Zargin kitsa juyin mulki: Ana binciken ƴan siyasa da sojoji a Kudu da Arewa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A sakamakon zargin juyin mulki ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, an sanya wasu ƴan siyasa da jami’an sojoji a yankin Kudanci da Arewacin Nijeriya a sahun waɗanda zargi ya yi ƙarfi akansu.

Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu ana gudanar da bincike akan wasu sojoji da ƴan siyasa bisa zargin su da hannu a kitsa juyin mulkin.

A kwanan nan ne Hedikwatar Tsaro DHQ, ta sanar da kama jami’an soji su guda 16 akan abinda ta kira da rashin biyayya ga tsarin aiki.

Saidai, wasu na ganin an kama su ne sakamakon zargin hargitsa ƙasar a ranar bikin ƴancin kai na wannan watan.

Daga cikin waɗanda aka tsare akwai wasu manyan sojoji da ke aiki a wasu wuraren na musamman. Sannan sashen Leƙen Asirin na hedikwatar, wato DIA ne ke jagorantar binciken da taimakon aiki daga rundunonin soji uku na ƙasar.

‎Mambobin kwamitin binciken sun haɗa da manya-manyan hafsoshin soji, bisa jagorancin wani mai muƙamin Manjo-Janar. An tsananta sirranta jerin sunayen waɗanda ake zargin saboda dalilai na tsaro.

Wani rahoto da PRNigeria ta fitar ya nuna cewa, wani sanannen ɗan siyasa daga kudu ne ake zargi da ɗaukar nauyin yunƙurin kifar da gwamnatin.

Haka kuma, jaridar ta ruwaito cewa, wasu daga cikin waɗanda da ke zargin suna da alaƙa da wasu manyan gidajen sarauta da na siyasa, lamarin da ya ƙara faɗaɗa al’amarin binciken.

By Babaji