗi-hannu nake nawa kasuwancin. Don haka ko da shekara ta zagayo, na samu alkhairi mai yawa da wannan kuɗin, kuma ga ƙarin cewa ba na buƙatar siyan mota a lokacin, saboda na san daɗin juya kuɗin, don haka na fi buƙatar su a kasuwancina.
Me za ki ce ga mata masu tasowa a yanzu da suka fi karkatar da hankalinsu kan saka kaya masu tsada ko riƙe manyan wayoyi alhali ba su da wata sana’a ko aiki da suke yi?
Gaskiya kam wannan ɗabi’a ta zama ruwan dare a tsakanin mata, ban sani ba ko don zamanin soshiyal midiya ne, don su saka, su nuna wa duniya suna sa manyan kaya ko suna riƙe babbar waya, wai duk dan a kalle su a matsayin wani abu. Wannan ɗabi’a ba ƙaramin illa ta ke yi wa al’umma ma gabakiɗaya ba, saboda sau da yawa za ki tarar masu wannnan ra’ayin sai sun yi daƙyar suke yin wannan ƙarya. Kiga matashi da babbar waya, amma yana neman na kuɗin abin hawa, ko na cin abinci. Yarinya bata sana’ar komai ta ƙuduri anniyyar mallakar waya ta maƙudan kuɗi, ina zata same su, bata da shi, amma tana da niyyar aikata komai ma don cikar burinta, to daga wannan ne fa rayuwa ke fara hawa matakin lalacewa.
Ba wai na ce matasa kada su sa kayan ƙwarai ba, ko kada su riƙe manyan wayoyi ba, su yi haƙuri har matsayi ya kai su ga yin haka ba ƙarya ba. Kuɗaɗen da za ka siye wata waya, sun ishe ka jan jari, ka fara sana’a, ka sa haƙuri, har Allah Ya kai ka ga iya mallakar kowacce irin waya ko kaya. A lokiacin idan ka yi ba mai ganin laifin abin, don guminka ne ka ke ci. Abu mai muhimmanci a rayuwa shi ne, mutum ya koyi sana’a, ya dogara da kanshi, domin a cikin sana’a akwai albarka, don haka mai yin ta ba a taɓa kiran sa wanda bai san ciwon kansa ba.
Ko sana’a ga ‘ya mace na taka rawa a zaman aurenta?
Gaskiya sana’a a wurin ‘ya mace na taka muhimmiyar rawa a zamantakewar aurenta, sabina idan kina da sana’a Ina mai tabbatar miki auren ma sai ya fi ƙarko fiye da na wadda ke zaman kashe wando. Ga uwa uba kwanciyar hankali, ba ki da tashin hankalin matsala ta taso miki kina fargaban ko miji ya yi ma ki ko akasin hakan. Sanin kin fi ƙarfin buƙatunki kawai wani kwanciyar hankali ne da ba wadda ta sani sai wadda ta ɗanɗana.
Idan kuwa ki ka zama a jerin matan da suke kallon miji ga duk wata lalurar da zata taso masu, zan iya cewa, ko ba ni ba ni kawai ya isa ya hana aurenku walwala, kusan zan iya cewa, zaman lafiyarku ba zai wuce kaso talatin bisa ɗari ba.
Zan iya cewa sana’a tana taka rawa wurin haifar da zaman lafiya, shi kuwa zaman lafiya shi ne ginshiƙin kowanne aure, domin da zaman lafiya ne kawai soyayya ke wanzuwa.
Ba mu labarin irin nasarorin da ki ka samu a ɓangaren kasuwanci kawo wa yanzu.
Alhamdu lillahi. Nasarorin da na samu ba za su ƙirgu ba, duba da cewa, na fara sana’a a falon gidana, ba ma ni da wani ɗaki takamaimai da zan iya ware wa sana’ar, a hakan aka wayi gari na tumbatsa na koma garejin gidana, saboda samun cigaba da wurin ya masu ƙaranci, a haka na sake yin gaba, inda na yi tsalle sai cikin kasuwa, na mallaki shago na farko, na sake ƙarawa da na biyu, na kai ga na uku.
Baya ga haka, Ina da katafaren shago a ƙofar gidana, don matan da ba sa iya zuwa kasuwa. An samu rufin asiri daidai gwargwado, an mallaki gidaje da wasu muradun zuciya. Alhamdu lillah!
