“Rashin ƙwaƙƙwaran abin yi bayan aure ne babban ƙalubalen mata”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Mata na ba da gagarumar gudunmawa ga al’amuran da suka shafi cigaban al’umma, ta ɓangarori daban-daban. Daga ciki akwai mata da ke ba da gudunmawa a fagen harkar hidimar jama’a tare da ƙungiyoyi masu zaman kansu, suna gudanar da ayyukan jinƙai waɗanda jama’a da dama ke farinciki da su. Wannan agaji da taimako da ake bai wa waɗanda ke cikin halin tagayyara shi ya ja hankalin matashiya, Shamsiyya Ibrahim Barde, ýar garin Potiskum a Jihar Yobe ta shiga aikin hidimar al’umma, musamman bayan fitintinun da aka fuskanta na ayyukan ƙungiyar Boko Haram. A ganawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Shamsiyya ta bayyana masa dalilin ta na jingine sha’awar ta na shiga aikin likita ta koma aikin NGO. A yi karatu lafiya.
MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanki da abubuwan da ki ke yi na rayuwa.
SHAMSIYYA: Sunana Shamsiyya Ibrahim Barde. Ni ɗaliba ce, marubuciya, kuma ýar kasuwa. Ina kuma aikin wayar wa matasa kai akan zaman lafiya da tsaro.
Ki ba mu tarihin rayuwarki da yadda ƙuruciyarki ta kasance.
Ni haifaffiyar garin Potiskum ce, a Jihar Yobe. Mu tara ne a wurin mahaifana, kuma ni ce babba, ƙannaina takwas, huɗu mata, huɗu maza.
Na kasance mai yawan kazar – kazar lokacin ƙuruciyata, ina da tarin ƙawaye, kuma gaskiya mun yi rigima a makaranta, duk da ina da tsoron bulala.
Na yi karatuna na firamare da sakandire a nan garin Potiskum, a wata makaranta da ake kira International Nursery and Primary School. Na Kuma yi karatu a matakin ƙaramar sakandire a Kwalejin Ýammata ta Tarayya da ke Damaturu, sai na koma babbar sakandire a Kwalejin ‘Ýammata ta Tarayya wato FGGC da ke nan Potiskum. Na karanci aikin malanta a Kwalejin Horar da Malamai ta Tarayya da ke Potiskum, inda na karanci yadda ake koyar da ilimin Kwamfiyuta da ilimin halittu (Biology). Daga bisani kuma na shiga Jami’ar Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa, inda na karanta ilimin ƙananan halittu, a matsayin digiri na farko. Yanzu kuma ina digirina na biyu a ɓangaren nazarin aikin Kula da Lafiyar Al’umma, wato Public Health, a Jami’ar Jihar Bauchi ta Sa’adu Zungur da ke Gaɗau.
Wanne abu ne za ki ce ya taimaka miki yayin tasowarki da ya ba ki ingantacciyar rayuwa da tarbiyya?
Jajircewar iyayena da ƙoƙarin su na tabbatar da na samu wadataccen ilimi ta fuskar addini da boko, da kuma kasancewar su mutane masu tsanani kan tarbiyya.
Mene ne ya canza a tunanin ki game da yadda ki ke kallon rayuwa a da, da kuma yanzu bayan ki girma?
A gaskiya a da ina ganin rayuwa a matsayin wata aba da mutum kan iya tsarata kuma ya same ta a yadda yake so, a kuma lokacin da yake so. Amma a sannu, girma da hankali sun saka na fahimci rayuwa gaba ɗayanta jarrabawa ce, ba kodayaushe ne karatun da mutum ya yi yake fitowa a tambayoyi ba, amma in har an yi karatun, dole ba za a rasa abin da za a rubuta ba.
Wanne abu ne za ki iya cewa ya zama gadon gidanku, wanda ki ke alfahari da shi a duk inda ki ka shiga?
Gaskiya muna da tarbiyya, Alhamdulillahi. Yaran gidanmu na da ƙoƙari da juriya, kuma muna da kyakykyawan idanu da zuciya, da kuma saurin kuka.
Yaya ki ka fuskanci gwagwarmayar rayuwa a lokacin kina makaranta, kin gamu da takura ko ƙuntatawa?
Alhamdulillah, ban samu damuwa ba saboda komai na ɗawainiyar karatuna, mahaifina ne ya ke mani.
Wanne abu ki ke so ki zama wanda tun kina yarinya yake ranki? Har yanzu akan wannan burin ki ke ko ya canza?
Ina da mafarkin zama likita kamar yadda mafi yawancin yara kan yi mafarki yayin tasowa. Amma yanzu gaskiya mafarkina ya canza, don kuwa ina so na cigaba da bai wa al’umma gudunmawa ta hanyar wayar da kai akan abubuwan da nake da fahimta akai, musamman mata da ƙananan yara.
Gaya mana abin da ya ja hankalinki ga shiga ƙungiyoyin sakai na NGO, da irin ayyukan da ku ke yi?
