Bai kamata mata su rungume hannu komai sai an yi masu ba – Bilkisu Beely 

Spread the love

“Idan kina yi wa kanki yan buƙatu har son ki sai ya ƙaru wurin mijinki”

Daga UMAR GARBA, a Katsina 

Bilkisu Yunusa matashiyar ‘yar kasuwa ce da ta yi fice a fannin sana’o’i iri daban daban, bata tsaya a nan ba domin kuwa matashiyar ta na koyar da matasa maza da mata dabarun kasuwanci na zamani. Wakilin Blueprint Manhaja a Katsina Umar Garba, ya zanta da Bilkisu Beely game da batutuwan da suka shafi dabarun kasuwanci a kafafen sada zumunta, yadda take koyar da wasu matan ƙananan sana’o’i a ajujuwan ‘online’, ta kuma ba wa matasa maza da mata shawara a kan su dage su nemi na kansu daga ƙarshen hirar Bilkisu Beely, ta bayyana mana ƙalubalen da ta fuskanta kafin a san ta a fannin kasuwanci, ta kuma bayyana nasarorin da ta samu a rayuwa.

MANHAJA: Shin ko zaki gabatar mana da kanki?

BILKISU: Assalamu alaikum warahmatullah. Sunana Bilkisu Yunusa wadda aka fi sani da Beely ni ‘yar kasuwa ce a nan cikin garin Katsina.

Za mu so jin taƙaitaccen tarihinki?

Ni dai an haife ni a ƙaramar Hukumar Kaita dake nan Jihar Katsina amma a halin yanzu ina zaune a unguwar ƙofar Sauri, cikin birnin Katsina. Na yi makarantar firamare a ƙofar Sauri Primary School, na kuma yi sakandare a Day Sahara Goɓt. Sec. Sch. yanzu haka ina neman ‘admission’ a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua dake nan Katsina don cigaba da karatun jami’a In sha Allah. Sannan na yi karatun addini bakin gwargwado ko kuma in ce har yanzu ina cigaba da neman sa.

An fi saninki a fannin kasuwanci. Me ce ce sana’arki?

Haka ne ni ‘yar kasuwa ce kuma na kasance ina sha’awar kasuwanci sosai saboda a gidanmu ma ko da na taso saye da sayarwa na ga mahaifina da yayu na maza suna yi, shine ni ma na fara ‘yan sana’o’i na mata bayan da na kammala karatun sakandare, kasuwancin ne ma ya sa ban cigaba da karatu ba bayan kammala sakandare to sai dai yanzu ina so na cigaba saboda a wannnan zamanin kasuwanci ya fi bunƙasa idan kana da ilimi.

Akwai kasuwanci da ake yi na zahiri kuma a akwai na ‘online’ wanne ne kika fi mayar da hankali?

Kasancewar ina sayar da abubuwa da dama kamar irinsu atamfofi, turaren wuta, turaren jiki ko na kaya da dai sauran kayan ado da kwalliya na mata, ina da shago na zahiri kuma ina amfani da soshiyal midiya, irin wannnan kasuwancin yana buƙatar mutum ya riƙa amfani da shafukan soshiyal midiya don tallata kayansa. Saboda haka lokacin da na fara kasuwanci na fara yi wa ‘yan uwa da abokan arziƙi talla idan na je gidan biki ko wajen wani taro sai in riƙa gaya wa mutane cewa ina fa sayar da kaya masu kyau da kuma arha daga nan sai na fara amfani da WhatsApp Status da kuma Instagram ina ‘posting’ Alhamdulillah wasu ta soshiyal midiya suka sanni har suke yin ‘order’.

Ya kike ɗaukar sana’a ga ‘ya mace?

Wasu lokutta ana gayyata ta wajen taron wayar da kan mata wanda ƙungiyoyi ko ‘yan siyasa ke ɗaukar nauyi don horar da mata game da sana’o’i daban daban, a duk lokacin da aka bani damar yin jawabi na kan gaya wa mata cewa su dage wajen koyon sana’o’i, saboda haka ina ɗaukar kasuwancin mata da muhimmanci sosai idan muka ɗauki sana’a ga ‘yan mata tana da muhimmanci sosai saboda idan kika fara sayar da wani abu a cikin gidanku za ki riƙa samun ‘yan kuɗin kashewa ta yadda ba sai kin roƙi mahaifanki ba ko wani a can waje, ke da kan ki zaki rufa ma kanki asiri, idan kuma muka ɗauki kasuwanci ga matan aure shi ma mace zata iya taimakon kanta da yaranta da kuma maigidanta abubuwa a halin yanzu sun yi wa maza yawa saboda haka sai muna taimaka masu idan mijinki ya ga kina yi wa kanki ƙananan buƙatu na yau da kullum wallahi har son ki sai ya ƙaru a cikin zuciyarsa.

Waɗanne dabaru kike amfani da su wajen tallata kasuwanci a kafafen sada zumunta?

