“Addinin Musulunci ya ɗaukaka mace, jahilci ne yake taƙaita ta”
Daga AISHA ASAS
Shafin Gimbiya bai tsaya a iya fira da mata kan sana’oinsu ba, ko samun bayanai kan ƙalubalen rayuwa ko nasarorin da suke samu ba, haka ma bai tsaya a iya darrusan wayar da kai ba, maimakon haka, ya yi nutso har zuwa ga tarihi, inda zai dinga kawo wa masu karatu labaran matan da suka kafa tarihi, ba don nishaɗi ko sani ba, sai don ya zama izna, ya koyar, sannan ya samarwa mata hanyar kamawa, wadda za ta zama makaranta a lokacin da suke fuskantar rayuwarsu.
Tabbas duniya ta ga mata da dama da suka cancanci a kira su da gimbiya, waɗanda suka bayar da gudunmawa mai tarin yawa ga cigaban al’umma, wanda idan har muna kallon irin rawar da suka taka, za mu iya cewa babu irin gwagwarmayar da mata ba za su iya shiga ba.
Kar na cika ku da surutu, a yau shafin Gimbiya na jarida mai farin jini, Blueprint Mnahaja zai yi bajikolin rayuwar macen da ta tabbar da matan Arewa na da gudunmuwar da za su iya bayarwa da har tarihi ba zai iya mantawa da su ba, kuma ita ce ta gaya wa duniya cewa, ba fa ta fuskar ilimin boko ne kawai mata za su iya shahara ba, kuma ba sai mace ta yi ihu da yekuwar ita ɗin ɗai take da namiji ba ne za a kira ta da jaruma ba.
Nana Asma’u binti Shehu Usman Daanfodiyo (tagamadahu llahu), malama, marubuciya kuma jagorar mata a Daular Sakkwato. Jagorar da ta haɗa addini da hikima a Arewa.
Na san da yawa masu karatu kan danganta shuhurar Nana Asma’u da mahaifinta, kasancewarsa babban jigo ga tarihin kafuwar Musulunci a Arewa, wanda kuma ya kasance babban abin alfahari a nahiyar Afirika ta fuskar kafuwar Islama.
Da wannan hujjar ce suke ganin ba ta bayar da wata gudunmuwar a zo a gani ba, saidai matsayi na babanta ya sa ta samu sunan da take da shi a duniya.
Mai wannan tunanin zan so ya amsa wasu ‘yan tambayoyi kamar hana;
Shin Nana Asma’u ita ce kaɗai ‘ya ga Mujadaddi Usmanu? To me ya sa ta yi fice a cikin ‘ya’yan nasa?
Idan kuwa har akwai wasu ‘ya’yan bayan ta, to tabbas za mu iya amincewa da ita ɗin ce ta samarwa kanta sunan da ta samu, ta hanyar kyakywan halayarta, gwagwarma, ilimi da kuma aiki da shi ta inda ya kamata.
Kada mu yi zurfi ga dogon bayani, har mu kuɓucewa manufar darasin namu, wato sanar da tarihi da kuma rawar da wannan sarauniyar ilimi ta taka don taimakon al’umma, musamman mata.
Dan haka zai fi kyau idan mun fara da sanin ko wacce ce Nana Asma’u bintu Shehu Usman bin Fodiyo (Allah ya yi rahma gare su).
An haifi Nana Asma’u a shekara ta 1793 a cikin Birnin ɗagele, daga cikin gida na malamai kuma masana addini. Mahaifinta kamar yadda muka faɗa, Shaik Shehu Usman ɗanfodiyo jagoran jihadi ne da ya kafa Daular Sakkwato, daular da ta shahara wurin addini, kyakyawar tsari da kuma adalci.
