
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wata gagarumar nasara da masu ababen hawa a Nijeriya suka samu, Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Owerri a Jihar Imo, ta hukunta cewa Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ba ta da iko a dokance ta ƙwace lasisin tuƙi na direba, mota ko kowace takarda da ke da alaƙa da su ba tare da bin hanyoyin da shari’a ta hukunta ba.
Haka kuma kotun ta ci tarar jami’an hukumar biyu a sakamakon ƙwace wa wani Dakta Emmanuel Ugochukwu Shebbs takardun motarsa da wulaƙanta shi a shekarar 2020, inda ta umarci a biya shi Naira miliyan 10 gq damejin da aka yu masa bayan ya shigar da ƙara.
A yayin hukuncin, tawagar alƙalai uku kan al’amarin ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Audi Wambai, kotun ta ce jami’an sun tauye ƴancin Dakta Ugochukwu da dokar ta ba shi a matsayinsa na ɗan Nijeriya.
Lamarin ya auku ne a wata rana da Dakta Ugochukwu ke tuƙi, inda jami’an suka tsare shi tare da tambayar sa takardun motarsa.
Bayan sun duba sun gano cewa babu matsala akansu, sai suka nemi ya ba su cin hanci inda ya ƙi amincewa tare da bayyana musu cewa ba shi da tsabar kuɗi.
Akan haka ne, suka zarge shi da saɓa wa ƙa’idodin tafiya a titi da cin sa tarar N3,000, sannan suka ƙwace masa lasisi duk cewa babu dokar da ya taka.