Lokacin da na fara ‘posting’ turaruka a ‘page’ ɗi na a gaskiya na kusa haƙura da tallata kasuwancin a soshiyal midiya saboda za ka yi ta ‘posting’ har ka gaji ba wani ‘ɓisibility’ idan ka yi ‘posting’ ɗin sai ka ga kamar masu sayen kayanka ba sa ganin posting’ ɗinka to amma daga baya akwai wani taron koyar da dabarun kasuwanci ta ‘Online’ da na halarta, a wurin an koyar da mu yadda za mu yi posting’ kayan sana’armu da yadda za mu samu ‘engagement’ a gaskiya tun daga lokacin na gane yadda ake tallata haja ga ‘target audience’ ɗinka kuma tun daga lokacin na ke samun ciniki daga wasu jihohin. Yanzu haka ina shirye shiryen koya wa mata  yadda ake tallata kasuwanci ‘Online’ kuma a kyauta zan koyar da su saboda na ga amfanin abun sosai, saboda idan ba ki san waɗannan dabarun na ‘Online Marketing ba’ haka nan za ki ta ɓata datarki daga ƙarshe ki haƙura ki bari.

Waɗanne sana’o’i ne suka fi dace wa da mata?

Kusan duk sana’ar da maza ke yi muma mata za mu iya yi ko baki fito kika kama shago ba zaki iya daga cikin gidanki abunda kawai ake buƙata ki samu jari ki yi bincike game da sana’a ko kasuwancin da kike son farawa saboda mafi yawan kasuwancin mata yana rugujewa saboda basa yin bincike kafin su fara da zarar kin ga ƙawarki ko maƙociyarki ta fara sana’a kema sai ki ce irinta zaki fara ba tare da sanin abunda ya kamata ki sani ba game da sana’ar siyasa ilimin kasuwanci keda amfani.

A ganinki ta ya mata za su samu jarin fara kasuwanci?

Gaskiya ko wane sana’a yana buƙatar jari samun jarin shine babban ƙalubale saboda haka ana iya samun jari daga wajen mahaifa ko ki tambayi mijinki idan yana da hali ko ‘yan uwa da abokan arziƙi, kamar ni na samu jari wajen yayana saboda na gaya maka gidanmu duk ‘yan Kasuwa ne, sannan kada ki ce sai kin samu babban jari dubu biyar ma ya isa ki fara ‘yar ƙaramar sana’a cikin gida koda sayar da ruwan ‘pure water’ ne daga nan idan sana’ar ta haɓɓaka kina iya ƙara wata sana’ar akai saboda ƙaramin jari shike zama babba.

Me ye burinki a nan gaba?

Buri na shine kasuwanci na ya ci gaba da bunƙasa, sannan ina da burin taimaka wa ‘yan uwa na mata game da sha’anin kasuwanci ta hanyar buɗe ‘Online Classes’ don koyar da su dabarun kasuwanci na zamani, rayuwa ta yi tsada bai kamata mata su rungume hannu ba komai sai an yi masu akwai sana’o’i da yawa da zaki yi daga gidanki.

Ranar da baki fita kasuwa ba me kike yi don nishaɗantar da kanki?

Gaskiya ne wani lokaci idan kanka ya yi zafi kana buƙatar ‘yar sararawa, shiyasa wani lokaci bana ma fita kasuwar idan na ji kaina na ɗan juya wa sai dai na tura yara su kula da komai, ni kuma na zauna gida na ɗan taya mama girki da yake ina son yin girki sosai musamman ‘yan soye soye ko toye toyen ‘small chops’ sai kuma ni kan zauna na ɗauka waya ta na rinƙa yi wa masu bibiyar shafukana ‘reply’ game da wani abu da suke son sani da ya shafi kasuwanci wani lokacin kuma ni kan zauna in yi karatu.

Wane ƙalubale kike fuskanta wajen gudanar da sana’arki?

Gaskiya ƙalubalen bai wuce na ‘yan bashi ba mutum zai karɓi kayan sana’arka ya baka rabin kuɗin ko kuma ma wani lokaci za a karɓi kayan a ƙi baka ko sisi sai a ce sai ƙarshen wata idan lokacin biya ya yi ka yi ta fama da mutane su hana ka kuɗin wasu ma har suna gaya maka maganganu marasa daɗi don ka nemi a biya ka haƙƙinka, sai kuma yanzu kaya sun yi tsada wani lokaci dakyar ake mayar da kuɗin wasu kayan.

Duk inda aka samu ƙalubale akan samu nasara. Waɗanne nasarori kika samu a fannin kasuwanci?

Alhamdulillah an samu nasarori sosai, saboda na samu rufin asiri ni kan yi wa kaina duk wata hidima da ta shafi kashe kuɗi, ina taimaka wa mahaifana ina taimakon ‘yan uwa na saboda yanzu a cikin dangi kallon wata hajiya ake mini duk wanda ke da wata ‘yar matsalar kuɗi sai ki ji an ce a zo wuri na duk da ina da ‘yan uwa maza manyan ‘yan kasuwa amma kafin aje wurin su neman taimako an zo wuri na, to ka riƙa farantawa ‘yan uwanka rai ta hanyar taimakonsu da ‘yar ribar da kake samu shima nasara ne. Sannan na koya wa wasu mata irin wannnan kasuwancin nawa kuma yanzu haka wasu daga cikinsu sun dogara da kansu shima wannnan ina kallonsa a matsayin wata nasara da na samu a rayuwa.

Mun gode sosai da kika bamu lokacinki don yin hira da jaridar Blueprint Manhaja.

By ukarofi