Barazanar ƙasashen waje na neman durƙushe haɗin kan ƴan Nijeriya, inji Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin Gwamnatin Tarayya ta koka game da barazanar da ƴan ƙasashen waje ke yi akan Nijeriya da al’ummarta wanda ke neman hargitsa al’amura da durƙusar da haɗin kan al’umma a ƙasar.

Akan haka ne ta kirayi ƙwararru akan harkokin yaɗa labarai da su riƙa amfani da dabaru wajen daƙile zantukan ƙarya da ake yaɗawa akan ƙasar musamman kan batun kisan kiyashin Kiristocin ƙasar da wasu ƴan waje suka ƙirƙira.

Ministan Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris ya bayyana haka a Abuja yayin taron ‘World Public Relations Forum’ (WPRF Abuja 2026), da Cibiyar Hulɗa da Jama’a da ƙasa NIPR ta shirya.

A kwanakin baya ne wani ɗan majalisa a Amurka mai suna Sanata Ted Cruz ya gabatar da ƙudirin neman hukunta gwamnatin Nijeriya akan yadda take tallafa wa ta’addanci da ke harin shafe al’ummar Kiristoci a ƙasar.

Saidai, Gwamnatin Tarayyar ta ce Cruz da ire-irensa suna kan kuskure duba da yadda aikin ta’addanci ke shafar ɓangarori da dama a sassan ƙasar.

A wata takarda da mai taimaka wa Ministan Labaran akan yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, Mohammed Idris ya yi gargaɗin cewa ana hakan ne da nufin wargaza haɗin kan al’umma ta hanyar amfani da lamarin addini.

By Babaji