Ko kin yi nadamar ajiye zancen aiki ki ka rungumi kasuwanci?
Gaskiya ban taɓa nadamar zaɓar sana’a na share zancen aiki ba, saboda sana’a ce ta ba ni ababe da dama, ciki kuwa akwai samun cikakken lokacin kula da iyalina da ni karan kaina, wannan ya sa na gane fa’idar sana’a, domin ni da da nake son aiki, sai naga zan je ne na yi aiki a ƙarƙashin wani, in fita da sassafe, na bar iyalina. Sai na fahimci kamar ban yi tunani ba sosai a lokacin, domin sana’a bata tursasa ni yin wannan ba. Ina tare da iyalina, komai a gida nake yin sa, musamman ma idan ka yi tsari mai kyau, domin zamani ya kawo sauƙi a harkar kasuwanci, a gida ma sai ka yi ta waya kana kasuwanci da kula da sha’anin sa, ga kuma na’urar CCTɓ da za ka iya saka wa, daga gida ka dinga kallon duk abinda ke wakana a wurin sana’ar ka.
Don haka gaskiya ban taɓa nadamar rashin yin aiki ba, sai dai ma jin daɗin da nake yi na kai matakin da na ɗauki ma’aikata da suke aiki a ƙarƙashina, suna samun rufin asiri. Na zama hanyar samar da aikin yi ga mutane, domin a yanzu muna da ma’aikata kusan 40, kuma muna ci gaba da ɗaukar wasu. Gaskiya sai hamdala.
Wacce shawara za ki ba wa macen da ta ce, tana son sana’a, amma ba ta da wani ƙwaƙwaran jari, ko ba ta da jarin kwata-kwata?
To zance na gaskiya jari shi ne sana’a, sai dai bai kamata a ce mace ta rena kaɗan da ta ke da shi a lokacin da zata yi sana’a. Ki duba ki ga abinda ki ke da shi, komai ƙarancin shi, ba za a rasa sana’ar da zai iya yi ba. Sai ki yi nazari ki duba irin wurin da ki ke zama, menene aka fi buƙata ko yawan siya. A ciki sai ki zaɓi wanda kuɗin da ki ke da shi za su iya fara ta.
Bari in bada misali da ruwan leda, wato ‘pure water ‘, Ina yawan bada misali da wannan sana’a, yanzu a yanayin da muke ciki na zafi, mutane na yawan siyan ruwa. Kinga sana’a ce da idan kina da firijin za ki iya yi da ɗan kuɗi kaɗan. Ki sa a kula ko bokiti, ki samu ko almajirarai haka su zauna ma ki a ƙofar gida, su ma ki talla ko su zaga, suna saidawa. Kinga ‘yan na ɓatarwa za su dinga fitowa, kuma sannu a hankali za a kai ga babba.
Amma sai kiga mace na ƙorafin bata da kuɗi, amma tana da kuɗin sa data ta hau soshiyal midiya, kinga kuwa za a iya cewa tana da kuɗin da zata iya siyan fiyawata ta fara saidawa. Ba iya sanar ruwa kawai ba, akwai sana’oi da dama da mace zata iya duba wa ta ga wadda ta dace da kuɗinta, kuma idan ta yi za a siya a unguwar da ta ke zama. Daga nan ne zata fahimci daɗin neman na kai, sai ta dage, ta fara kallon gaba, wanda da ɗan abinda ta tara, sai ta ciyar da sana’ar gaba.
Ta yaya ki ke iya tauna taura biyu a lokaci ɗaya, wato kula da iyali, karatu da kuma kasuwanci?
Da farko dai idan da tsari ba na jin wani zai iya samun tawaya tsakanin waɗannan ababe guda biyu. Abinda ake buƙata, tsara kowanne a ba shi na shi lokaci. A gaskiya ban samu wata matsala ba wurin haɗa kula da iyali da kasuwancin da nake yi, saboda na yi wa kowanne matsaya mai kyau, kowanne daga ciki yana da lokacinsa.
Kasancewar ana cewa, wai mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo, don haka yake da matuƙar muhimmanci ki fahimci tsarin naki gida da kuma sana’ar da ki ke yi, don ganin kin ba wa kowanne muhimmanci da lokacin da yake buƙata, ba tare da kin tauye ɗaya daga ciki ba.
