
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar jagororin kasuwanci da masana’antu ta Afirka, wato Africa CEO Club (ACC), ta ƙulla yarjejeniya a tsakanin masu ruwa da tsaki daga ɓangarori daban-daban da nufin ciyar da harkokinsu a Nahiyar Afirka.
Shugabar ACC, Fatoumatta Gaye ta sanar da haka a yayi taron manema labarai da aka gudanar a Afreximbank Africa Trade Center da ke Birnin Tarayya Abuja, ranar Litinin.
Ta ce, hakan abu ne da zai ƙara kusanto da jagorori masana’antu kusa duba da manufar ƙungiyar ta faɗaɗa hanyoyin zuba jari da inganta ƙananan ƴan kasuwa da kasuwancin Afirka ta yadda za su samu ci-gaba a jagoranci da gudanarwa.
Ta kuma yi tsokaci akan harkar ƙirƙira daga ɓangaren mata da matasa domin gogayya kasuwanci da masana’antu a mataki na duniya, lamarin da ka iya janyo ra’ayoyin masu zuba jari dag sassan duniya daban-daban.
Haka kuma, ƙungiyar ta ACC tana samar da damanmakin zuba jari t haɗaka tsakanin masu ruwa da tsaki na masana’antu masu zaman kansu da na gwamnati, inganta jagorori da ƴan kasuwa da ma fannoninsu a matakin shiyya da na duniya baki ɗaya.
Kazalika, ta ce fagen yana inganta sa’o’in mata da matasa ta shirye-shiryen, tattaunawa da haɗaka domin bunƙasa tattalin arziƙin Afirka a idon duniya.








