
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya ci alwashin cigaba da tallafa wa Ƙungiyar ƴan kasuwa ta Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited, inda ya bukaci su kasance masu haƙuri, addu’a da jajircewa bisa ƙalubalen da suke fuskanta, sakamakon sauya wa kasuwar tasu matsuguni.
Alhaji Hamza Sule Mai Fata, wanda kuma shi ne Sakataren Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin ta jihar, ya kuma bayyana farin cikinsa kan ziyarar da ‘yan kungiyar kasuwar suka kai masa, inda ya ce yana alfahari da kasancewarsa tsohon dan kungiyar.
A sanarwar da Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, wato jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar, Ciyaman ɗin ya shawarci ‘yan kasuwar da su karɓi halin da suke ciki a matsayin jarrabawar Allah, tare da ƙarfafa musu gwiwa da su cigaba da kasancewa cikin imani da hadin kai.
Sannan kuma yi alkawarin kafa tsarin tallafi domin taimaka wa ‘yan kasuwar da suka yi asarar jarinsu sakamakon matsalar sauya wa kasuwar muhalli.
A wani ɓangare kuma, ƙungiyar ta kai ziyara ga Maigarin Bichi, wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar Ruwa ta Jihar Kano, Injiniya Garba Ahmad, inda ya yaba da jajircewar ‘yan kasuwar, tare da bayyana su a matsayin ‘ya’ya nagari na garin Bichi masu mutunta darajar masarauta.
Ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafa wa kungiyar tare da kira ga ƴan kungiyar, su rika kula da marayu, musamman ‘ya’yan abokan kasuwancinsu da suka rasu.
Kazalika, ƙungiyar ta ziyarci Shugaban Kasuwar Bichi, Alhaji Garba Tukur, domin taya shi murnar dawowa lafiya daga aikin Umrah.
A cikin jawabinsa, ya yaba wa kungiyar bisa kokarinta na karfafa hadin kai da shugabannin al’umma, malamai, da jami’an tsaro, kokarin da ya bayyana cewa zai habaka zaman lafiya da ci-gaban yankin.
Ƙungiyar ta kai ziyarar ta’aziyya ga daya daga cikin ‘yan kungiyar, Alhaji Ibrahim Mai Madara, wanda ya rasa dansa sakamakon hadarin mota kwanan nan, inda kungiyar ta yi addu’a, Allah ya jikan sa da rahama, tare da bai wa iyalansa hakurin rashin da suka yi.