A ɓangare na waɗannan matakai na bi, don haka ban da matsala ta kowanne ɓangare, kuma komai na tafiya yadda nake so.
Wane kira za ki yi ga iyaye kan horar da ‘ya’yansu neman na kansu?
Ai uwar da ta san daɗin sana’a ba ta taɓa barin ‘yarta hakan kawai. Ai tun da wuri ta ke fara koyar da ‘yarta sana’a don ta san daɗinta da kuma illar rashin ta. Kuma kamar yadda aka ce, uwa ce makarantar farko ga ‘ya’yanta, kinga kuwa sana’ar da ta ke yi kawai ta koyar da ‘ya’yanta zaman banza ba na su ba ne. Duba da cewa mahaifiyarsu ba zaman banza ta ke yi ba, don haka su ma za su ga sana’a a matsayin wajibin su.
Abinda na jima Ina faɗa, ita sana’a daban ta ke, idan an kammala karatu ne, ko ana kan yi, ko ana aiki ne za ka iya yin sana’a kuma idan ka yi za ka ga alfanun ta. Kada ka ce don kana ɗaya daga cikin waɗannan ba za ka iya sana’a ba. Ita sana’a ita ce bata da lokacin gama ta, misali idan aiki ka ke yi, akwai lokacin ritaya, idan kana da sana’a a wannan lokacin ba za ka fara tunanin ina za ka ba, bare kuma su yara, wai a ce don suna karatu ba za su yi sana’a ba, shin kuna da tabbacin za su samu aiki a take bayan kammala karatun? Kuma ma yin sana’ar ta su a lokacin zata iya taimakon ku kanku iyaye, domin a hankali za su kai ga ɗauke ma ku wani nauyi nasu.
Don haka yana da matuƙar muhimmanci iyaye su cusa wa ‘ya’yansu so sana’a tun tasowar su, hakan zai iya zama hanyar da zata ba su rufin asiri.
Wasu na ganin sana’a zata iya hana yaro karatu, don haka sai su hane su da yin kowacce sana’a a ƙoƙarin su na ganin sun mayar da hankali sosai kan karatu. Me za ki ce game da wannan?
To a halin da muke ciki ma zan iya cewa muna bisa gaɓar da bai ma kamata ka hana wa yaronka yin sana’a ba wai don yana karatu. Duba da cewa mutane nawa suna kammala karatun, amam ba aikin yi, suna zaune a gida, saboda ba su da sana’a kuma aikin bai samu ba, sai fa a lokacin ne za su fara tunanin neman sana’a.
Mu kanmu muna ganin irin waɗannan, za ki ga yaro ya gama karatu, an kawo mana Cɓ shi, ana neman mu ɗauke shi aiki, saboda bai samu ba a inda yake tsammanin samu. Kinga kuwa da tun lokacin da suke karatun iyaye sun nuna masu muhimmancin sana’a tare da sa su a hanya, da wataƙila ko da za a kammala karatu ana da wani mudabbari da za ka iya dogaro da shi.
Yanzu ko ɗan harkan nan ta siyar da data, amatsayin ka na ɗalibi za ka iya haɗawa kana yi, da ɗan jari kaɗan, kuma bai taɓa karatunka. Ga sana’o’i nan da dama da za ka iya yi tare da karatu, ko iya na soshiyal midiya ma kawai za ka samu zaɓi masu yawa.
Kaga ta hakan idan dama ta ƙiya, sai a koma wa hagu. Idan aiki bai samu ba, dama ba ka zama baƙo a sana’a ba. Idan kuwa ya kasance zuciyar yaro ta bushe daga sana’a, bai san komai ba sai karatu, to fa a lokacin da ya kasa samun aiki kowanne irin hali ma zai iya shiga. Da wannan nake ganin ya kamata iyaye su dage ƙwarai wurin tusa wa ‘ya’yansu son sana’a tare da sa su a hanyar yadda za su yi. Idan kuma sun zo da irin wadda suke son yi, idan dai ba illa a ciki, kada a sare masu gwiwa, a ba su ƙwarin gwiwa yadda zai ƙarfafa su, su ƙara dagewa.