Mahaifiyarta kuwa, Aisha ta kasance mace mai ilimi, sanin ya kamata da kuma tarbiyya, hakan ya sa tun tana yarinya, Nana Asma’u ta samu tarbiyya mai kyau cike da ilimi, domin dai idan kana son ka san makomar yaro tun kafin a haife shi, to ka duba ɗabi’un mahaifiyarshi, domin dakyar barewa ta yi gudu, ɗanta ya kasa rerafe, duk da cewa akan samu wasu lokuta albasa ta kasa yin halin ruwa, amma dai yadda Larabawa suka ce, ‘al’ummu madarasattin bani nan ula’, ma’ana uwa ce makarantar farko ga ‘ya’yanta. Don haka ne halin Nana Asma’u ya samo asali tun daga tarbiyyar da ta samu daga mahaifiyarta, da kuma irin tasirin gidansu wanda ilimi da bin tsarin addini ya yada zango.
Kamar yadda tarihi ya sanar, Nana Asma’u ta kasance cikin yara mafi nutsuwa a lokacin ƙurciya, mai ƙwazo da son karatu, don haka take yawan sauraron karatukan da mahaifinta ke yi, kuma tana rubuta abinda ta sani. Wannan sha’awar tata ga ilimi ya sa ta zama mace ta farko a Daular Sakkwato da ta rubuta litattafai sama da 60. Ciki har da waƙe na wa’azi, tarihi da kuma faɗakarwa ga mata.
Kasancewar gidansu tamkar jami’a ta fuskar ilimi, inda ake koyar da maza da mata, Nana Asma’u ta kasance ɗaya daga cikin fitattun malamai na wannan gida. Ta koyar da mata masu tarin yawa, tun daga yara mata, zuwa matan malamai, har ma da matan sarakuna.
A wasu lokuta takan tafi ƙauyuka da kanta don koyar da mata ilimin addini da kuma yadda ya kamata su yi zamantakewa da koyar da tarbiyya. Bata tsaya a nan ba, ta yi wani shiri na musamman, inda ta haɗa mata masu ilimin addini da zamantakewa, don su zama abokanen wannan namijin aiki da take yi na haskaka al’umma, kamar yadda ta faɗa a cikin wasu rubuce-rubucen ta, “Ilimi yana haskaka zuciya kamar rana. Duk wanda ya rasa ilili, ya rasa haske.”
Wannan ya kasance babbar gudunmuwa da ya kamata a jinjinawa Nana Asma’u kanta, kasancewar ta sila ko kuma ginin da ya zama tushen samuwar malamai mata masu yin wa’azi a arewacin ƙasar nan.
Bayan kafa Daular Sakkwato, Nana Asma’u ta ci gaba da bayar da gagaruwar gudunmuwa a matsayinta ta mai bayar da shawara kuma malama ta farko a fadar Sakkwato, wanda aikinta ya haɗa da neman amsa kan al’amuran addini, sha’anin da ya jiɓinci mata, da tarbiyyar al’umma. Wannan ya zama wani girma da ƙasar Sakkwato ke ba ta har bayan ranta, inda ɗakinta da ke cikin Hubbaren Danfodiyo ya kasance abu mai muhimmanci da ake gadon zama cikin sa, wanda bayan muturwa Sarkin Musulmi ya buƙaci ‘yarta da ta baro gidanta ta zo ta zauna a ciki don ci gaba daga inda mahaifiyarta ta tsaya. Kuma kamar yadda wani masani kuma ɗaya daga cikin masu kula da Hubarren ya sanar da Manhaja, cewa, har yanzu ɗakin na Nana Asma’u na nan akan wannan turba.
Nana Asma’u ta kasance mai tsantsar adalci da natsuwa a lamurranta. A duk lokacin da rikici ko saɓani ya samu a tsakin mata daga matan malamai ko na sarakuna, ita ake nema don ta yi sulhu gare su, wanda kuwa take yi cikin hikima irin wadda Allah ya bata.
