ASUU: NLC ta gargaɗi Gwamnatin Tarayya kan rikici da manyan makarantu

Spread the love

Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta ba gwamnatin tarayya wa’adin mako huɗu domin ta kammala tattaunawa da ƙungiyoyin ma’aikata na manyan makarantu ko kuma ta fuskanci yajin aikin ƙasa baki ɗaya daga dukkan ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta.

Shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero, ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, inda ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ƙungiyoyin ilimi don tabbatar da biyan haƙƙoƙin da aka amince da su, da kuma inganta kuɗin gudanarwa da albashi a jami’o’i, kwalejoji da sauran cibiyoyin ilimi.

Ajaero ya ce, NLC ba za ta sake amincewa da gwamnatin da ke turo wakilai masu halartar tarurruka ba tare da ikon yanke hukunci ba, yana mai cewa wannan ɗabi’a ta jima tana dagula lamari tsakanin gwamnati da ASUU.

Ya jaddada cewa, duk wata ganawa da gwamnati daga yanzu sai ta haifar da mataki na ainihi, ba alƙawurran bogi ba.

Shugaban ƙungiyar ya ƙara da cewa, matakin ya biyo bayan cigaba da rashin biyan haƙƙoƙin malamai, da rashin aiwatar da yarjejeniyoyi gami da ƙarancin kuɗin gyaran makarantu, lamarin da ke ƙara jefa harkar ilimi cikin ruɗani.

Haka kuma, ƙungiyoyin NASU da SSANU sun sake yin barazanar yajin aiki saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da aka yi musu tun da daɗewa.

‎Kazalika, Ajaero ya gargadi gwamnati da cewa idan ta gaza magance matsalolin cikin mako huɗu, NLC za ta tsunduma cikin yajin aikin ƙasa baki ɗaya, wanda zai haɗa dukkan ƙungiyoyin ma’aikata a faɗin ƙasar.

By Babaji