Ayyukan da wasu ƙungiyoyin sakai suke yi ya tafi daidai da irin ra’ayina na hidimtawa al’umma, shi ya sa na kutsa kaina a ciki. Mun ɗan yi aiki akan cin zarafin mata da ƙananan yara ta fuskar jima’i (SGBɓ), tare da ƙungiyar HumAngle, inda na fara samun damar wallafa labarun waɗanda suka tsinci kansu a wannan yanayin (surɓiɓors), sai kuma tsaftar muhalli wadda muna dangantashi da ɗumamar yanayi, da kuma abin da yanzu na fi mayar da hankali akai wato PCɓE, ƙoƙarin wanke zukatan matasa daga tsattsauran ra’ayi da ka iya jefa su ga ayyukan ta’addanci. Kasancewata wacce ta fito daga Jihar Yobe, ɗaya daga cikin jihohin da ayyukan ýan ƙungiyar Boko Haram ya shafa, ina ganin dole ne mu cigaba da wayar da kan jama’a, don ganin an fahimci abubuwan da ke haifar da yawaitar masu tsattsauran ra’ayi saboda gujewa komawa gidan jiya.
Shin ke ma kina da burin kafa ta ki ƙungiyar watarana?
E. A gaskiya a yanzu dai ba zan iya cewa e ko a’a ba, sai dai duk abin da hali ya yi nan gaba.
Ba mu labarin yadda rayuwa ta kasance miki a lokacin da ake tsakiyar hare-haren Boko Haram?
Rayuwa ta yi wahala sosai, saboda kullum a cikin fargaba da firgici muke. Rikice-rikicen da aka yi sun kawo mana koma baya ta fuskar ilimi da kuma tattalin arziƙi. An rufe makarantu na tsawon watanni, iyaye da ƴan’uwa sun yi hijira, abubuwa marasa daɗi waɗanɗa ba mu so mu tunano duk sun faru. Allah dai ya ƙara karewa. Amin
Ta yaya hakan ya shafi rayuwarki da tunaninki a matsayinki ta ýa mace?
Hakan ya shafi rayuwata ta kowacce fuska, a matsayina ta ŷa mace. Hakan ya ƙara tabbatar min da dole na jajirce, na kuma zama mai dakakkiyar zuciya saboda yadda yanayin ya sa mata da yawa da suka rasa mazajensu, suka koma ɗaukar ɗawainiyar tarbiyya da hidimar iyalensu.
Waɗanne irin ƙalubale yara mata a yankin da ki ke suke fuskanta, wanda ki ke ganin da za ki samu dama da kin taimaka musu?
Rashin ƙwaƙƙwaran abin yi ko sana’a bayan aure. In da zan samu dama, kowacce mace idan za ta yi aure, zan bata jari da kuma dabarun kasuwanci.
Waɗanne abubuwa ne suka fi ɗaukar hankalinki, kuma ki ka fi mayar da hankali a kansu?
Ba da labari, wato Storytelling, ta hanyar rubutu ko kuma zane-zane, da kuma mu’amala da sabbin mutane. Ina da kwaɗayin sanin sababbin abubuwa (curiosity), shi ya sa wasu lokutan nake ɗan mayar da hankali wurin karatu akan abubuwan da nake da ra’ayi kamar addinai, al’adu da kuma ƙirƙirarrun labaru.
Kawo yanzu waɗanne nasarori ki ka samu sanadiyyar ayyukan da ki ke yi?
Alhamdulillahi. Akwai sanayya tsakanin mu da waɗanda ba don ayyukan ba, ba za mu taɓa samun damar sanin juna ba. Haka zalika akwai guraren da ba don ayyukan ba, ba zan taɓa zuwa ba. Babbar nasara ta ita ce kawo canji a rayuwar waɗanda muke mu’amala da su, da kuma muhallin da muke.
Shin kina da ra’ayin kasuwanci? Wanne irin kasuwanci ki ke sha’awa?
ƙwarai kuwa. Ina son kasuwanci sosai. Yanzu haka ma ina kasuwancin sayar da kayan sawa irin na maza (Moroccan Kaftan) kaɗan-kaɗan, da kuma kayayyakin mata kamar su camisole, black soap da turaruka. Buri na nan gaba shi ne na haɗa bodin tirela da za a riƙa min jigilar ɗaukar kaya, da kuma buɗe shagunan sayar da kayan masarufi.
Wacce gudunmawa mata za su iya bayarwa wajen kawo sauyi a cikin al’umma?
Ai mata su ne al’umma. Idan mata suka nemi ilimi, kuma suka yi ƙoƙarin aiki da shi ta hanyar mu’amalantar abokan zaman su, da kuma bada tarbiyya.
Shin kina da ra’ayin siyasa?
Wataƙila.
Idan za ki samu dama wanne matsayi ki ke sha’awar hawa a siyasance?
Minista.
Wanne abu ki ke yi a lokacin da ki ke cikin nishaɗi?
Ina rubutu, ko zane wanda ake launuka daban-daban (painting).
Shin wanne abu ne ya fi ɗebe miki kewa a lokacin da ki ke cikin kaɗaici ko ba kya komai?
Rubutu ko karatu.
Kuma ina ƙaunar barci.
Gaya mana wata karin magana da take tasiri a rayuwar ki?
Sannu bata hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba.