A wasu lokuta kuwa takan yi amfani da nasiha ta hanyar ayoyin Al’ƙur’ani mai tsarki, ko waƙoƙin hikima na lurarwa da ita ta rubuta.
A cikin wasu waƙoƙin ta, Nana Asma’u kan janyo hankali kan abinda take so ta wa’azantar cikin hikima. Kamar inda take cewa,”Ku ji tsoron Allah, ku koyi abinda zai amfanar da ku, domin ranar ƙarshe ba za a tambaye ku da zurfin ku ba, sai da ilimin ku.”
Jajirtaciyyar mace da rayuwarta ta kasance makaranta ga mata, Nana Asma’u ta yi fice wurin zantukan ilimi, wanda ko a firar ta kawai za a iya samun ababen ƙarfafawa, ko lurarwa ga mta da ma al’umma baki ɗaya.
Don haka muka ga buƙatar zayyano wasu daga ciki, wanda muke fatan su zama fitila ga mata masu zurfin tunani.
Nana Asma’u ta faɗa a wasu zantukanta cewa;
“Mace mai ilimi tana jagorantar al’umma da nutsuwa.” Ta kuma faɗa a wasu lokuta, “Ilimi shi ne kyautar da za ta kare ka daga zalunci, jahilci da tsoro.” Haka kuma ta faɗa a wani lokacin cewa, “Ku tsaya da gaskiya, domin gaskiya tana kare mai ita, koda kuwa kowa ya bar ki.”
Sannan kuma Nana Asma’u ta taɓa rayuwar mata ta hanyar neman na kai, inda ta koyar da mata cewa, ilimi da sana’a su ne ginshiƙin ‘yanci da mutumci. Ta yi kira ba sau ɗaya ba ga mace ta zama mai faɗin albarkacin baki, ba wai mai shiru da tsoro ba.
“Ku riƙe sana’a da halin kirki, saboda mace mai sana’a ba ta zama mai dogaro da wasu,” inji Nana Asma’u ɗiyar Mujjadadi.
Idan muka yi duba da nazari kan kalaman wannan baiwar Allah, za mu iya cewa ta kasance babbar jagora kuma fitila ga rayuwar mata, ba wai na zamanin ta ba, har ma na wannan zamani, waɗanda ke amfani da tsarabar da ta bar masu. Domin ba wata mace da za ta ce kalaman Nana Asma’u na matan baya ne, ba za su yi tasiri a gare ta ba.
Idan ma muka yi duba da idon basiria, za mu fahimci matan wannan zamanin ma fa sun fi buƙatar shawarwarin da ta bayar, tamkar ma don ta ajiye masu ta yi kalaman.
Idan za mu ci gaba da zayyano gudunmuwar malamar mata, Nana Asma’u, za mu ce ta yi gagarumin ƙoƙari a ɓangaren daidaito tsakanin addin da kuma al’ada, wanda masana tarihi suka tabbatar ke da matuƙar tasiri a zamanin nata. ɗaya daga misalan wannan akwai al’adar da ke ganin bai kamata mace ta fita ko ta koyar da jama’a ba, Nana Asma’u ta fahimtar da cewa, addini bai haramta hakan ba a matakin da suka ɗauke shi ba, kuma ta jadadda hakan ta hanyar koyar da matan waɗannan mutane da ke da wannan aƙidar, kuma sun ga amfanin ilimin a gidansu.
“Addinin Musulunci ya ɗaukaka mace, jahilci ne ke taƙaita ta,” inji Nana a ɗaya daga cikin kalamata na wayar da kai kan muhimancin mace, wanda a lokacin yake da ƙaranci.
Duk wata gwaƙwarmayar rayuwa za ka tarar da nasara da kuma akasin haka, idan mai karatu na karatun da fahimta zai iya fahimtar nasarorin da Nana Asma’u ta samu a wannan aikin alkhairi da ta yi wa raywar mata da kuma addinin Musulunci, don haka za mu waiwayi ƙalubalen da ta fuskanta, domin idan ka ji wane ba banza ba, ko ya ce bai sha dare ba, to tabbas ya sha rana.
