Gwamna Dauda ya naɗa sabon Sarkin Gusau

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon sarki kuma Sarkin Masarautar Gusau.

Da yake sanar da hakan, sakataren gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa shawarar kwamitin naɗi da sarakunan masarautar Gusau suka bayar, bisa ga tsarin al’ada da kuma dokokin da suka dace.

Alhaji Abdulkadir ya hau karagar mulki a matsayin Sarkin Gusau na 16, bayan rasuwar mahaifin sa, Mai Martaba Dokta Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Yulin 2025, bayan shafe shekaru goma yana sarauta.

Sabon Sarkin, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, shi ne babban ɗan marigayi sarkin, kuma har zuwa lokacin da aka naɗa shi, ya rike sarautar gargajiya ta Bunun Gusau.

Gwamna Lawal, yayin da yake taya sabon sarkin murna, ya buƙace shi da ya ci gaba da riƙe wannan gado na kakanninsa, musamman a matsayinsa na zuriyar Malam Sambo Ɗan Ashafa wanda a tarihi shine wanda ya kafa garin Gusau.

Gwamnan ya kuma yi kira ga sarkin da ya zama fitilar haɗin kai, zaman lafiya, da ci gaba, wajen samar da zaman lafiya a faɗin Masarautar Gusau da ma wajen ta.

By ukarofi