“Kungiyar Matanmu a Yau Organization na da manufofin taimakon mata da yara”
DAGA MUKHTAR YAKUBU
Masu karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja. A wannan makon shafin Gimbiya zai kawo wa masu karatu rahoto na wata ƙungiya da me rajin kare martabar mata ta hanyar koyar da su sana’o’i domin dogaro da kai. Da kuma tsaya masu a lokacin da suke buƙatar taimako. Hakazalika ƙungiyar ta waiwaye ɓangaren ƙananan yara da sha’anin da ya shafe su. Kamar yadda muka sha faɗa, shafin bai karkata a iya fira da mata kawai ba, maimakon haka ya kan leƙa kowane ɓangare da ya shafi rayuwar mace. Kama daga lafiyarta, sana’a ko aiki, muhimmancin neman ilimi ga rayuwar mace da makamantansu.
Wakilin Blueprint Manhaja a Kano, Mukhtar Yakubu, ya samu nasarar tattaunawa da shugabar ƙungiyar kuma fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Arewa, wato Kannywood, Hajiya Zulai Babeji.
Idan kun shirya, sai in ce a sha karatu lafiya.
MANHAJA: An yi kira ga mata da su tashi tsaye wajen magance matsalolin su ba tare da nuna gajiyawa ba, domin samu sauƙin rayuwarsu da ta iyalansu.
Shugabar ƙungiyar Matanmu A Yau Organization ce ta yi wannan kiran a lokacin taron masu ruwa da tsaki na ƙungiyar, wanda aka yi domin tsara yadda za su farfaɗo da ƙungiyar tare da ci gaba da ayyukan da ƙungiyar take tun tsawon shekarun da aka kafa ta kimanin shekaru shida kenan.
Taron wanda aka gudanar a gidan ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar Hajiya Hauwa ‘Yar Gwana da ke Unguwar Gaida a cikin garin Kano, ya samu halartar wasu daga cikin jagororin ƙungiyar kamar shugaba Hajiya Zulai Babeji, Bilkisu Maigado, Rukayya Sharaɗa da sauransu.
Tun da farko dai take bayani a kan manufar kiran taron. Shugabar kungiyar Hajiya Zulai Babeji, ta bayyana cewa,
HAJIYA ZULAI: Manufar kiran wannan taron shi ne don mu haɗu mu tattauna a game da tafiyar da ƙungiyar da kuma dawo da martabar ta.
Domin kuwa abu ne da kowa ya sani kusan shekaru shida da kafa wannan ƙungiyar, mun yi abubuwa da dama na tallafawa mutane da kuma taimakon junan mu. To amma a yanzu ne muke ganin mun ɗan yi sanyi, don haka ya kamata mu samo bakin zaren.”
Ta ci gaba da cewa, “Ita manufar wannan ƙungiyar ba wai ta tsaya ga wani ɓangare na mata ba ne, duk wata mace da take da buƙatar a haɗu a taimaki juna kuma a taimaki waɗanda suke buƙatar taimako, to muna maraba da ita. Don haka wannan tafiyar tamu ta hada da jaruman fim da mata ‘yan siyasa da masu gudanar da harkar kasuwanci da ma’aikatan gwamnati duk a tafiyar.
Ta ci gaba da cewa “Sanin kowa ne a baya mun yi abubuwa da dama na taimakon junan mu kamar lokacin bikin aure ko haihuwa ko rashin lafiya ko suna. Duk waɗannan abubuwan an yi wa mutane kuma sun ji daɗi.
To a yanzu ya za a yi mu ci gaba da wannan abubuwan alheri da ma wasu a nan gaba?
Dole ne sai mun samar da mafita da tsara yadda za mu tafiyar da abin don haka muka kira taron, muna fatan wannan zama namu zai samar mana da hanyoyin da ƙungiyarmu ta matan mu a yau Organization za ta samu ci gaban da za mu daɗe muna cin moriyar sa har zuwa ‘ya’yanmu da jikoki.”
Hajiya Zulai Bebeji ta kuma yi bitar manufofin ƙungiyar kamar haka;
Magance matsalolin da mata suke fuskanta na rayuwa.
Domin ciyar da mata gaba, don ganin sun tsaya da ƙafafunsu.
Shiga loko da saƙo, don ganin an tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi.
Koya wa mata sana’o’i domin kula da kansu da iyalansu. Wanda a lokaci zuwa lokaci mu kan koyar da mata sawa, ɗinkin jakankuna, takalma da manshafawa da na gyaran gashi.
Don haka wannan ƙungiyar ta himmatu wajen magance matsalolin mata da suka haɗa da
Rashin kulawa mata da suke da yara marayu. Safarar mata da bautar da su. Rashin bai wa mata ingantaccen ilimi. Yawan mutuwar aure. Shaye-shayen kayan maye da wasu matan suka tsinci kansu a ciki. Yawon barace-barace da wasu matan suke yi.
Duk da mata su ne ƙashin bayan al’umma, amma wani lokacin a kan mantawa da su, don haka ne muka samar da wannan ƙungiyar, domin mu taimaki kanmu da sauran mata da suke da buƙatar taimako domin su tsira da rayuwarsu.
A taron dai an tattauna muhimman abubuwa tare da bayar da shawarwari.
Haka nan an samar da hanyoyin da ƙungiyar za ta rinƙa samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan ta ba tare da ana cewa a kawo a harhaɗa daga wajen ‘yan ƙungiya ba.
Cikin hanyar da aka samar akwai yunƙuri na shirya fim a ƙarƙashin ƙungiyar wanda ƙungiyar za ta nemi haɗin gwiwa da wasu ƙungiyoyi ko kamfanoni don samar da kuɗin da za a yi fim din.
An dai yi taron an tashi lafiya, tare da nuna gamsuwa da abin da aka tattauna da mahalarta taron suka yi.