ɗaya daga cikin ƙalubalen da Nana Asma’u ta fuskata, akwai fuskantar suka daga wasu a lokacin da take ƙoƙarin nuna haƙƙin mata, ganin da suke yi ta zo da wani abu da zai sa matansu da suke biyayya gare su fanɗare masu, matan da suke biye da umurninsu tamkar na bawa da ubangidansa, matan da ba su da iko ko haƙƙi na zaɓi akan abinda ya shafi rayuwarsu ko na ‘ya’yansu.
Duk da tsangwama da irin ababen da waɗannan mutane suka yi mata, Nana Asma’u ta zaɓi ta tsayu kan gaskiya, wanda ke nufin ba ra’ayinta ba ne, abinda ya kasance gaskiya ne. Kamar yadda ta faɗa cewa, “Na fi jin tsoron rashin gaskiya fiye da jin tsoron magana.”
Hakan na nuna jarumtar ta da ƙarfin zuciya irin tata wajen kare abin da ta gasgata.
A ɓangaren rubutu kuwa Nana Asma’u ta kafa tarihi na kasance mace ta farko da ta rubuta waƙoƙin addini da tarihi a harshen Hausa, Larabci da kuma Fulfulde. Kuma waƙoƙinta sun kasance ginshiƙi na ilimantar da mata da yara.
A cikin wata waƙarta ta ‘Wa’azi ga Mata’ ta yi nuni da cewa, “Ku tuna Allah a cikin ayyukanku, ku kasance masu nutsuwa da taimako. Mace mai kyakyawan hali ta fi zinariya daraja.”
Masana adabi sun bayyna ta a matsayin “Sarauniyar adabin Arewa” duba da yadda ta haɗa addini, ilimi da fasaha cikin rubuce-rubucen ta.
Nana Asma’u ta koma ga mahaliccinta a shekarar 1864, inda ba sai mun yi bayanin irin alhinin da aka yi a ranar ba, kasancer ta bar giɓi da har yau an kasa cike shi.
Idan muka yi duba da matsayinta a wannan zamani da muke ciki, za mu ce har yanzu Nana Asma’u na rayuwa a cikin al’umma, domin jami’oi da cibiyoyi da dama na duniya suna nazarin rayuwarta da litattafanta.
Idan mun soma da gida, a Jami’ar Usman ɗanfodiyo da ke Jihar Sakkwato, an ware sashen bincike na mata mai ɗauke da sunanta, ba don komai ba sai don tunawa da ita, a ƙasar Amurka da Ingila, ana koyar da darussa kan ‘African Women Scholars’, inda sunata yake fitowa a jerin matan farko da suka kafa tsarin koyar da mata a Afirka.
Wani masanin tarihi da ke Jami’ar Oɗford ya rubtuta cewa, “Nana Asma’u ta nuna cewa, addini da ilimi ba maƙiya ba ne; ta haɗa su don samar da cigaba.”
A taƙaice Nana Asma’u ta haɗa addini, hikima, da jagoranci a tafiyar rayuwarta. Ta nuna wa duniya musamman ƙasar Hausa da ba su cika ɗaukar mace da muhimanci ba cewa, mace ba wai kawai mashiin ɗin ƙyanƙyasar ‘ya’ya ba ce, ko kuma mai bautar gida ba, ginshiƙi ce ta al’umma. A cikin kalamanta na kusan ƙarshen ruyuwa, waɗanda jama’a ke yi wa kallon wasiya, Nana Asma’u ta ce, ” Ku tsaya da gaskiya, ku nemi ilimi, kuma ku kasance masu nutsuwa da adalci, domin wannan shi ne hasken duniya.”
Allah Ya kai haske kabarin Nana Asma’u, ka sada ta da manzon rahma.
