
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Shura ta Jihar Kano ta gargaɗi sanannen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Lawan Abubakar da aka fi sani da Triumph da ya kiyaye furucinsa a yayin da yake gabatar da karatukansa.
Hakan ya biyo bayan zargin sa da yin kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) a kwanakin baya a lokacin da yake gabatar wa ɗalibai karatu a Kano.
Sakataren Kwamitin, Shehu Wada Sagagi ya bayyana cewa da fari kwamitin ya karɓi ƙorafe-ƙorafe guda tara akan malamin kana daga bisani aka mayar da su huɗu bayan yin nazari akansu.
A cewar kwamitin shurar, ƙorafe-ƙorafen sun ta’allaƙa ne akan furucin malamin game da ingancin bayanan da ake ruwaitowa akan haihuwar ma’aiki da shayi (kaciya), waɗanda wasu suke ganin ɓatanci ne.
A yayin zama na tsawo sa’o’i a gaban kwamitin ƙarƙashin jagorancin jami’an hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), shehin malamin ya kare kansa, inda ya tirje akan cewa an yi wa kalaman nasa gurguwar fahimta, sannan an koma tattauna ta a wani fage na daban.
Ya kawo nassosin musulunci da madogara na tarihi domin bayyana haƙiƙanin abinda yake nufi, yana mai ikirarin ba ya nufin nuna rashin girmamawa ga Manzon Allah.
Bayan sauraron jawabinsa ne sai kwamitin ya gargaɗe shi da ya iya bakinsa a yayin gabatar da wa’azi nan gaba musamman kan al’amuran da suka shafi Ma’aiki kai-tsaye.
Kazalika, Majalisar ta kuma jaddada matakinta na dakatar da malamin daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za ta kammala haɗa rahotonta akan lamarin da miƙa wa gwamna Abba Kabi Yusuf na Jihar Kano.
