Natasha ta koma bakin aiki bayan kammala dakatarwar wata shida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a karon farko ta halarci zaman Majalisar Dattawa bayan wa’adi dakatar da ita da aka yi na watanni shida ya ƙare.

A yau Talata ne majalisar ta koma bakin aiki, bayan tsawaita lokacin komarsu da ƴan makonni daga hutun da suka tafi a watan Agusta.

Saidai Sanatar mai wakiltar Kogi ta Arewa ta halarci zaman majalisar ne, wadda mataimakin shugabanta, Sanata Jibrin Barau ya jagoranta a yau.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Shugaban Majalisar kuma abokin rikicin Natasha, Godswill Akpabio bai halarci zaman majalisar ba.

Dakatar da ita ya janyo cece-kuce sosai musamman a fagen siyasa duba da yadda zargin cin zarafin da ta yi wa Akpabio ya shiga cikin rikicin nasu.

By Babaji